Page 44
( aslm readers nasan za kun jini shiru kusan wata biyu, na gamu da hatsari ne ranar da zan rubuta jarabawa ta ƙarshe ranar da zan gama School amma yan zu na samu sauƙi , inshallah daga wannan lokacin zaku cigaba da ji na, dan nima a yadda na tsara na so kawo i yan zu na gama wannan littafin sai dai muna namu Allah na na shi ta shi shine dai-dai ina mai ƙara baku haƙuri na zaman jira )
Gaban ta ne ya ke ta fa ɗuwa tun san da mama ladi ta aika a kira ta, ta zo ta same ta a gida,
Tafiya kawai take tana furta innalillahi wa'in na ilaihir'raju'un, har ta ƙara sa gidan ta tura ta shiga bakin ta ɗauƙe da sallama, ba wan da ya amsa mata kamar kullum,
Itama bata kalli kowa ba tasa kai ta shiga cikin ɗakin mama ladi, mama ladi na zaune saman ƙa tifar ta , tana shafa powder,
Ganin shigo War A'ishah yasa ta aje a gefe ta ɗauƙi wata leɗa dake gefen ta ta wur ga wa A'ishah a gefen ƙafar ta , tana cewa yi sau ri yi maza je kiyi wanka kisa kayan da ke ciki kizo akwai in da zamu,
Dum gaban A'ishah ya bada amma batai mata musu ba ta ɗauƙi ledar ta fita a cikin ɗakin,
Bayan tayi wanka ta shafa mai , zazzage kayan da mama ladi ta bata tayi, wata doguwar riga ce Wanda daga ganin in A'ishah ta sa su sai an ga ko wani sassa na jikin ta bata ma da maraba da tsirara,
Goje wa rigima A'ishah ta ɗauƙi rigar dan ta gwada, rigar ta kame ta kam, hatta ɗan cikin da yake four months da kwanaki ya fito ɗan ƙarami da shi,
Da sauri tayi maza ta cire dan ita kan ta ma kun yar kan ta taji, wata abaya ta ɗau ko cikin kayan tasa ,
Ba ƙaramin kyau tayi mata ba , kuma sannan duk muna fur cin mutun baze ce ciki ne a jikin ta ba,
Yafa maya fin abayar tayi, ta ɗauƙi ƙaramar jakar ta, tasa ɗari biyar a ciki , cikin kuɗin da mama ladi ke basu kullum in an tashi aiki,
Sannan ta fito, mama ladi na ganin ta ta wurga mata harara, har miyau na fita a bakin ta saboda Masifa, tace ina kayan da na baki nace kisa,
Dur ƙusar da kan ta ƙasa A'ishah ta yi, dan ba ƙaramin tsoron mama laɗi take ba,
Tsawa mama laɗi ta daka mata tace ba dake nake magana ba , ki ka wani sun kuyar da kai kai kamar an kama tsohuwar muna fuka,
Jikin A'ishah na rawa tace cikin kak kakwar, da sun min kaɗan sun ƙi shiga ta ne, tsaki mama ladi tayi , tace ai kece kullum cikin hijabi sumu mi sumu mi taya za a san kayan da zai miki dai-dai
Ƙare wa A'ishah kallo tayi sama da ƙasa , sai yanzu ta ga irin kyan da A'ishah tayi, ba ƙar ya tayi kyau ko ma ƙiyi ya gan ta dole ya yaba,
Harara Mama ladi ta wurga mata ta fita, A'ishah ta bita a bayan, ƙatuwar mota suka gani a fake a ƙofar gidan ,
Da sauri wani mutumi ya fito daga sit ɗin driver yana gai she da mama ladi, mama ladi cikin ya tsina fuska ta amsa, ya buɗe musu gidan bayan, mama laɗi ta sa A'ishah ta fara shiga kafin itama ta shiga,
Drivern ya ja mota suka bar unguwar, unguwanni masu kuɗi dake dauke da manya manyan gine-gine sukai ta wuce, har suka kawo wata unguwa , mai masifar kyau, ba kowa unguwar shiru,
Wani ƙaya taccen gida, aka bude get ɗin driver ya shiga da motar cikin gidan , sannan ya fito da sauri ya buɗe ma su A'ishah suka fito , mama ladi ta nufi ƙofar shiga A'ishah na biye da ita a baya, har suka shiga cikin,
Wasu manyan mutane suka tarar suna fira a cikin falon da ka gani kasan sun ci kuɗi sun ƙoshi , ko wannen su ya aje uban ciki
