part 7

274 18 7
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 31-35

Har su nafisah suka gama lecture ta fito, kafin suka ɗauki hanyar fita a makarantar.

Ba wai A'ishah ta manta bane, da lion yace ta kira shi in ta gama lecture.

Kawai dai tana so ta ɗan ja baya da shi ne, ganin cikin kwanaki ƙalilan har ta sha ƙo da shi da yawa, bata san mai zai faru ba , in da sun dade da sanin juna.

Suna fitowa bakin get suka ga lion a tsaye a kusa da motar shi yana wasa da key ɗin motar shi.

Dum gaban A'ishah ya bada ta ja ta tsaya, tana lulawa duniyar tunani,.

Katse mata tunanin nafisah tayi ta ja hannun ta suka ƙara sa inda lion yake tsaye,

Cikin iya yi nafisah ta gaishe shi, ya amsa kawai da lafiya,

Ka fin ya bude motar, daƙyar A'ishah ta motsa jikin ta shiga gaba ta zauna , nafisah kuma baya.

Za gaya wa shima lion yayi ya zauna a driver seat , ya tada motar, suka ɗauki hanya ,.

Tun bayan fara tafiyar su ba mai cewa da ɗan uwansa wani abu, daƙyar A'ishah dai ta iya buɗe baki ta gaya wa lion inda zai aje nafisah,

Shima karkaɗa kanshi kawai yayi, ba tare da ya ce komai ba suka ci-gaba da tafiya, ita dai nafisah acikin zuciyar mamakin wannan al'amarin take,.

In ka kalle su baza kace ba masoya bane, amma sun kasa barin wata alama da mutum zai yadda da su masoyan ne.

Wannan al'amarin akwai sarƙaƙiya a ciki, kai dole ne ma ta nemi ƙarin baya ni , ko ba yanzu ba.

Har suka kawo chikaji a inda nafisah zata sauka, kowa da irin abin da yake tunani a cikin zuciyar shi , da sauri nafisah ta fita a motar ganin mangariba data sawo kai,.

Tayi wa lion godiya, tare da cewa A'ishah sai sun haɗu gobe in Allah ya kai mu .

Suna fita daga cikin unguwar sun hau ti-ti , lion ya juyo ya balla wa A'ishah harara, yace, yanzu da ban zo ba kenan baza ki kira ni ba, haka zaki biyo daren nan ki taho.

Sai wani abu ya faru yanzu ku fara cewa kaddara ce, ita dai A'ishah rasa bakin magane tayi sai ce mai kawai tayi yi haƙori,.

Tana saukar da kanta ƙasa cike da mamakin lion ɗin, sai kace ba da kanta take zuwa makaranta ta dawo ba.

Shi ko lion taɓe bakin shi yayi yace sorry for your self ƴan Mata ,

Suna kawo wa unguwar su lion ya nemi guri yayi packing ɗan nesa da gida jen, kafin ya juyo da kallon shi kan A'ishah wacce kanta ke a sun ƙoye , tana wasa da yatsun ta kamar ko da yaushe.

Kallon tsaf ya gama ƙare mata yana ƙara tari yo irin halitta jikin ta, ji yake kamar ya jawo ta ya bata, wata kyakkyawar runguma tare da aika wa wannan lallausan bakin nata sun ba,

Ya san ko hakan ma zai Wada ce shi, ka War da tunanin shi yayi yace, ya ne ƴan mata, ko ba ki gaji da zama da wannan kyakkyawan saurayin bane,

Hararar shi A'ishah tayi kamar idanun ta zai fito kafin ta figi jakar ta, ta fita a cikin motar,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now