Page 37
Not edited
" ki maza kizo gida ina son ganin ki, ki kira yan uwan ki kuzo tare yan zun nan,
ya mardiya ta ce to mama amma dai lafiya ko, mama tace ke dai kuyi maza kuzo dan Allah, sannan ta ka she kiran ,
Ta koma ta zauna tayi ta gumi, zuwa wannan lokacin Aishah ta yi shiru ta ɗe na kuka, ta haɗa kan ta da gui wa sai ajiyar zuciya take sauƙe wa,
Can ɓangaren yaya Sa'a kiran naja da mardiya tayi ta ce su haɗu a gida mama na neman su, suma tambayar ta sukai da lafiya tace su dai suzo zasu ji me ke faruwa itama bata sani ba,
Sannan ta kira mijin ta ta tambaye shi izinin fita ya yace ta dawo lafiya, kafin ta tashi ta canza zanin dake jikin ta ,
tasa hijabi ta rufe gidan ta bawa maƙota key in yaran ta sun dawo a basu , ta tare mashin ta hau,
A dai-dai ƙofar gida aka sauke ta na kafin ta shiga cikin gida sai ga yaya mardiya suka gai sa suka shiga tare ,
sallama sukai su ka shiga gidan iske mama sukai, suka tsugunna suna gai she ta,
suna cikin gai sawa sai ga yaya naja ta shigo cikin gidan itama , sai da aka gama gai sawa,
Yaya Sa'a tace mama ina malam, mama tace malam yana ciki , mama ta ƙara da gaya musu duk abin da ya faru da ga shigo War malam har shigo wa Aishah tana ,
Kuka, sai a lokacin suka lura da Aishah da ta faɗa duniyar tunani, yaya mardiya ta ce Tofa kuma lafiya ƙalau Aishah ta fita daga gida,
Yaya Sa'a ta tashi tace bari ta shiga gurin malam ɗin, ta shiga cikin ɗakin tana ta sallama malam bai amsa ba ya lula duniyar tunani,
sai da yaji alamar motsi kafin ya dawo cikin hankalinsa, Sa'a ta samu guri a gefe ta zauna ta gai she shi,
Ya amsa, ta tambaye shi ko lafiya shin ko akwai wani laifi da Aishah ta mai ne, malam yayi shiru bai bata amsa ba,
Yaya Sa'a tayi-tayi, har sai da ya kai ga ta saka mai kuka kafin baba yace zai gaya mata
amma kafin nan ta je ta shigo da ƴan uwan ta , Sa'a ta ta shi ta fito waje ta ce musu su shigo ciki malam na neman su,
kowa ya shiga ya rage Aishah ce kawai a waje bata san ma wai bar da ake toya wa ba, dukan su da shigar su ɗakin suka nemi guri suka zauna , suka gai she shi ya amsa.
Sai da malam ya jima yana saƙe saƙe a cikin zuciyar shi ta yaccen zai fara magana ,
ɗakin yayi tsit gaba ɗaya kowa yayi shiru yana jira yaji mai malam zai ce,
Sai can yayi gyaran murya yace, ban taɓa zaton ko tunani ko kuma nayi mafarkin irin wannan rana zata gama ta a cikin ranakun rayuwa ta ba, naja tace malam mai ya faru haka maradaɗi ba musani ba,
Malam jan nunfashi yayi yace cin amana ta akai, dukan suka haɗa baki suka ce cin amana kuma, mardiya tace amma wacce irin cin amana aka maka haka malam,
Malam yace har kina da bakin tambaya ta mardiya, bayan da ke aka haɗa baki aka ci amana ta, mardiya ta dafa ƙirjin ta tace Ni kuma malam ,
taya zan iya cin amanar wani barre kai malam, kasan irin tarbiyyar da ka mana hakan bazai sa muje muna cin amanar mutane ku yin wani abu da ba dai-dai ba,
Malam ya ce daka ta min a gurin , ku sani dukan ku da ina da tabbacin irin ingan tat ciyar tarbiyyar da na baku ,
Amma yau na fara shakku ku akwai ta inda na gaza da har ɗiyar ciki na, zata je tana aika ta abin kun ya irin wannan,
Tun da nake a rayuwa ta ban taɓa aika ta wani lefi da mutane zasu taru suna aiba tani ba, sai yau ƴata ta jawo min abin da fita ƙofar gida ma sai ya gagare,
Wai ace ƴar ciki na dana haifa ita ke bin saurayi gida suna aika ta saɓon Allah Ni ina nan zaune ashe duk unguwa kallo na suke akan uban da ya gaza bawa ɗiyar shi tarbiyya,
Yau dubu ta cika anka ma Aishah a gidan saurayi suna aika ta saɓon Allah, nima Allah yayi yau na sani,
Amma meye lefin da na miki da zaki kasa gaya min cewa Aishah tana kulla wani saurayi ba yan mijin da na zaɓa mata,
