part 11

258 16 0
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 51-55

Illa soyayyar lion da tai miki mugun kamu , wacce kika kasa gane wa, saboda baki taɓa faɗa wa cikin irin wannan yanayin ba, shiyisa baki fahimci me ke faruwa da ke ba ina nufi abin da zuciyar ki ke so,

kina ƙaryata ta da zarar ta gaya abin da take so, kina ƙaryata gaskiya duk da cewa a baiyana take ɓaro-ɓaro yarda da ita ne kawai kika kasa yi shine kawai,

A zabure A'ishah ta miƙe, tace subhanallah nafisah, kin san kuskuren da bakin ki ke furta wa kuwa shin mai zai kaiki yin wannan tunanin, mai yisa kika kasa yarda da hukuncin da baba ya yanke akan mu,

Ina Ni ina son wani Aliyu, kar ki manta dukan mu da baiko akan mu, kin san dai tuntuni Nuhu nake so, shi baba ya zaɓa min , zan yi biyayya da hakan a ko wani hali na tsinci kaina, kafin nasan Aliyu Nuhu na fara sani shi na koya wa zuciya ta da zan zauna da shi a nan gaba,

Nafi tashi tayi, itama, tace zaɓin baba bana kiba ne kamar yadda baba yake da zaɓin shi kema kina da naki nima ina da nawa,

shi baba abin da yake yana ganin daidai ne a gurin kowa , kowa yana da abin da zuciyar shi take da muraɗi, mu yanzu ba yara bane, ke kanki kin san gaskiyar cewa ba son Nuhu kike ba, biyayya kike yi, amma zan kyale ki a yanzu, nasan da sannu zaki fahimci abin da nake, nufi,

zaki iya zuwa ki bawa malam Abdullahi haƙori tun kafin ya bar makarantar, nafisah na gayar hakan ta bar gurin,

A'ishah dan tsayawa a gurin tayi jim tana tunanin maganganun nafisah, daga baya ta share zan cen ta nufi ofishin malam Abdullahi , malamin da ya kore ta a class,

Da isar ta bakin ofishin tayi sallama ya bata izinin shiga, ta shiga, gaishe shi tayi ya amsa, sai ta tsaya jim ta rasa ta ina zata haɗo kal momin ta saka a bakin ta,

Bakin ta na rawa tace, ka kayi ha ƙorii malam ba da gangan nayi ba,

Kallo tsaf malam Abdullahi ya ƙare mata kafin ya jefa mata tambaya, yace soyayya ko,

Ita dai A'ishah bata ce komai ba sai sun kuyar da kanta da tayi ƙasa,

Malam Abdullahi dan guntun murmushi yayi, kana yace da ganin ki na gane soyayya ce ta miki mugun kamu, ina so kibi komai a sannu karki yanke wa kanki hukuncin da nan gaba zaki zo kina da na sani,

Nasan baza ki fahimci magana ta a yanzu ba sai nan gaba, amma kiyi komai akan abin da kike so,karki bari zuciyar ki ta rauna ta ko yaya ne, kar ki bawa zuciyar ki damar da ta yar da cewa zaki iya mutuwa akan so,

Ki gane cewa muna yin soyayya dumin mu rayu ne ba dan mu mutu ba, ina miki fatan alheri a rayuwar ki ta nan gaba , zaki iya tafiya,

A'ishah cewa tayi nagode malam kafin ta fita a office ɗin sum sum, tana cikin tafiya zata koma lecture hall ɗin su , ta ci karo da nafisah,

Nafisah cewa tayi, yauwa dama ke nake nema, jakar ki na gurin sahura, malamin da zai mana lecture ba zai zo ba so zan je gidan su wata ƙawata in kin gama lecture kawai ki wuce gida ba sai kin jira niba,

A'ishah cewa tayi yau zaki zo gida ne , nafisah cewa tayi balallai ba gaskiya, sallama sukai nafisah ta wuce, A'ishah ta ƙara sa lecture hall ta zauna kusa da sahura,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now