✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨✨بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Page 29Not edited
" Boka kakan sheɗanu , boka na dotse mai gani har han ji, ya uban mu maganin kukan mai share mana hawaye yauma gamu mun kawo ƙorafi."Duk wannan kirarin shukura ce keyi, a cikin tsakiyar wani ƙasur gumin daji wanda ba gida gaba ba gida baya.
"Tun asubar fari shukura ta tashi latifa su tafi gurin boka dumin cikar burin su, sun yi tafiya me nisa a mota kafin suka daka ta a gaban wani daji, suka ñau sa ciki suna ta tafiya har wajen ƙarfe sha biyu na rana kafin suka kawo tsakiyar dajin.
"Suka tsaya a tsakiyar filin Allah, latifa duk ta tsorata da lamarin ta riƙe mayafin shukura gam , kamar jira take kace kulle ta an tara na kare.
"Amma shukura ko , ko a jikin ta da alama ma ita ta saba dan yadda ta tsaya tana ta zuba uban kirari ba tsoro ko far gabar komai a fuskar ta ko cikin zuciyar ta.
" Can shukura nata kirari sai gari ya haɗe yayi baƙiƙ ƙirin gurin yayi duhu kamar tsakiyar dare, wata iska haɗe da guguwa ta taso, tana nan na ɗe a guri ɗaya,
"Sai ga wata tsohuwar bukka ta bai yana a gaban su, nan take duhun da dajin yayi ya washe komai ya dawo dai-dai.
"Wani ihu ne kuma ya taso mai ban tsoro ya fara fito wa daga cikin bukkar gaba ɗaya ya mamaye dajin.
" Fitsarin da latifa ke riƙe wa tun tuni ne ya zubo mata a wando wani mukin tsoro ya kama ta, ta ƙara ƙan ƙame shukura.
"San da a ka fara fito wa da ita kafin jikin wani ramenmen tsoho ya fito daga cikin bukkar ya na dogara san da,
kallon shi ma kawai abin tsoro ne , jikin shi duk gashi kamar biri, tare da wani zaƙo-zaƙon farce kamar na mai cin naman mutum.
" Duk ta ku ɗaya da zai yi sai kin ji wani gurnani na namun dawo mai ban tsoro wanda baza ka iya tan-tan ce ko na wace dabba bace.
Cikin Muryar mai amo da ban tsoro yace ya ke kafira la anan niyar baiwa,
Barka da zama ɗaya daga cikin man yan she ɗanun duniyar nan . Dama an sanar dani zuwan ki, jiran isowar ki kawai nake yi, ina mai miki bishara
Daga yanzu duk abin da kike so a cikin duniyar nan zai zama mallakin ki, ki kasan ce mai yiwa babban sheɗan biyayya ko ki ƙarbi mommunan hukunci .
Sannan ki sani kin shigo ƙungiyar kenan kuma ba'a fita duk wanda yayi yunkurin yin haka mafi munin mutuwa zai fuskanta a ƙarshe,
Zazzaro ido waje latifa ta fara yi, tana cewa ƙungiya kuma a'a bana so , Ni bana so.
Kun gama tafiya ta , juya wa latifa tayi ta fira tafiya, tayi taku ɗaya biyu, babban boka ya ɗaka mata wata uwar tsawa , da sai da dajin ya girgiza, yace ke ɓatacci ya daga ta anan.
Tuni cikin latifa ya ɗuri ruwa zawo ya fara kama ta, boka nuni yayi da latifa da san dar shi sai ga latifa ta bai yana a gaban shi tana rawar ɗari kuka ma yaƙi zuwa mata a wannan lokacin sai gumi take.
Tafin hannun shi ya ɓuɗe ya fara wani karatun sulkulle da tsafi ku Ni kai na ban fahimci mai yake cewa ba,
Yana cewa Makkkkar Makkkkar zumgum-zumgum sai ga wata ƙwarya ta baiyana a tafin hannun shi ,
ruwan cikin ta ɓaƙiƙƙifin mai fitar da wani mugun wari tare da hanani,sannan yana ta fasa ga wasu abubuwa suna yawo a ciki kamar tsutsutsi kamar maciji wasu dai halittu ne a cikin ruwan.
Boka cewa latifa yayi ungo Kisha , latifa ansa tayi hannun ta na karkar wa gashi tashi daya taji baza ta iya wa boka musu ba, zuciyar ta ta mata nauyi,
Ƙurɓa tayi ta cire ƙwarya a baki tana ɓata fuska kamar ta kwara amai haka take ji amma dole ta ɗaure,
Wata shegiyar dariya boka yayi mai ban tsoro yayi wa kan shi kirari, kafin yace kuje she ɗanu la anan nu, sannan ke sabuwar sheɗaniya ki sani aiki ki na farko,
zaki bari sai nan da wata uku zaki je ki nemi yaron , ƙarki sake ku sake magana ko haɗuwa har sai nan da wata uku, daga nan duk abin da kika so shi zai faru .
Nuna shukura yayi yace ke kuma ki tabbatar kin ku ya mata duk wani aiki da ɗan gun giya yake yi, sannan tabi duk wani shara ɗi , saboda haka ku ɓace min ɗa gani.
Jan hannun latifa shukura tayi suka fara gudu, gudu suke tayi ba juya wa basu suka kai bakin jejin nan ba har sai gaban nin magriba.
Gurin da suka faka mota suka ƙara sa a gala bai ce , suka shiga suka bar gurin har suka kusa kai gidan shukura ba mai ce da wanin shi uffan .
Shukura nayi fakin a ƙofar gidan ta, latifa ta buɗe ƙofa ta fita ta shiga cikin gidan da gudu, toilet ta shiga da guda ta fara zawo zoo-zoo zurororo haka kake ji , can sai ta fara yin ƙurin amai tai ta yi amma abin da ta sha yaƙi fita.
Brush ta fara yi sai da ta ƙarar da month clean guda kafin ta haƙora ba dan taso ba,
Duk ta jiga ta , da kyar taja jikin ta ta fito a cikin bayin, shukura ta samu a falo ta ba je a ƙasa tana cin abin ci, dariya ta fara tana cewa ƙawa ta kin ga yacce kika dawo kuwa,
Haba kar ki bani kun ya mana, ke kika ce zaki iya komai , shine Ni kuma na kai ki inda za Amin maganin matsalolin ki na yan zu da kuma na nan gaba.
Latifa bata ce komai ba ta zabga mata uwar harara tayi shige War ta cikin ɗaki ta ƙwanta ba tare da taci komai ba.
Ɗakyar bacci ya ɗauke ta mai cike da munanan ma farkai.
Ta ɓangaren lion ko waye War garin ne ta kama ranar.....
Sorry for the short page
Yau nayi busy
Anyway kuyi manage.
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...