Not editing
AYANA na fita a ɗakin ba daɗe wa , A'ishah da AHYAN suka dawo daga asibiti, oyoyo AYANA tawa Aisha,Sannan A'ishah ta bar su suna wasa tazo ta ɗaura musu girki dan rana tayi , yan zu zasu fara damun ta suna jin yun wa,
A'ishah ta kusa gama dafa abinci, AYANA ta taho da tsalle tsallen ta, A'ishah ta na ce mata kul gaban wuta ne fa,
AYANA ta ce aunty A'ishah, A'ishah ta ce na am, AYANA ta ce abin ci kike dafa wa A'ishah ta ce a'a ruwa na ke dafa wa,
Me ƙo sai cewa tayi yau wa gwara da kika bata amsa dai dai da tambayar ta, yariya sai shegen feleƙe, da man yan ce,
AYANA ɓata fuska tayi tana turo dan ƙaramin bakin ta, A'ishah ta ce in abin cin nake da fawa , me ya faru,
AYANA cikin shagwaɓa ta ce ni ki zuba min nawa da ban bana so in ci tare da AHYAN, A'ishah ta ce akan me baza kici tare da AHYAN ɗin ba,
Yana majina shi kajami ne, A'ishah riƙe haɓa tayi ta ce oh Ni ƴa su, yanzu dai ke kaɗai kike so kici AYANA ta ce eh, A'ishah ta ce to naji jeki zan zuba miki
Tun da Ni haifi abina naci tare da shi, tana gama wa kuwa , ta zuba mata , AYANA ta ɗauka ka plate ɗin abin ci ki, ki zata shiga ɗakin ajiya,
A'ishah ta ce sai kuma ina , AYANA ta ce ciki mana , A'ishah ta ce to a ci abinci lafiya, me ƙo sai ta ce aiki ga mai shi
Shiga cikin dakin tayi ta iske lion zaune ya tashi ciwon kan da yake ji ya dena ji , aje mai abin cin ta tayi a gaban shi tana cewa yau wa ɗan nan ka tashi
Ga abin ci nan , maza ka cin ye ina gani , ganin bai fara ci ba ta ce ci mana ko so kake in baka a baki , to bari in baka yaron mommy , lion kutt yace cikin zuciyar shi
AYANA ta ɗebo abin cin ta tura mai a baki dan dole ya haɗiye, sai Abin cin ma ya mai daɗy,
cigaba da ba shi tayi, hakan sai ya tono mai da mahaifiyar shi lokacin da yana ƙarami , sai yanzu ya gano da wa AYANA ta ke kama , da mommy shi take mai kama dan idanun su iri ɗaya ne hazal eyes ,
Shi fara ɗeban abin cin yayi yana bata tana ci har suka gama,
AHYAN ne ke tambayar A'ishah, momy ina super man ɗina A'ishah ta ce Ni kam ina zan San in da kuke jefa kayan wasan ku ,
AHYAN cewa yayi yau kwa bari in tambayi AYANA, da gudu ya shiga cikin ɗakin ajiya ya buɗe baki zai tambayi AYANA super man ɗin shi da ta ɗau ka, ba kawai sai yaga lion ba,
Ihu yayi ya kira sunan Abba , A'ishah daga wajen jin abin da AHYAN ya ke cewa yasa ta ce, wani abban kuma ,
AHYAN zai yi magana, AYANA ganin zai tuna mata asiri yasa ta ɗau ki lomar abin ci ta tura mai a baki , tana zazzare ido,
AHYAN bai saurare ta ba yaje ya faɗa jikin lion Yana rungume shi, shima rungume lion yayi, yana mai aika mai da kiss
A'ishah ganin AHYAN bai amsa ta ba yasa ta tashi sun ta duba taga ko lafiya, sai dai tana shiga cikin ɗakin taga lion rungume da AHYAN dafe ƙirjin ta tayi,
AHYAN yace mommy kin ga abba yazo , yaci mu game ɗin , amma am so sad yanzu we lost bazan samu chocolate da yawa ba,
Lion yaja kuma tun AHYAN yace No my boy duk da haka Nama alƙawarin siyo ma chocolate da yawa,
AHYAN yace yeee thank you abba I love you, AYANA ta ce ba wani abban ka bane yaro , ɗana ai Ni na samo shi
AHYAN ya ce dalla ma can Abba nane ko mommy, AYANA ta ce zan mare ka mommy ki gaya mai zan mare shi, A'ishah shiru tayi ta fita sukuku,
AHYAN ya taso ya tsaya gaban AYANA a dole zasu yi faɗa, shi lion ma abin dariya ya bashi,