a gaba , ɗaya daga shi sai gajeren da vest yana wata uwar dariya kamar boss,Ganin mama laɗi yasa ya sake fashe wa da wata dariyar yace Hajiya laɗi ashe kin iso, mama ladi ta ce wallahi kam,
Idon shine ya kai kan A'ishah yace a'a'a sannu da zuwa baby , dan tsuguna wa A'ishah tayi ta gai she su,
Su Alhaji bawa suka washe baki su na amsa wa, tare da bin ta da wani maya tac cen kallo,
Koma wa gefe A'ishah tayi ta zauna a raku ɓe duk ta tsar go da irin kallon da suke mata,
Alhaji bawa yace Hajiya laɗi kenan Hajiya laɗi Hajiyar wuta, wani far da ido mama ladi tayi , tace uhmm Alhaji kenan,
Alhaji bawa yace Hajiya laɗi ashe kaya masu zafi sun sau ka haka,
Abokin Alhaji bawa ale sabo yace Hajiya laɗi ashe kuna gari kwana biyu shiru babu labarin kun
Mama ladi tace ale sabo kenan kai dai baka rabo da tsoka na da abin dariya kwata-kwata ya kai sati da muka kawo ma ziyara,
Fashe wa da wata basa mudiyar dariya ale bawa yayi yace ai kune Hajiya laɗi ba a gajiya da ziyarar ku,
Murmushi mama ladi tayi, ale bawa ya ɗaura da cewa naga sabuwar fuska kun yi baƙuwa ne, yana cewa haka yana kashe wa A'ishah ido,
Subhanallah A'ishah ta furta cikin zuciyar ta tana neman tsari daga sharrin su, duk ta matsu su bar gurin,
Magana Alhaji bawa yayi wa ale sabo a kunne naga ale sabo ya tashi yayi sallama ya wuce,
Fira Alhaji bawa da mama ladi suka cigaba wan da A'ishah kwata-kwata ta kasa fahimtar me suke nufin dan magana suke a jujjuye ,
Chan sai mama ladi ta tashi, A'ishah zuruf tayi ta miƙe dan dama a kage take da su tafi, harara Mama ladi ta cilla mata tare da cewa to ina zaki kuma,
A'ishah ta ce cikin rawar murya, ba ba tafiya za muyi ba, mama ladi ta ja tsaki tace sai nace ki biyu Ni,
To ki buɗe kun ne ki saura re Ni , zan je na dawo mu tafi ki zauna anan ki jira Ni , kuma duk abin da Alhaji bawa ya buƙata ki masa,
Hawaye ne ya tsiyayo ya sauƙo saman fuska A'ishah, mama ladi ta ce kina jina ko, A'ishah da kyar ta amsa tace eh,
Gaba mama ladi tayi ta fita a gidan, can ƙar she nesa da Alhaji bawa A'ishah ta koma ta zauna a ra kuɓe ,
Alhaji bawa yace baby kenan me kike so kisha a kawo miki, shiru A'ishah ta yi bata bashi amsa ba, maga na ya cigaba da yi A'ishah bata dai kula shi ba,
Har ya taso ya zauna kusa da A'ishah, zabura A'ishah tayi ta matsa can gefe, jikin ta na rawa,
Alhaji bawa yace baby ki natsu mana sai kace ba ƴar gari ba fira za muyi,
Me kike so ki siya, nasan ku mata akwai ku da san iphone wacce daga ciki kike so yan zu in yi waya in sa aka wo miki, shiru A'ishah tayi bata amsa mai ba, Alhaji bawa ya sake cewa ko chocolate kike sune dai,
Ganin A'ishah baza ta kula shi ba ya sa tam ƙe fuska , yace ta shi ki je ki gyara min wan can ɗakin , ya nuna mata wani ɗaki dake chan sama ,.
A'ishah bata kawo komai a ran taba , ita daɗi ma taji ganin daga ƙar she da bai samu fuska zai bar ta tayi aikin da aka kawo ta tayi,
Ta shi tashi sumi-sumi ta haura sama, ta buɗe ɗakin da Alhaji bawa ya nuna mata sai dai mai makon ta .........
See you soon
Don't forget to vote and comment share to your love ones
Thank you

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Roman d'amour* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...