page 74

187 8 0
                                        

             
      "35 vote and comments b4 I updated next chapter.

           Page 74

" Washe gari , tun kafin kowa yazo ruky tayo samma ko da sassa fe, da kayan abin ci niƙi-niƙi, lokacin da ta shigo likita na duba lion yace inshallah ba wata matsala zuwa rana in an duba shi , za'a iya bashi sallama,

Cikin iya yi da feleƙe ruky ta ƙaraso gaban lion ta aje basket ɗin abincin a gefe, ta maƙe murya tana cewa my honey doctor shin dai yanzu kana lafiya,

Kasan kasa bacci nayi da tunanin ko a wani irin hali ka kwana, amma fa honey jiyan Nan ka ɓata min rai da kace in tafi naso in zauna in yi jinyar masoyi na da kaina,

amma na yafe ma ko dan samun lafiyar da kayi da wuri,son da nake ma ma bazai barni in yi fushi da kai na tsawon lokaci ba,

Kasan me da kai na yau na shiga kitchen Dan nama girki , kash na ciki ka da surutu ta shi na kama ka in baka abin ci kaci,

Tun da ruky ta shigo zuciyar A'ishah ta fara zafi, har sai da ruky ta kai hannun zata kama lion , da sauri A'ishah ta shiga gaban ta, ta ture hannun ta daga jikin lion ,

Sannan ta ai ka mata da wata harara da ita kan ta bata san ta iya ba, tare da kallon ƙarya kike baki isa ba,

Ruky cewa tayi ke yadai ya da haka, A'ishah ta mai da mata da eh ya dai mara kunya, yada taba mijin da ba naki ba, oh na ma manta ƙila a gida ba a koyar da ke waenene muhar'rami da kuma wani da ba muhar'rami ba,

Yar dariya ruky tayi, sannan ta ce ai sanin hakan ne shiyisa har yau ba a ganni da ɗa a goye ba,  lion ne ran shi a ɓace ya tashi yana cewa ya isa , ki kiyaye har shan ki da kalaman da suke furta rukayya,

Ko da wasa kada ki sake kuskuren ai bata min ƴaƴa, dan zan mance irin mutum ci da amun taka da ke tsakanin iyayen mu,

Ruky kamar zatai kuka tace amma Honey kana Ganin ita ta fara takalata, mai yisa ita baka hana ta shiga abin da ba a sako ta ba,

Lion yace koma meye ba duba Ni kika zo ba, to na gode kin ga ina lafiya zaki iya tafiya, ruky tace amma, lion ya tare ta da just go ruky if you  don't want me to lose my temper on you,

Rai a ɓace ruky ta kalli A'ishah ta ce mata almajira ƴar shara ta wuce, hannun A'ishah ta kai a zuciye zata janyo ruky ,lion ya yi maza ya haɗa hannayen nata ya riƙe,

Ƴin ƙurin ƙwace kan ta zata bi ruky duk da ta fita daga cikin ɗakin, jan yo ta yayi ya matse ta a cikin shi, amma duk da haka bata dena chuku-chukun kwa cewa ba,

Lion yace stop A'ishah, can't you just stop, Aisha cikin fushi ta ce wato so kake ma ina barta bayan duk abin da waccan yariyar da take kiran kan ta sa masoyi yar ka ta gama gaya baƙa ɗauki mataƙi,

Lion da sausauta Muryar shi yayi sannan yace dukkan ku kuna da lefi , ku kin manta ke kika fara saka iyayen ta a ciki,

Samun damar fisge kan ta tayi tayi ta tashi tana cewa Ni dama na sani, dole haka ta faru, wato Ni ka gama dani, ka ga ba abin da zama sake samu ajiki na, dole ka bar waccan ƙoɗaɗɗiyar tana wani tattaɓa ka,

To wallahi gwamna tun wuri ma ka sani in ma baka sani ba, baka Isa ka shigo da wata mace cikin rayuwar ka in bari ba, in ma kana tunani Ni kamar da ce to a'a na canza, ban da mutum ci wallahi,

Lion gajiya yayi har kan shi ya fara ciwo , jan A'ishah yayi da ƙarfi ta faɗi a saman gadon ya zamana shi koma yana saman ta,

Ya kamo fuskar ta da hannayen shi,  ya ce relax baby girl take a deep breath ( ja dogon nunfashi ) aiko A'ishah sau ke nunfashi kawai ta ɗin gi yi,

Lion ya good girl, to wa ya gaya miki akwai wata mace a rayuwa ta bayan ke da and my princess ayana,

In dai nine ( KECE GUDA ) ke kadai Aliyu yake da muraɗi , ki kwantar da hankalin ki mutuwa ce kadai zata sa ina iya rabuwa da ke bayan ita kuma ban ganin akwai wani abu,

Kallon cikin kwayar idon ta yayi ba tare da ya ɗauke idon shi a cikin nata ba ,yace ke kadai zuciya ta take ƙauna my Shona,

