Page 73
Ku na ganin lefi na naƙi muku update bayan kuma, na fada bazan yi updating next chapter sai na samu 30 like da comments to wannan ma haka .
"Lion yace jiki yana nan, A'ishah bata tan ka shi ba balan tana tace uffan dan ta gane magana yake so ta mai kuma baza tayi ba, ayana ce tace ammi kema zo ki zauna kusa da abban mu,
Dan guntun murmushi wanda bai kai ciki ba A'isha tawa ayana, sannan tace a'a mamana yan zu ma za mu wuce gida ba sai na zauna ba,
Ana cikin haka sai ga shigo war Ahmed shi kadai, lion ɗaya mai giri yayi sannan yace ya dai malam nace ma ina da buƙatar ganin fuskar kane kuma,
Ahmed yace to wa ya gaya ma ina so ni in ga taka, what ever nazo na ɗebi yara nane na kai su susha ice cream ayan lashe bakin shi yayi, yace ice cream party yeee, miƙa hannun shi yayi Ahmed ya ɗauke shi,
Ita ma ayana ta sauko , ya riƙe mata hannu, Ahmed ya kalli A'ishah yace my inlaw in ba damuwa ki zauna tare da mutumin nan kafin muje mu dawo,
Yana gama cewa haka bai jira abin da A'ishah zata ce ba yana hannun ayana suka fita a cikin ɗakin,
A'ishah ta buɗe baki zata yi magana kenan amma har sun riga da sun fita, dafe goshin ta tayi ta koma ta jin gina da jikin ban go , gaba ɗaya duk haushi ya cika ta,
Message ya shigo cikin wayar lion da Ahmed ya kawo mai, wayar tana gefen shi yasa hannu ya dauko ta,
Yana buɗe wa number Ahmed ne ya gani ya tura mai da saƙo kamar haka,
"kayi amfani da damar nan ka janyo hankalin suruka sai da safe".😎
Murmushi lion yayi ya ake wayar a gefen, ya ja dogon nunfashi shi ya sauke, ya rasa ta inda zai fara don ya daidaita abun da ke tsakanin su, ina ka duba irin girman lefin da ya aika ta a gare ta,
Gyaran murya yayi, A'ishah ta juyo ta kalle shi, yace ga kujera ki zauna baki gaji da tsayuwa bane,
A'ishah ta ce a'a nan ma yayi, sai lion ya Yun ƙura zai ta shi, da sauri A'ishah ta ƙarasa ta rike shi tana cewa" me kake so ba ance kada ka tashi ba,
Lion cewa yayi ruwa nake son sha , A'ishah ta temaka mai ya zauna jin gine a jikin gadon, sannan ta dauko ruwan ta bashi ya sha ,
Ta sake temaka mai ya koma ya kwanta, garin haka idanuwan su , suka hade da na juya na, suka fara kallon juna ba tare da ɗayan su ya ankare da hakan ba , kallon juna soke mai wiyar fassara wa,
Ana cikin haka aka banko ƙofar ɗakin aka shigo, da sauri A'ishah ta farka ta saki lion ta miƙe, dama kusan rabin jikin ta na saman lion,
Ruky ce ta shigo ciki , da sauri ta ƙaraso gurin lion har tana ɗan tura A'ishah, faɗawa jikin lion tayi ta rungume shi, tana cewa am so happy love you've finally be found, ( ina matukar farin ciki daga ƙarshe dai an ganka masoyi ,)
Shafa fuskar shi tayi takai labɓan ta zata sumba ce shi , da sauri lion ya ture ta faɗi ƙasa, a zafafe tace what the hell you crazy woman what are you trying to do, ( mahaukaci yar mata mai kike shirin aika rawa)
Ruky cewa tayi cikin shagwaɓa da batai mata kyauba, lion love , shin meye lefi na kuma anan,
Lion cewa yayi lefin ki ke son sani ko kiyi maza kumar nan ko in da a zo a fita mun da ke, ruky cewa tayi but ,lion cewa yayi i said get out,
Tashi tayi ta aika wa da A'ishah wata muguwar harara , sannan ta fita ran ta a ɓace,
Tun shigo War ruky cikin ɗakin wani abu ne mai ciwon ya tukare a ƙirjin A'ishah ji tayi kamar ta mutu ganin yadda ruky ta rungume lion ya barta,
da lion Bai ɗau mataki da wuri ba sa , da kan ta tayi niya tura ruky waje, A'ishah wani kallo mai cike da haushi da baƙin ciki ta aika wa lion sannan ta fita daga cikin ɗakin ran ta na mata ƙuna,
Lion buga hannun yayi ajikin gadon da yake kwance cike da baƙin abin da ruky tazo ta aika ta yanzu nan , gashin tun kafin komai ya dai-dai ta rusa komai, ƙarshe ma sai fushi da A'ishah ta sake yi da shi,