Kawo iyan zu , daga yaya mardiya zuwa yaya Sa'a kuka kawai suke, yaya mardiya ko ita kuka take tana cewa Wallahi malam ban sani ba , ban san abin da ke faruwa kenan in Aishah ta fita zuwa gidan nan ba,
Mama ko inalillahi wa'in na ilaihir'raju'un kawai take maimaita wa, yaya naja ta tashi ta fita a zuciye,
Kan Aishah tayi ta shaƙo ta, ta buga ta da jikin ban go, sannan bata batta ba , ta kuma rufe ta da duka, da guɗu yaya mardiya ta fito ita ma ta shiga dukan Aishah,
Su mama ne suka fito, yaya Sa'a ta kwaci Aishah daga hannun su, Aishah ko motsa jikin ta ta kasa yi,
Sai yaya Sa'a ta jata gefe ta jin ginar da ita, malam ya kalli su , yace kar wani ya sake dukan ta ku batta da duniyar zata koyar da ita darasi,
Malam yana gama cewa haka ya sa kai ya fita, yana fita dukan su suka zauna bamai furta komai, sai kukan zuci da tunani ,
Malam ku da ya fita Masallaci, ya tada salla, tun da luƙa cin sallar aza har yayi,
Abin mamaki ƴan unguwa ko mutum ɗaya ba wanda ya halacci masallacin ayau ɗin zai almajiran shi, haka aka idar da salla malam ya dawo gida,
Ya iske kowa a inda ya barshi, sai nafisa da tazo tana tsugunne kusa da Aishah tana tan bayar ta waye ya mata irin dukan nan,
Yaya naja ta bata amsa da mu mukai mata ku zaki rama mata ne, nafisa ta tura bakin ta gama, tana cewa ko wani irin lefi ta kuma ai bai kamata kuyi mata irin wannan dukan ba, sai kace wata yarinya,
Mardiya ta ce duk wanda yabi hanyar Iskan ci ai dole ya amsa fiye da irin wannan hukunci,
Naja cewa oho ai yanzu na gano kan zaran kun wani zauna jigum jigum kamar wa'in da aka wa mutuwa,
Oh wato duk akan yarinya ta nuna bata son zaɓin malam tana da wanda take so shi ne za a mata irin wannan hukunci to ai ba ita ka ɗai zaku wa ba nima sai ku haɗa har dani, tun da Ni na fara bijire wa,
Naja itacen dake kusa da ita ta ɗauka ta jebi nafisa da shi tana cewa oh neman naki kike kema kenan , tsale nafisa tayi ta kauce wa icen ya faɗi age Fe,
Nafisa ta ce ai gaskiya na faɗa sai dai in baƙo san a gaya muku , dan ku an muku aure ba tare da kun ce kuna so ba, mu da muke yaran zama Ni ba lallai mu yar da amana irin wannan aure ba, mun yi karatu mun san ƴan cin kan mu ba mai mana dole ehe
Malam da yake tsaye yana jin duk faɗe faɗen da nafisa ta ke , ya ƙara sa shigo wa, nafisa na ganin shi tayi shiru ta na gai she shi ,
Malam bai amsa mata ba yace , naji duk saƙon ki na goɗe kuma sai dai kuma ki sani daga yau na baki Umar nin zuwa ke da mardiya ku kwaso kayan ku ,
ku dawo nan gidan, ban san ku ƙara kwana a wani gida, dama ke mardiya dan taka ba kike to alhamdulillah yan zu kin gama sai ki dawo gida mu zauna duka,
Ku kuma ya nuna mardiya da naja ya ce ku tashi kuyi salla ku koma gidajen maza jen ku,
Ita kuma wannan ya nuna Aishah daga yau ban san aƙara barin ta, taka koda ƙofar gidan nan ne,
kuma duk aikin gidan nan daga wanki shara da wanke wanke da girki na kowa da kowa a gidan nan ita zata rinƙa yi, ban san a saurara mata koda na misƙala zar ratan,
Malam na gama cewa haka ya shiga cikin ɗaki , kowa ya tashi yaje yayi alwala,
Nafisa ta ɗaura wa Aishah ruwa mai zafi tayi wanka ta gaza jikin ta, duk bakin ta ya fashe , fuskar ta, ta kuk ƙun bura, nafisa ta bata paracetamol ta sha ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta,
Su yaya Sa'a suka wuce, mardiya da nafisa suka wuce dan cika umarnin malam..
************
Shin kuna ganin Aishah ta cancanci duk hukuncin na,
Ku biyu Ni dan jin yacce zata cigaba da kasan cewa a cikin rayuwar Aishah,
Kada ku manta muyi following ɗina, tare da vote and comment share to your love ones,
Nagode..
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...