Ta sowa yayi ya riƙa su, sannan ya ce dukkan ku kuyi shiru, my AHYAN Ni ne abban ka , AYANA you're my ammi , ni kuma am your daddy,
AHYAN da AYANA cewa suka yi daddy a tare sannan suka ce mu dai bamu da baba ,
Lion sai yaji ba daɗi na rashin kasan cewa da bai yi a cikin rayuwar yaran ba tun da aka hai fe su,
Dan murmushi yayi sannan ya ce , nine nan abban ku nayi wata ƴar tafiya ne sai yanzu na dawo kuma na muku alqawarin bazan ƙara yin nesa da ku ba saboda haka kada ku sake cewa baku da baba kun ji ,
Suka haɗa baki suka ce Yes , lion yace yes who , suka ce Yes Abba, rungume su yayi dukkan su , tara da san ya musu albarka , wani farin ciki ne ya sake mamaye zuciyar shi gana cewa ba ɗa bane kawai gare shi har da ƴa , a brilliant girl like this , one in a century,
Such a coincidence that happened, yarinyar cikin ta temake shi ta kawo shi gidan da yake nema
Tashi yayi yace oya muje muga mommy ku , fita sukai daga cikin ɗakin AHYAN da AYANA rike da hannun shi suna tsalle tsalle,
Me ƙo sai suka tarar tsakar gida, cikin mamaki ta tashi tana cewa, a'a to , ganin babban mutum da ke matukar kama da AHYAN a cikin gidan nasu ,
Cewa tayi yaro lafiya haka, gai she ta yayi sannan yace Ni baban sune,
Me ƙo sai tace to masha Allah gama kama nan, tambayar ta yayi ina A'ishah, me ƙo sai ta ƙwala kiran sunan ta Amma bata amsa ba bare ta fito,
Sau ke nunfashi lion yayi ya ce , ba komai baba kyale ta bari in shiga in same ta , shiga cikin ɗakin yayi,
Ya samu A'ishah zaune a ƙasa kan ta kife saman katifa wan da alamu ya nuna kuka take,
Sai da ya tsaya yana kallon ta na kusan minti ɗaya kafin ya zauna kusa da ita, ya fara magana kamar haka,
Nasan ko wace irin tuba zan sanar dake nayi kan abin da na aika ta a gare ki baza ki yadda dani ba, dan ko Ni kai na nasan abin da yi miki ban aika dai dai ba,
Sai dai a wannan lokacin ina so ki tsaya ki saurare Ni , ba magana zan yi akan kai na ba , bazan takura miki ki yafe min ba ko ki kuma amsa ta karo na biyu har sai lokacin da kika shirya wa haka,
Bayan duk abin da na aika ta miki , hakan ba rayuwar ki ka ɗai ya shafa ba , har da ta iyayen ki da ƴan uwan ki,
A ganin ki yin nisa da su shine zai sama musu salama cikin rayuwar su , sai dai a'a bayan halin da kun ci da tsan gwama da suke ciki,
Sun kasance tun bayan tafiyar ki suke jiran ganin dawowar ki , a kullum gani suke zaki sallama da sunan kin dawo,
Kiyi haƙori ba dan niba ko dan yaran mu susan ɗan gin su , ki koma gare su , suna da buƙatar ki,
Sake fashe wa da kuka A'ishah tayi , lion ya kamo hannun ta yana matsawa alamar lallashi , da kyar tayi shiru daga baya AHYAN da AYANA suka shigo cikin ɗakin suka yi cheering mood ɗin ta
Daga baya ta tashi taje daƙin me ƙo sai, sun dade suna magana, kafin ta fito
*********
Akwai sauran labari ba iya nan ya tsaya ba,
Akwai
yaki tsakanin LION da LATIFA.
Daukar fan sa, akan AYANA.
Yaƙi domin neman soyayya,
Rikicin ki shi tsakanin A'ishah da ruky
Sa daukar war mahaifi akan yar shi
Hukuncin king luxury zuwa ga latifa
Dana sani mara iya ka
Ku dai ku cigaba da bibiya ta don jin yadda zata kasance
Ga Ramadan ya zoso , ban yi alkawarin cigaba da rubutu ba har sai after Ramadan, saboda iba da duk yadda dai ta kasance
Zaku jiniAyi ibada lafiya

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Roman d'amour* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...