Page 66.
•Ignore the typing error..
*Happy reading*
" Tun da suka ɗauƙi hanya , gaban ta ke faman faɗuwa, gaba ɗaya tunanin ta ya ta allaƙa ne ga irin karbar da zata tarar in Allah yasa suka isa Zariya, bata san da wani ido zata kalli malam, sannan azo kan mama ,
zuwa ga ƴan uwan ta, da tsakani da Allah tana matuƙar jin kun yar haɗu wa da su, don abin da ta aika ta musu a baya ba abin da za a taɓa man ce wa bane,
Tun daren ranar zuwan lion , ya Ari waya ya Kira daddy suka yi magana, washegarin ranar ƴau kenan da safiyar ranar,
Daddy ya turo musu da man yan motoci guda biyu, suka rufe gidan gaba ɗaya, mota ɗaya suka shiga, A'ishah lion AHYAN da AYANA, ɗayar motar kuma, me ƙo sai ce ta shiga ɗayar motar , suka ɗauki hanyar Zariya,
AHYAN ne dake zaune kusa A'ishah ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, yana miƙa mata chocolate din dake hannun shi wai ta buɗe mai ,
Amsa tayi ta buɗe mai, ba daɗe wa cikin awa biyu da rabi suka shiga cikin garin Zaria,na take hankalin A'ishah ya ƙara tashi gumi ya fara tsatsubo mata duk da Ac dake kunne a cikin motar,
LION ne ya an kare da halin da ta shiga tun tawowar su, saka hannun shi yayi cikin nata, yana matsa wa alamun ta kwantar da hankalin ta,
Cikin harabar gidan motocin suka yi parking,lion ya buɗe mota ya fito AHYAN da AYANA suma suka fito, ya buɗe wa me ƙosai ita ma ta fito,
A'ishah ta ce su shiga zata shigo daga baya, lion bai matsa mata ba dan ya fahimci abinda take ji a halin yanzu,
Kama hannun AHYAN da AYANA yayi yama me ƙo sai jagora suka shiga cikin gidan, daga malam , mama da su Aunty sa'a dukan su tare suke suna zaune a falon gidan ,
suna tsammanin zuwan su, dan tun jiya da daddare daddy ya sanar da malam zuwan na su , shi ma yace in an yi kwana biyu zai shigo,
Suna shiga cikin falon yara yaran ƙana na da murna suka taso suka rungume lion , cikin faɗa AYANA ta fara ture su abin dariya wai kar a taɓa mata yaron ta, shigo AHYAN kun yar ganin mutane da yawa yasa ya ɓoye bayan lion,
Gaba ɗaya manyan tashi sukai fuskar kowa ɗauke da farin ciki, dan kowa ya fahimci wa'in nan yaran sune yaran A'ishah,
Yaya naja ce ta jan yo AHYAN da ke ɓoye ta ɗau ke , shi tana mai wasa, ita dai AYANA kicin-kicin tayi da fuska ta haɗe girar sama da ta ƙasa tana balla wa yaran da suke manne wa lion harara,
Nafisah ce ta ɗauke ta , tana cewa zo nan yarinya ta fushin me kike ke da ya kamata kiyi farin ciki,
Mama ce ta lura da me ƙo sai, ta mata Barka da zuwa ta mata , sannan ta bata gurin zama , Aunty Sa'a ce tambayi LION, A'ishah fa, kowa shiru yayi dan yaji mai lion zai ce shiru yayi bai ce komai , sai kallon ƙofar shigo wa da yayi,
Malam fahimtar, abin da lion ke nufi yasa ya fita waje ba tare da yace komai ba, motar da ya gani fake harabar gidan ya je ya buɗe , take ko suka haɗa da A'ishah da ta wai go ,
Sau kar da kan ta tayi kasa take hawaye ya cika idon ta, malam be ce komai ba , ya kamo hannun ta, ta fito daga cikin motar, suka shiga cikin gidan ,
Kan ta a ƙasa ta kasa daga ido ta kalli kowa , sai hawaye da ke uban ambaliya a cikin idon ta zuwa saman kuma tun ta , kowa bin ta da kallo yayi, malam riƙe da hannun ta ya shiga da ita cikin ɗakin shi,
Sannan ya saki hannun ta ya nema guri ya zauna, A'ishah a tsaye ta tsaya , tana share hawayen ta,
Malam ne ya buɗi bakin shi ya fara magana kamar haka, ashe akwai ranar da zata zo da ƴa zata ɗin ga guje wa haɗuwa da mahaifin ta, in wani lefi na miki kike hukun ta Ni mama na ki yafe min wannan irin hukuncin yayi mun tsauri, bazan iya jure wa hukuncin da zai Ni san tani da ke ba,
Kuka ne ya kuf ce wa A'ishah ta na girgiza kai , zube wa tayi a ƙasa tana sake sakin wani sabon kukan mai taɓa zuciyar masoyi , mai imani da tau sayi,
Sannan ta Fara magana cikin kuka, tana cewa na tuba kayi haƙuri , ka yafe Ni Abba na, nasan lefin da na aika ta zai yi wuyar a yafe min , amma san kai irin nawa bazai hana in roƙe ka a kan ka nemi gurbi cikin zuciyar ka gurin ganin ka yafe min ba,
Na aika kuskure kuma nayi nadama , tashi malam yayi , ya ɗago ta yana cewa , tashi abin ki mamana ,
Ni ban ta ɓa riƙe ki dan kin aika ta min wani lefi ba a cikin zuciya ta ba, baki mun wani lefi ba , in ma kin mun to tabbas na riga da na yafe miki,
Maza ki share hawayen ki sannan ki man ce da duk abin da ya faru a baya ki fuskan ci gaba,
amma sai kin min alƙawarin ko mai zai faru baza ki taɓa nesan ta kan ki daga gare niba,
A'ishah cewa tayi na gode na gode, na riga da nayi nadama, amma bazan taɓa barin nan gaba na sake yin wata nada mar ba,
Ana cikin haka, mama tayi sallahma ta shigo cikin ɗakin, A'ishah tsayuwa tayi suna kallon juna ita da mama,
mama tace shin ni ban cancanci a rungume Ni ba kenan, da sauri A'ishah taje ta rungume mama suna kuka tare, tana neman yafiyar ta,
Haka ta kasance tsakanin ta da yan uwan ta suka rungume juna suna neman yafiyar juna, kafin komai ya lafa,
baba ya haɗa su duka ya ɗaura musu da nasiha akan su kasance a ko da yaushe masu sa gaskiya da tsaron Allah a cikin lamarin su ,
Tare da guje wa duk wani abu da Allah ya hana , yin ladabi da biyayya ga iyaye yana shi zai taka babban jigo cikin ko wanne daga cikin su,ya shi musu albarka tare yi musu addu'ar Allah ya fito musu da mazaje na gari,
Sannan yayi wa me ƙo sai godiya da kula da ɗawainiya da A'ishah ta yi na shekarun nan har izuwa yau,
Me ko sai ta ce ba ko mai ai ɗa na kowa ne, addu'a yayi su AYANA tare da sauran jikokin shi daga nan nafisah ta gabatar musu da abin ci aka ci aka sha, ƴar karamar walima aka yi ranar cikin gidan ta dawowar A'ishah cikin ƙoshin lafiya...
°°°°°°°°°°°
Ina wa kowa Barka da salla , tare da murnar sanar da ku zan cigaba da littafin nan daga yau insha Allah tare da izinin Allah da kuma addu'ar ku,
Kada kuma ku man ta a ɗin ga comments da vote na gode..

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romansa* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...