part 13

244 19 1
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 61-65

Cikin ta, tunanin ma fita ta rinƙa yi kala kala amma har yanzu ta kasa samo wata hanya,

Tana a wannan yanayin ne mama ta shigo cikin ɗakin, amma duk da haka bata san da shigo War mama ba tunanin ta yayi nisa

Mama bayan ta dawo daga maƙota, ganin ƙofar ɗakin su A'ishah a buɗe yasa ta fara kiran sunan ta , jin shiru yasa ta nufi ɗakin da sallama a bakin ta ta shiga amma hakan bai sa A'ishah ta ji taba,

Gashi dai idanuwan ta a buɗe tana kallon sama ballantana a ce bacci take,

Tsoro mama taji ta taɓa tana cewa A'ishah lafiya, a firgice Aishah ta tashi ta zauna ganin mama yasa tace au mama kin dawo,

Mama ajiyayyar zuciya tayi gani abin da ya zo mata zuciya, rayuwa ta ƙaryata haka,

Amsa mama ta bawa A'ishah da , gani kuma kina gani na ke zan tambaya da har kin dawo, mai ya dawo dake haka yau da wuri,

Sun kuyar da kanta A'ishah ƙasa tayi tana tunanin kallar amsar da zata bawa mama , tun da dai kowa yasan ƙarya ba ɗabi'ar ta ɓace,

Mama zuba wa A'ishah ido tayi yana karanta yanayin ta, kana ta ce kefa nake jira baki bani amsa ba,

A'ishah cewa tayi imm mama bana jin daɗi shiyisa na dawo ganin cewa ko na zauna ba wani abun zan fahimta ba,

Mama tun fara magana A'ishah ta gane cewa ƙarya take , cewa tayi hmm duk sanda kika shirya magana kya zo ki same ni, tashi tayi kana ta ce ki je ki zuba abin ci kici, kisha magani , ƙana ta fita,

Ko da nafisah ta dawo gida mama ta titsiye ta sai ta gaya mata mai ya faru , nafi ta sake mata ƙarya bata da lafiya ne shiyisa ta dawo gida, mama badan ta yarda ba ta kyale su tace in Tai tsami taji,.

★*****★

Yau sati ɗaya kenan da faruwar wannan lamari, gaba ɗaya movement ɗin A'ishah ya canza ba kamar da ba ko makaranta ta dena zuwa a cikin wannan rana kun da sunan bata da lafiya,

Duk yadda taso ta cire lion a cikin zuciyar ta abin ya ci tura ta rasa wani irin tunani zata yi ta rasa gurin wa zata je ya bata shawara a wannan lokacin,

Wata rana da Nuhu ya aiko a kira ta, bayan ta fita ce mai tayi ya ɗan rabu da ita na wani lokaci ,

Nuhu yayi mamakin sau yawar A'ishah a cikin lokaci ƙalilan, amma besan dalilin ta ba da nufin ta, dole yayi yacce ta ke so, in ya samu akai auren duk abin da zai biyu baya ma saiya faru

****
Lion ba irin kira a waya da message da bai wa A'ishah ba amma bata ɗauka ko da yaushe yana ƙofar gida yaga ta inda zata fito amma bata fito wa , ya rasa dalilin ta nayin hakan

Koma hukunci take mai akan wani laifi nashi yaci ace kawo iyan zu ya hukuntu iya hukuntuwa, tabbas ya hukuntu da tun bayan sun batar da ya mata ya shiga cikin wani hali na buƙa tuwa da ita,

duk yan mata shi ya kira su ko zai samu relief akan abin da yake ji amma abin yaci tura A'ishah kawai yake gani a matsayin mace, ko hannun su baya iya riƙe wa,
zaman ƙofar gida ya zamar mai jiki,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now