✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Page 91-95
" Sallama A'ishah tayi ta shiga cikin gidan , ta tadda nafisa zaune a tsakar gida tana latsa wayar ta,
Amsa sallamar tayi tace au ashe kece, A'ishah ce tayi:" ina anti sa'a tare da zama kusa da nafisa,
Nafi amsa ta bata kar dai ace baki sani ba, A'ishah tace me kenan, nafisa tace:" mijin anti mardiya yayi hatsari yanzu haka suna asibiti,
Inalillahi wa'in na ilaihir raju'un shine abin da bakin A'ishah ya furta, ta tambayi nafisa garin yaya , nafisa tace wallahi nima ban sani ba kiran mu akai aka gaya mana, ya Sa'a ce taje Ni kuma kin san yara na makaranta kar su dawo basu ga kowa ba a gida,
Wayar ta A'ishah ta Ciro a cikin jaka, taga miss call wajen guda 20 daga na mama sai na ya mardiya,
Number mama ta Kira , ringing ɗaya mama ta ɗauka, tana cewa hello A'ishah wai ina kika shiga kika bar wayar ki ne ana ta kira,
A'ishah cewa tayi ya haƙori mama da safe ina fita aka kira Ni aka ce muna da lecture a lokacin shine na wuce sai yanzu nazo gidan ya Sa'a nafi ta gaya min abin da ke faruwa,
Ya jikin nasa A'ishah ta ƙara da gaya, mama ta amsa da sauƙi, yanzu kiyi maza-maza ki wuce gidan yayar taku mardiya ki kula da yaran , amsa wa A'ishah tayi da to ,
Kafin ta kashe wayar, tashi A'ishah tayi tana cewa nafi bari in wuce banga ta zama ba, mama tace naje gidan ya mardiya, nafi cewa tayi ok sai gobe kenan, sallama sukai A'ishah ta fita a gidan,
Dan karta ɓata lokaci gurin zuwa ganin da kuɗi a jikin ta yasa ta tsaida mai mashin ta gaya mai inda zai Kaita , sukai ciniki ta hau ya tada mashin ɗin,
A dai-dai ƙofar gidan ya mardiya me mashi ya aje ta , ta Ciro kuɗi a jakar ta , ta bashi ta shiga cikin gidan,
Da sallama ta shiga cikin gidan , yarinyar ya mardiya Amina ta taso ta rungume ta tana mata oyoyo, shafa kanta tayi tana tambayar ta me ya faru da jabir yake kuka haka,
Kallon ƙanin ta daya ke kuka shaɓe-shaɓe da majina Amina tayi tace ohun mishi na bashi abin ci ya cifa , wai sai dai in Kai shi gurin maman mu, kuma mun dawo school bamu ganta ba,
Zuwa tayi A'ishah ta kamu hannun jabir ɗin tace yi shiru dena kuka maman ka ta kusa dawowa taje unguwa ne,
Da kyar ta lalla sheshi yayi shiru , ta musu wanka ta basu goma-goma suna murna suka wuce islamiyya,
Share gidan A'ishah tayi ta gyare shi tsaf, kafin ta shiga kicin ɗin gidan ta daura san War tuwo da miya, tana cikin aiki ne taji wayar ta dake kusa da ita na ruri , sunan lion ta gani ta ɗaga kiran fuskar ta cike da murmushi,
Tayi sallama lion yace nayi fushi da ke A'ishah ta ce subhanallah me nama, lion cewa yaya cewa akai an ganki a mashin ɗin haya , duk tarin motoci na haba
Rose flower
Aishah marairai ce murya tayi tace I'm sorry yah aliyu , gaya mai abun da yake faruwa tayi,
Lion yace oh Allah ya kiyaye gaba ya bashi lafiya , A'ishah tace ameen fira suka yi bayan wasu mintina suka yi sallama da juya ,
Rungume wayar A'ishah tayi a ƙirjin ta tana sauke ajiyar zuciya tare da sakin murmushi, ita kadai tasan me take ji acikin zuciyar ta wanda bata san ta dena jin kallar yanayin sam , ta fiso ta dan wama a haka, ta mutu a haka,
Cigaba da aikin tayi ba dade wa ta gama, ta zuzzuba a mazubi ta ƙyara, gurin.