Zuciyar A'ishah a wannan lokacin sai da ta buga ta sake buga, ita ma ta fara kallon shi,

cikin ɗakin cikin yanayin da suka tsinci kan su, da cikin yanayin da suka na kusan ci da junan su, kowanne su na jin fita da saukar nunfashin juna,

A hankali fuskokin su suka fara hade wa hancin su na gogayya da na junan su, cikin shauƙi mai daɗi lamɓan su zai haɗe dana juna,

A cikin wannan yanayin ne aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, bakowa bane face Ahmed, take hankalin su ya dawo jikin su, da sauri A'ishah ta ture lion,

Ahmed ya Sosa Kai sannan yayi gyaran murya kuyi hakuri na ɓata muku yanayin ku bari in koma, You guys should carry,

Lion cewa yayi munafiki bayan ka riga ka shigo, A'ishah ta shi tayi ta gyara jikin ta da sauri ta bar ɗakin, ƙun ya duk ta cika kamar ta tsaga kasa ta shige,

Ko su nafi da bata lura da su ba har ta wuce su, sai ayana ce ta kira ta sannan ta ankare da su, ta ce su wuce bari ta je ta dawo,

Cikin ɗakin A'ishah na fita Ahmed yace wa lion cikin zolaya , shegen gari , yaran nan you'll never left your chance slipped away, ( baza ka taba bari damar ka ta wuce kama)

Wato tun da wuri har ka fara wa su ayaan tana ɗin kanne, I see abu dai a hankali ka bari jinin ka ya gama dawo wa karfi ya dawo kada ya zama Madam ɗin ce zata ja ragama,

Lion ɗaukar pilo tayi ya jefa wa Ahmed yace, ɗan wahala, Ahmed ya kau ce yana mai dariyar shaƙi yan ci,

Ana haka su ayaan suka shigo dukkan su da gudu suka hau saman gaɗau tare da rungume abban su,

*****

Zaria

Latifa, sai kai da kawowa take tana tunani , kala kala amma ta rasa mafutar da zata samu ta mata maganin matsalar ta,

Komai ya chushe mata , a wannan lokacin ma har boka yaƙi sauraran ta, saboda haka ma abubuwa da yawa nata sun tsaya ,

Iya adadin zaman ta a Nigeria, iya adadin lalacewar al amarin ta, Nigeria ba gurin sa ar ta bane, dole ne ta nemo mafita tun kafin komai ya ƙare mata,

Ba dan ran ta yaso ba ta ɗau ko wayar ta, ta danna kiran number shukura, ringing biyu tayi ta ɗauka,

Tace hello ƙawata Please duk in da kuke kizo ki sane Ni ina da buƙatar ki akwai matsala, shukura cewa tayi gata nan zuwa , kana latifa ta kashe wayar ta jefa sama kujera   ta zauna zaman jiran shukura,

Bayan wani lokaci shukura ta iso ta iske latifa zaune a falon gidan ta, ta zauna kusa da ita tana cewa ke yana naga kin taso Ni ina cikin more daɗin duniya,

Latifa cewa tayi dalla ƴar iska kema kin san komai ya lalace amma shine har kika da damar zuwa yawan iskan ci,

Shukura cewa tayi to ban san wulaƙan ci gaya mun mai ya faru, latifa tace da yafi, mafuta nake so mu natsu mu samo , ta yadda samu samu damar sake ɗaukar lion na tafi da shi,

Boka tace sai dai inyi komai da hannu na a wannan karon bazai iya mun komai ba har sai na kawo lion.

Kin san ko ina cikin damuwa indai babu shi tawa ta kare , lion shine nasara ta , zama na a Nigeria kuma shine faɗi ne,

Shukura ce ta ce dama tun da fari dan kin sau rara tane na ce kibi komai a hankali cikin salo da wayau har ki cin ma nasarar ki,

Latifa mugun ta kawai kika fini, amma nafi ki sanin kan solon hanyar mugun ta,

Yan zu dai ba wannan ba, abin da ya kamata ki fara yi shine ki bar Nigeria, latifa tace mene in bar Nigeria da kika ce ,

Shukura ta ce ki tsaya mana ki gama sau rara ta , ki bar Nigeria na zuwa ɗan wani lokaci, kiyi hayar mutane da zasu sama lion Ido na wannan lokacin , har sai shi da ƴan uwansa sun ɗauka tamkar komai ya wuce kin fita daga cikin rayuwar shi,

Sannan sai ke kuma ki dawo ki masa dirar miki ya, latifa jan dogon nunfashi tayi ta sauke sannan tace shike nan zan duba in gani ko hakan zai yi wu,

Shukura tace ai ba duba wa ma zaki ba kawai haka zaki dan shine kawai mafitAr da ta
Rage mana
.........

See yaaa

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now