Page 50
Doctor ji tayi zuciyar na bugawa a hankali, ta yi saurin riƙe kafuwan shi ya zama na kan shi ya na kallon ƙasa, ta shiga jijjiga shi, ba jima wa ya shiga jan dara ƙara,
Ham dala doctor tayi ta miƙa nurse shi dumin su gyara shi ita kuma ta shiga duba A'ishah , A'ishah har baccin wahala ya ɗebe ta,
Umarni doctor ta bada cewa da zarar ta ta shi a haɗa mata shayi da ruwan zafi ta sha, sannan su temaka mata taba yaran nono
Nurse na gaba gyara yaron suka naɗe shi a zani, suka fita da shi , me ko'sai suka kai wa, dama tuni me ƙo sai ta goya macen tana shan dumin bayan ta,
cike da murna da godiya ga Allah, ta amshi yaran tana ƙara rufe shi da zani, sannan ta tambayi ya jikin A'ishah nurse ɗin ta amsa da tana lafiya ta samu bacci da ta tashi za a kira ta,
Godiya me ƙi sai ta mata ta koma gurin da take zaune ta zauna, zaman jira,
*******
Sai da asuba misalin ƙarfe biyar A'ishah ta tashi, nurse ɗin dake lebour room ɗin ne ta lura da ta tashi , zuwa tayi ta temaka mata ta zauna,
ta haɗa mata shayi ta bata , A'ishah bata yi musu ba dan tana bukata a wannan lokaci, sai da ta shan Yesu tass kafin ta aje kofin a gefe,
Nurse din fita tayi dan ta kiran me ƙo sai , me ko sai nacan na fama da yara sai kuka suke suna neman abin ci , jin cewa A'ishah ta tashi sai tayi ham dala ta wuce ɗakin haihuwar, suma yaran kamar sun san me ke faruwa suka haɗa baki sukai shiru,
A zaune me kosai ta samu A'ishah , cewa tayi sannun ki ƴar nan barkan ki dai, sun kuyar da kai ƙasa A'ishah tayi ta amsa me kosai ciki ciki da yauwa,
Nurse ɗin tace Madam gyara zaki yi breastfeeding yaran , A'ishah yi tayi kamar bata ji taba , nurse ɗin ta sake maimaita abin da ta ce amma A'ishah tayi biris da ita ba wai dan bata ji taba sai dan kawai bata ji zata iya abin da aka ce ɗin bane,
Me ƙo sai cewa tayi ƴar nan gyara mana ki Basu abin cin su, A'ishah dan tura bakin tayi, nurse ɗin tace batta dai baba karta buɗe ta basu ta bari na kira nurse sun danne min ita,
Inda mijinta ne , baza ta san ma lokacin da zata buɗe mai ba jikin ta na rawa, sai an zo gurin haihuwa su rinƙa nuƙe-nuƙe to in baƙi buɗe ba taya kikai cikin
Madam bude ko na kira nurse yan zun nan , A'ishah ba dan taso ba ta buɗe , nurse ɗin ta amshi macen a hannun me ƙo sai ta sai ta dai-dai,
aiko ana sa mata yariyar ta fara ja da ƙarfi kamar wacce tayi kwana biyar bata ci ba , A'ishah jin wani bala'in zafi tayi, ta saka ɗan ƙara tana cije baki, haka dai ba dan ta so ba ta basu su duka biyu,
Na mijin take bawa a yanzu, ta zuba mai ido kawai tana kallon shi yaran ba inda ya bar kamamnin ma haifin shi gwamma macen tana ɗan kama da ita,
Ita abin ma ƙara bata mama ki yake wai yau ita ta haihu , ba ma ɗaya ba har biyu , lallai Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso, a baya in aka ce duk haka zata faru da ita ,
ba wani ja zata rantse hakan baza ta faru ba, ba ita Bama wani ma da ya san ta zai ce haka zata iya faruwa da ita ba,
Fatan ta Allah ya bata ikon kula da su da basu tarbiyya bata re da ta Gaza ba,
Gama Basu nono tayi duk sunyi bacci ita ma kwanciya tayi tai baccin,
Garin Allah na waye me ƙo sai tayi hana zari ta koma gida, ta kimtsa duk wani abun da zasu buƙata in an sallamo su, tare dayin abin kari da kunu , tare da maƙociyar ta suka dawo asibitin,
Wajen misalin ƙarfe goma, A'ishah ta ci abinci ta sake bawa yaran nono, ko da mai ƙo sai ta wuce gida ɗasu kwan ciya kawai tayi ba tare da tayi bacci ba gani ta da ta rufe ido ta buɗe zata ga wani abu ya same , ƙo taga duk mafarki ne,
Wato wata irin soyayya yaran ce ta shiga cikin zuciyar ta fiye da yadda take son kan ta da kowa ma , ji take har Gara abu ya cutar da ita da wani abu ya same su,
Zuwa sha biyu na rana doctor ta shigu za Gaye, ta Basu sallama, amma after one week zasu dawo a duba lafiyar yaran saboda namijin har yanzu numfashin shi baya fita da kyau sannan a goje sa miji sabulu a hanci ,
Sai da suka dau hotuna, doctor da kan ta, ta biya kuɗin asibitin, ta ƙara musu da ten thousand tace a haɗa a sewa yaran riga, godiya me ƙo sai ta rinƙa yi ma doctor , doctor ta ce ai ba komai an riga da an zama ɗaya,
A'ishah ma cikin jin kunya tace wa doctor an gode, doctor tace ba komai ƙan wata ba dai inda ya ke miki ciwo ko,
A'ishah ta ce eh, jiki na ne kawai, doctor ta ce shima zai tafi ina kika koma gida kikai wan ka sannan ki rinƙa shan magungunan da aka baki,
Godiya suka sake yi kafin suka wuce,
Suna kai wa gida me kosai ta daura ruwan zafi a ƙatuwar tu kunya,
Nan ma da aka zo wanka sai da aka sha daru da A'ishah kafin ta bari aka mata,
Suma yaran aka musu wanka, aka gasa su, sannan aka sanya musu kayan sanyi suka cigaba da bacci,
Ma ƙota da abokan arzikin me ko sai ne suka rinqa tururuwar shigo wa Barka, wasu ma ɗan kawai suga kyawun yaran da ake labari suke shigo, abin da ya cigaba da faruwa kenan har dare yayi, kafin masu shigo wa suka ragu
*********
To masoya gafa na ƙarshen sati sai kuma in Allah ya kai mu ranar Monday amma fa in kunyi comment da bore kamar guda talatin,
Ganin comments ɗin ku na faran tamin rai,
Kada ku manta kuje ku duba new novel ɗina nisan kiwo
.na gode ina muku jumma'a Mubarak

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...