Ba dade wa su amina suka yi sallama suka shigo gidan, Amina ta wa A'ishah sannu da gida ta zauna kusa da ita tana cewa wash na gaji wallahi,
jabir yana tsaye yana wutsil-wutsil da ido, yaja ya tsaya yana taɓe fuska alamar zai yi kuka,
Kallon shi A'ishah dake kan tabar ma tayi, ta mai nuni da hannu da yazo,
Ƙara sowa ya zauna shima a gefen A'ishah, tan bayar shi A'ishah tayi tace meye, kamar jira yake ya fashe da koka , da kyar A'ishah ta lallashe shi, yayi shiru ,
Ƙara tan bayar shi tayi a karo na biyu menene, cikin shesh sheƙar kuka da yace maaa maan mu, yana fada hawaye na zubo mai,
Sake lalla shin shi A'ishah tayi tace yanzu zata kai shi gurin ta,
Abin ci ta zuba musu suka ci , ta musu wanka ta shirya su ta zuba kulolin abin cin a Dan basket,
Suka fita, ta rufe gidan, bakin titin unguwar suka ƙarasa ta tari abin hawa ta gaya mai inda zai Kaita, suka yi ciniki, kafin ta shigar da yaran itama ta shiga,
A dai-dai bakin asibitin mai adaidaita sahu ya aje su, ta biya shi kudin kana ta kama hannun su amina suka shiga cikin asibitin,
Da tan baya suka ƙara sa ɗakin da ake aje yan hatsari, babban hall ne guda, da ke ɗauke da majin yata, kusan guda talatin ko wanne majin yaci yana jin jiki na wani ya fin wani abin gwanin ban tausayi , in kaga wani ma saika zubda mai da hawaye dan tausayi ( Allah ka bawa marasa lafiya-lafiya na gida dana asibiti, mu kuma da muke da lafiya Allah ka ƙara mana lafiya dan girman Annabi da Alqur'ani )..
bata sha wahala ba ta gano inda su yah mardiya suke ba, a zaune ta same ta tayi ta gumi ita kadai, tsallen da jabir ya mata a jiki ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta lula,
Tana cewa A'ishah sannun ku , ta shi ya mardiya tayi daga kan kujerar da take zaune ta koma gefen gadon da mijin ta ke kwance akai ta ɗora jabir akan cinyar ta , zama A'ishah tayi ta gai sheta tana mata ya me jiki,
Yah mardiya cewa tayi da sauƙi , kin gan shinan tun da aka mai alurar bacci bai tashi ma likitan yace sai zuwa cikin dare zai tashi,
Tan bayar ta A'ishah tayi su mama fa, yah mardiya ta bata amsa da basu dade da tafiya ba , su A'ishah sun kai kusan 30 minute da zuwa asibitin lokacin an kusa kiran sallah magrib,
Wayar A'ishah tayi ƙara ta tashi ta fita dumin amsa wa, lion ne ya kira, gaya mai tayi tana asibiti , ya tan baye ta zuwa wani lokaci zata dawo tace nan da minti ishirin ,
Lion yace ta jira shi zai zo ya dau ke ta , sallama sukai A'ishah ta koma ciki, bayan wasu dogon minti toci A'ishah ta cewa yah mardiya,
Naga dare ya farayi bari mu wuce Allah yaba shi lafiya, da kyar jabir ya yadda suka tafi, da fitar su basu fi min ti biyar ba a tsaye a bakin asibitin sai ga motar lion ta faka a gaban su ,
za gaya A'ishah tayi ta buɗe wa Amina da jabir bayan motar suka shiga suna sissinne kai suna gai she da lion , ya amsa ba yabo ba fallasa Dan lion shi ba mutumin yara bane kwata-kwata bai saba dasu ba, bude gidan gaba A'ishah tayi ta shiga, baƙin ta ɗauke da sallama tana sakar wani kyakkyawan murmushi,
Amsa sallamar lion yayi shima yana sakar mata shu'umin murmushi tare da Binta da wani mayan kallon,
Tan bayar ta yayi ya mai jiki tace da sauki, yace Allah ya ƙara sauƙi kafin ya tada motar suka bar asibitin,
A Hanyar su ta zuwa gida ya, suka tsaya a wani guri da ake sai da gasassun kaji , lion yayi packing motar a gefen gurin ya fita yaje ya siya ,
be dade ba ya dawo da ledoji uku a hannun shi ya aje a gefen ya tada motar suka cigaba da ta fiya,
A dai-dai ƙofar .....
Vote and comment

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Storie d'amore* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...