Page 31
" Ana kiran sallar asuba A'ishah ta, ta shi duk jikin ta ciwo yake mata, jiya ba ƙaramin gajiya tayi ba, ga kuma yau ko ya yau ɗin zata kasance Allah ne masani.
" Miƙa tayi haɗe da salati, kana ta miƙe tana murza idanun ta, sai da ta gama was tsake wa daga magani bacci da ke idon ta,
Sannan ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita, eban ruwa tayi ta shiga ban ɗaki, ta kama ruwa ta fito ta ci karo da ya mardiya,
Matsa mata tayi itama ta shiga, kafin ta samu guri ta tsugunna ta fara alwala, bayan ta gama ta koma ɗaki ta shin fiɗa dadduma ta tada salla.
Bayan ta giɗar ta ɗaura da azikar tare da yin addu'a akan abin da zata aika ta ayau , duk da cewa zaɓin tane amma sai dai bata san ko tayi laifi ba gurin yin hakan..
Har cikin zuciyar ta tana ji hakan shine dai-dai hakan shi ne zai tse ra tar da ita daga auren Nuhu,
Ya kuma bata damar mallakar zaɓin ran ta muradin zuciyar ta hasken idani yar
Ta ƙara da cewa ina rokon ka ya Allah kaine mafi sanin dai-dai Allah ka sa hakan da na zaɓa wa kai na shine dai-dai a gare Ni da rayuwa ta.
Addu'a A'ishah ta cigaba da yi har gari ya waye rana ta fito , ƙana ta tashi ta fara share gidan, sai da ta share ko ina da ya kamata, ƙana ta ɗaura ɗumamen tuwo,
Dama yau ta kama ranar asabar ba makaranta su Amina har sun tashi, wanka ta musu, suka shirya, sannan kowa ya ƙarya.
Wanka A'ishah tayi cikin sauri tana shirya wa, Amina da jabir da ya mardiya duk suna cikin ɗakin
Amina dake wasa tare da jabir taga Aishah na shiri tace anty A'ishah ina zaki je zan biki, A'ishah tayi saurin cewa ba inda zaki je makaranta zani muna shirin tafiya teaching practice da mun koma zamu tafi.
Amina tace wallahi zan natsu bazan dame kiba, yaya mardiya ta ce ke tun da tace baza ta je da keba ki haƙora mana.
Oh dama in ta fita dake magana kike sata ko to ba in da zaki sake bin ta daga yanzu,
A'ishah tana jin su bata ce komai ba ta gama shirya wa, ta saka wata light bulu atamfa ɗin kin doguwar riga ya zauna mata a jiki, ta ɗau ko wani dark bulu hijab tasa yau ma face mask tasa da Glass,
Kallon ta yaya mardiya tayi, ta ɗan yi murmushi tana cewa a'a yanzu fa ƙan War tawa ta ƙara waye wa fa an dena sa nikab,
Murmushi Aishah tayi tace yaya mardiya kenan wai na waye wato da Ni baƙauyi yace ko, yaya mardiya tace a'a Ni ban ce ba nina isa,
Ɗaukar jakar ta tayi A'ishah ta ƙara da cewa sai na dawo yaya mardiya ta mata a dawo lafiya Sannan ta fita,
Tana sa ƙafa ta fita a gidan, abinda zata je ta aika ta ya faɗo mata a cikin zuciyar ta,
Nan da nan gaban ta ya fara fa ɗuwa, sai innalillahi take ambata cikin zuci,
Haka dai take ta fama da nauyin zuciya har ta ƙara sa, koda ta ƙarasa ƙofar gidan su lion bugun zuciyar ta ya hau hawa ji take kamar zuciyar ta zata fasa ƙirjin ta ta fito,
Ja idon ta yayi taji wani zazzaɓi na shirin kama ta, juya wa tayi ya zamana ta bawa gidan baya, ita bata tafi ba ita bata shiga ba,
Tana nan a tsaye taji an kira sunan ta daga bayan ta, farhan ne shima zuwan shi kenan gidan sai yaga A'ishah a tsaye a ƙofar gidan shine ya kira sunan ta,
Bai lura da yanayin da take ciki ba saboda face mask glass ɗin da ya rufe mata fuska yace amarya mu ke ce a tsaye a nan haka,
A'ishah ta gane ko waye daya daga cikin abokan lion ne ɗan ƙaƙalo murmushi tayi wanda ake kira da yaƙe kafi kuka ciwo sannan tace.

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...