Page 71
Kusan kwana biyu kenan A'ishah na cikin ma wuya cin hali, sai koke koke take ba irin lallashin da ba amata ba Amma ina abin yaci tura,
Daga ƙarshe malam ya yanke shawara zasu tafi , da A'ishah Abuja har zuwa san da za a ga lion ,
Tafiyar yar da aka tsara , da malam, A'ishah da su AYANA sai nafisah da Aunty sa'a,
Malam sun gaba magana da daddy , yace su dakata ta inshallah, gobe zai tura da motoci da masu basu tsaro saboda yanayin da ake ciki,
Aiko washe gari, da sassafe , motoci da masu tsaron da , daddy ya toro suka iso ,
Dama masu tafiya tun asuba sun gama shiri , fito wa suka yi tare da yiwa su mama sallama, sannan suka shiga cikin motocin,
Cikin a wanni ƙalilan suka iso garin Abuja, in Banda Aishan bana ceba ,
kama da ga Aunty sa'a zuwa nafisah ba wanda ya taɓa barin garin Zariya gwamma malam , dama ya saba zuwa ƙauyukan da ke gefen Kano da Kaduna, sai ko kalle kalle suke
Ɓangare guda daddy yasa aka sauke su , tare masu hidimta musu,
A haka aka ɗauki kusan sati guda, da ɓace War lion , Amma shiri har ila yau ba wani labari,
*******
Ton kawo lion gurin da be san ko ina ne ba, sai yau Allah ya bashi damar kwance igiyar dake ƙulle da hannun shi,
Ba ɓangaren lokaci , ya kwance na ƙafarsa ma , ya miƙe, ya lallaɓa ya gano inda ƙofa take,
Bubbuga ƙofar yayi ya koma ya laɓe, ɗaya daga cikin masu gadin gurin ne ya kalli ɗan uwansa, yace kamar ƙofar nan naji ana bugawa ko kai ma kaji,
Ɗayan yace kai share ƙila kunne kana ya jiyo ma ba dai dai ba,
LION ƙara bubbuga ƙofar yayi , a wannan karon dukkan su biyu ne suka ji ƙarar buga ƙofar,
Kallon juna sukai cike da mamaki , kafin ɗayan su ya tafi dan ya duba, ɗaya kuma ya cigaba da gadin gurin yana ƴan dube-dube,
Me gadin yana buɗe ƙofar ya shiga,. LION ya silalo ta bayan shi ya shaƙe mai wuya tare da toshe mai baki ,
dan baya da buƙata , da yayi ihu saboda bai san iya adadin masu bada tsaron gurin ba,
Yana fita ya hangi ɗaya me gaɗin , a hankali shima ya ƙarasa ta bayan shi ya murde mai wuya har sai da yaji ya dena motsi ,
Mukullin da ya gani jikin mutumin ya zare , yayi gaba , a suɗade amma bai haɗi da kowa ba, da alama latifa masu gadi guda biyu kawai, ta zuba,
Wata ƙofa ya hanga , da sauri ta ƙara sa gurin bisa Sa'a kuwa yana saka key ɗin da ya zare jikin me gadin ƙofar ta buɗe,
Ya fita, sai dai abin mamaki yana fita wani ƙaton daji , ba gida gaba ba gida baya , sai wannan gurin da latifa ta aje kawai,
Addu'a yayi , ya yanki dajin da ke gabansa ya fara gudu , gudu yake cikin dare na tsawon awannin , amma bai fita a cikin dajin ba ,
Har sai da ya fara ganin hasken safiya ya fara fito wa, amma a wannan lokacin ƙarfin shi ya riga da ya fara ƙare wa,
Daga nesa ya fara hango wasu ƴan tsirarun gidajen Fulani , tare da shanaye a garke garke,
Yayi iya ƙoƙarin shi da ya isa rugar fulanin nan amma ina , ƙarfin shi ya ƙare , a hankali yana ji yana gani ya fadi a sume a gurin,
*****
Latifa tana cikin gidan ta dake , Zariya ta gama shiri tsaf, dan a yau ta gama tsara komai zata dauki lion zuwa Brazil, tasa an share mata titi tsaf ,
duk ma aika ta an bisu da cin hanci, dan inta zo wuce kada a samu mai yunkurin tsai da ta
Sai dai tun cikin dare take ta Kiran , yaran ta da tasa su mata gadin lion basa ɗauka , hakan ba ƙaramin har zuƙa ta yayi ba,
Washe gari tana gama shirya wa , ita da yaran ta suka nufi cikin dajin da aka ɓoye lion, motichin guda uku suka yi fakin wajen misalin sha biyun rana ,
Buɗe mata ƙofa suka yi ta fito , ganin gidan a bude yasa ta cire gilashin ta , bakin ta ya furta what ,
Lallai ma wa'in nan wawayen suna nema wa kan su mutuwa , ita da wasu daga cikin yaran ta suka shiga cikin gidan sauron suka tsaya a waje suna gadin gurin,
Mutun ɗaya suka fara cin karo da shi a kwance ba alamar nun fashi tattare da shi , da sauri ta nufi dakin da a kasa lion zuciyar ta na mugun buga wa,
Tana ture ƙofar ta shiga ta kusa yin tuntuɓe da ɗaya mutumin, amma sai dai ba lion a cikin , dakin take taji wani baƙin ciki da ɓacin rai ya danne mata ƙirji,
Wani iyu tayi , wanda sai da saurin ihun ya mamaye dajin , magana ta fara, tana cewa ina bazai yiwu ba, baza ka taba iya guje min ba , dan Ni aka yi ka , kai nawa ne ni kadai ,
Sai da ta gaba san batun surutun ta , kana ta fito,ta nuna yaran ta, a fusace take ce musu , kuje ku nemo min wancan ƙaramin ɓeran , na baku nan da awanni biyu , nasan ba
Be yi nisa ba bazai wuce cikin ƙauyi kan da suke kusa da nan ba, a tsawace tace kuna jina , suka amsa da Yes ma, kafin suka shiga cikin daji , farautar lion ,
*****
Wasu magidan tan Fulani ne suka koro shanayen su dan tafiya kiwo,
Sun zo barin cikin rigar su zasu shiga cikin daji , suka iske mutun akwan ce ,
Kallon juna suka yi, ɗaya daga cikin su yasa sandar dake hannun shi , ya tattaɓa jikin lion da shi,
Amma bai ga anyi motsi ba , cewa sau ran ƴan uwan shi yayi , wannan ta ruga da ta mutu,
Wani ya tsugonna ya kai hannun shi daidai hana cin lion , yaji Yana nun fashi , da sauri yace aradun Allah da sauran ta, tana nun fashi ,
Da sauri mutun biyu Daga cikin su suka cicciɓe shi , sai gurin ardo wato mai garin su kenan,
Suna zuwa ya basu guri aka shin fude shi , kafin suka gaya mai dalla dalla abin da ya faru ,
Arɗo ya ciro wayar da jami'an tsaron Nigeria suka bashi musamman in irin haka ta faru, ya kira su ya sanar da su abin da ke ........

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...