Yasan A'ishah ko ta fita ba wanda zata gani bare ya Kaita gida dan kowa ya wuce, da sauri ya ɗauki wayar shi yayi kira ya bada umurnin kada abar A'ishah ta fita daga cikin asibitin,
A'ishah zuciyar na ta farfasa ta fita daga cikin ɗakin, ko zata ga su nafisa su koma gida, amma har ta ƙara sa baƙin get ɗin fita bata hada ɗin da kowa ba, gashi ba waya a hannun ta bare ta kira su,
Sai ta yanke shawarar kawai bari ta fita ƙilan ta suna waje, sai dai da tazo fita masu gadin suka hana ta fita , tayi tayi amma sunƙi barin ta har sai da ta gaji ta haƙora,
Ta fara bulayi cikin asibitin, har dai ta kawo cikin ƙayataccen gadin ɗin dake cikin asibitin, ta nemi gurin ta zauna, tana saƙe saƙe cikin zuciyar ta, duk abin da ke kawo mata a cikin ran ta shine ,
wato ma lion har ya man ce da abin da ya aika mata, ya dena son da yake ta ambaton yana mata, ya fara son wata ƴa mace,
So yake shi yayi aure Ita ya barta, tun da ita duk wanda yaji labarin ta ba mai cewa zai aure ta, shigo ko dan kuɗin shi mata zasu so shi,
Dafe zuciyar ta yi tace tabɗi lallai ko akwai ƴakin mata , yana tunanin zai aika ta mata duk abubuwan nan ne kuma tazuba mai ido , to bazai taɓa yiwuwa ba,
Bai isa ya shigo da wata mace cikin rayuwar shi ba ta bari, wani ƙuduri ta ɗauka wa ranta sannan ta yi murmushi muguta ta miƙe,
Ganin mangariba tayi duhu ya fara yi, ta koma cikin asibitin cike da saƙe abubuwa masu tarin yawa a ran ta.
Tana shiga cikin ɗakin ta iske likita yana duba jikin lion , taja ta tsaya har ya gama ya fita,
Lion yi yayi kamar ba abin da ya faru, yace temaka min zan yi alaula, danne duk abin da take ji tayi , ta temake shi yayi alaula, sannan ita ma take tayi nata sallar,
Ta tambayi lion yaushe su Ahmed zai dawo da su ayan tana so ta koma gida, lion cewa yayi Ahmed ya kira shi ya gaya mai ya wuce dasu gida sun gaji,
A ƙufule A'ishah ta ce to Ni waya zai mai dani gida, lion ganin yadda A'ishah ta yi sa fuskanta ya danne dariyar da tazo mai, yace may be sai gobe,
Balbale shi da masifa tayi tana cewa a kan me zai ce sai gobe ina zata kwana kenan, sai da ta gama faɗan ta sannan ya ce kin gama, A'ishah cewa tayi oh mahaukaciya ma ka ɗauke ni, nA gama ma kake cewa,
Dafe kan shi lion yayi , sannan ya janyo ta faɗa jikin shi, ya goga fuskar shi jikin Tata, sannan yace a hankali yadda ko da akwai wani a cikin ɗakin bazai jiba yace , relax matar , fushin me kike haka kamar da dodo aka barki ba tare da mijin kiba,
A'ishah sauke nunfashi kawai take ɗaya bayan ɗaya, ji take kamar wata duniyar take inda ta man ce da komai da dukkan Ni damu woyin ta daga ita sai lion,
Kama fuskar ta yayi ya shafa laɓɓan ta da yatsan hannun shi guda ɗaya sannan ya furta the most beautiful,
Ya sake cewa yanzu dai ɗaga Ni in Mana order abin da zamu ci yaja hancin ta yace duk kin saka Ni cikin wani yanayi , gaji ba iya kula da ɗan mutumin zaki ba
Da sauri A'ishah ta tashi daga jikin shi duk kunya ta cika ta , amma lion har yau bashi da kunya ji irin maganar da yake gaya mata, neman guri tayi ta zauna dan taga alama ba halin tafiya gida,
Lion da kyar ya tashi duk ya haɗa gumi dan ɗan kusan cin da suka samu a yanzu har ya saka shi cikin wani hali, ji yake kamar ya janyo ta ya mai da ita jikin shi , amma ya daure ,
ya ɗauki wayar shi ya sa a kawo musu abin da zasu ci , ya mai da kan shi yana sauke zazzafan nun fashi tare da satar kallon A'ishah ta gefen ido,
Ba daɗe wa aka kwankwasa kofar A'ishah ta je ta duba abin cin aka kawo ta amsa ta dawo, ta zuba wa lion ta bashi itama ta zuba kanta, suka gama ci,
... ......
Shin me kuke tunanin Aisha na shirin aika tawa
See yaah
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...
