Page 51
( Duk wan da ya ƙaran ta ba tare da yayi like ƙo comment ba shi da mahalicci )..."Haka ma washe gari tun da safiyar Allah mutane suka cigaba da shigo wa yin Barka haɗe da tsegumi,
Me ƙo sai ta tambaye wani irin suna ya ka mata a sa musu dan yan zu zamani ya canza da an haifi yaro ake ra ɗa mai suna na ba sai an jira ranar suna ba,
A'ishah ta ce dama tun tuni ta yanke shawarar in ta haifi mace zata sa mata AYANA in kuma namiji ne zata sa mai AHYAN tun da yanzu Allah ya bata duka , to zata san ya musu duka sunan
Me ƙo sai cewa tayi ƴar nan wannan wani irin suna ne haka A'ishah mur mushi tayi ta ce baba suna ne mai ma'ana da duka ma'anar su kyauta daga Allah
Amma namijin za a samai Muhammad wani da sunan baban mahaifin shine, sai a dinga mai in kiya da ayan, me ƙo sai ta ce to masha Allah , bari nasa yara su kira min liman sai ya musu huɗu ba,
Tashi tayi ta fita waje ta samu yaran da suke wasa ta aiki ɗaya a ciki sannan ta koma gida,
Ba dade wa suka ci ana ran gaɗa sallama daga zauren gidan, tashi me ƙo sai tayi ta dau ƙi tabar ma ta fita , a zauren ta samu limamin unguwar,
tabar mar ta shim fiɗa mai suka gai sa ta gaya mai dalilin da yasa ta aika a kira shi, malam liman yace bisimillah aje a fito da yaran , tashi me ko sai tayi ta koma cikin gida
Ta ta ɗauki yaro ɗaya tasa A'ishah ta biyu ta da ɗaya dan tace baza ta iya faɗar sunan ba,
A'ishah gai she tayi ya amsa yana tambayar ita ce mahaiyar su mai ƙo sai ta amsa mai da eh yace masha Allah tare da yi mata Barka da samu kyauta daga Allah har rai biyu,
Faɗa mushi sunayen akai ya musu huɗu ba, tare da shi musu albarka da fatan taso wa cikin addinin Musulunci, godiya me ƙo sai tayi mai ya musu sallama ya wuce,
Jikin AHYAN yaƙi daɗi da zarar AYANA tayi kuka shima yayi shi daga ƙar she sai yazo mai da zazzabi duk da cewa suna kula da yaran sosai amma AYANA ta cika rigi ma ,
haƙori kawai suka cigaba da yi har zuwa ranar da suka kai kwana bakwai tun da likita ta basu umarnin dawo wa a duba lafiyar yaran a ranar,
Shirya wa sukai A'ishah da me ƙo sai sannan aka shirya AHYAN da AYANA cikin kayan sanyi da abokan arzikin me ƙo sai suka kawo musu ,
Duk da an ce ba suna amma haka akai ta tururuwar kawo wa yaran abun arziki, baƙa ramin goshi da farin jini sukai gurin mutane,
Koda suka je asibiti suka bada katin su cewa akai su ɗan jira ba wani lokaci, kafin daga baya wata nurse ta zo ta shiga da su office ɗin doctor,
Sai dai ba yadda sukai tsammanin bane ba doctor da ta amshi haihuwar A'ishah bane wani doctor ne daban namiji , basu umarnin zama yayi , ya buɗe file ɗin su yana duba wa, sannan ya ɗago kan shi ya fara musu tambayoyi,
Akan ko yaran suna fuskantar wata matsala, A'ishah ta bashi amsa da namijin ne ke fama da zazzabi mai zafi tun ranar da aka haife su da zarar yayi kuka,
Amsar AHYAN doctor yayi yana duba bugun zuciya da sauran abubuwa, bayan ya gama ya mai da shi, yayi wasu ƴan rubuce rubuce cikin wata ƴar takar da ya basu yace ga wannan takarda ko kai daƙin gwaje-gwaje na asibiti koyar wa na Aminu Kano a mai wa'in nan tests ɗin ,
in anyi sai ku dawo min da sakamakon, amsa sukai suka tashi suka fita, sai da suka koma gida da kyar suka haɗa dubu biyar, kafin suka wuce asibitin,
Sun kai kusan yamma kafin aka gama aka basu sakamakon gwajin suka dawo gida,
washe gari ma suka sake sanma ƙon koma wa asibitin dan kai sakamakon gwaji, bin layi sukai har aka kai kan su , suka shiga doctor ya amsa ya duba,
Bayan ya gama yace Hajiya sai dai kuyi haƙori yaran yana ɗauke da ciwon zuciya , wani hawaye ne mai ɗumi ya sakkowa A'ishah a saman fuskanta , me ƙo sai kuma sa saki salati ,
Doctor ya cigaba da cewa kuyi ha ƙori kun san kowa da irin tasa kaddara shi kuma tasa kenan amma komai zai zo da sau ƙi har dai kuka kiyaye, A'ishah ta ce cikin kuka yanzu doctor ya za mu yi,
Doctor ya ce zan rubuta muku wasu magungunan in Sha Allah zasu temaka kamai gurin hana tashin ciwon da kashi saba'in na daga cikin yuwu war ta shin, kashi talatin kuma wannan da kan ku za kuyi ,
ku tabbatar baya kukan da zai zarce ƙa gida da gujin baccin ran shi , inshallah a cikin magungunan da zan rubuta muku har da zazzabin da kuka ce yana damun shi,
San nan ki rinƙa cin abinci mai gina jiki, kuma da wata matsala ta samu a rinƙa hanzarin wuce wa da shi asibiti dan shawo kan matsalar tun da wuri,
Rubuta musu maganin yayi ya basu , cikin sanyi jiki suka wuce,
Ba anan tashin hankalin yake ba , sai da suka je pharmacy aka gaya musu kuɗin magani dubu ɗari, anan al'amarin ya ƙara lala cewa,
Daga me ƙo sai har A'ishahn dukan su dubu biyu ne riƙe a hannunsu, a wannan lokaci A'ishah ta kasa riƙe kukan ta ,
kuka ta fara bilhakƙi da gaskiya, ita ma me ƙo sai share hawaye kawai take da gefen zanin ta, a haka dai suka lallaɓa suka koma gida,
A wannan lokacin ko abin hawa basu hau ba dan ba ta jin daɗi suke ba , dan ma Allah yasa an rufe yaran da manyan hijabai , su basu ma san wainar da ake suya wa ba, sai baccin su suke sha,
Suna kai wa gida A'ishah ta kwantar da AHYAN da yake bayan ta tashi ga shiga da fito da kayayyakin sawar ta, ita ma me ƙo sai haka tayi ta kwantar da AYANA tana fito da ƴan tsofaffin ...........
***********
Nasan kun ƙosa kuji ko ya lion yake Ni nasan abin da nake , ku ƙara haƙori very soon zai baiya na....
Na gaji da ro ƙungiyar ayi like da comment da ga yanzu hakkin na wato hakkin fansar littafin nan shine vote and comment wan da ya ƙaran ta bai yiba shi da Allah
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...