Page 59
Not editing.
"Wajen wata biyu kenan da , dawowar lion gida Nigeria, ya fara ai yukan shi cikin Sa'a da nasara a asibitin da daddy da ya gina mai tun shekarun baya da ya gama karatunsa,Sai dai abu ɗaya da yake damun sa shine tunanin A'ishah da yake ci mishi rai, gashi daddy ya fara damun shi akan ya fito da mata yayi aure , dan duk sa'an nin shi sun dade da ake iyali, a yadda yake cewa kenan
Saboda damuwa da ta mai yawa , zama yake a asibiti baya dawo wa gida, sai dai ya dawo yayi wanka ya shirya sannan ya koma, yau ma bayan sallah isha'i yana zaune a cikin office ɗin shi yayi nisa cikin dogon tunani,
Wayar shi da ta fara ringing ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin, sa hannun shi yayi ya ɗauka sunan daddy ya gani sai yayi picking call ɗin ya kara wayar a kunne shi , tare da yin sallama ya gai sar da daddy ,
Daddy bai amsa ba, ya tambaye shi da ina yake , ya bashi amsa da yana asibiti, daddy yace kayi maza kazo gida ka same ni ina jiran ka yanzun nan, sannan ya kashe wayar,
Lion sauke nunfashi yayi, sannan ya tashi ya cire farar rigar likitoci dake cikin shi , ya dauƙi key ɗin motar shi ya fita ya bar Asibitin, zuwa gida,
A falo ya samu daddy a zaune yana zaman jiran shi, zama yayi ya fara gai da shi , nan ma daddy bai amsa ba, yace Aliyu Aliyu so uku, sannan yace so nawa na kira sunan ka lion yace so uku daddy,
Daddy ya ce to abokin wasan ka ka mai dani kenan ko , wato kan nace ka fito da mata kayi aure shine muka fara wasan buƴa da kai ko, ko bari baka yi mu haɗu saboda baka son a tada maganar,
Cikin sanyin murya daddy ya cigaba da cewa haba my son, in ma baka da wacce kake so ne , ba sai ka min magana ba na samo ma ko da cikin yaran abo kai nane ai ba a rasa ba,
Yau wa gama wannan yarinyar rukayya ɗiyar amini na , yarinya mai kunya da tarbiyya tana matuƙar son ka,
Shiru lion yayi
To ko dai baka da lafiya ne , da sauri lion ya ce a'a ba haka bane daddy , daddy yace to menene gaya min kuma gaskiya kawai nake son hi a wannan lokacin,
Me makon daddy yaga lion ya fara magana, sai ya ga ma ya tafi duniyar tunani da ban, kiran sunan shi yayi amma lion bai jiba, har sai da ya taɓa shi kafin ya dawo cikin hankalinsa,
Dafa ƙafa ɗar sa daddy yayi, sannan yace my son ka faɗa min na maka alƙawarin koda ban maka maganin matsalar kaba zan nemo ma mafita,
Kayi haƙori ka Gaya min, a duniyar nan bamu da kowa daga Allah sai kan mu, lion cewa yayi shike nan daddy zan gaya ma amma ina so ka fahimce duk abin da na aika ta wallahi yanzu nayi na damar aika ta shi,
Daddy yace na yar da , da kai gaya min ko menene ke damun ka, labarin A'ishah lion ya fara bawa daddy ɗaga haɗuwar su , zuwa ƙuɗirin shi akan ta ,
zuwa auren sirri da sukai har lokacin da iyayen ta suka gano da mutanen unguwa , sannan a lokacin ya tafi ya bar ta lokacin da tafi ɓuƙatar sa,
Sannan ya cigaba da cewa haƙiƙa A'ishah mai sona ce , ta ƙi bin umarnin iyayen ta duk dan Ni , tayi komai duk dan ta tabbatar da cewa tana SONA,
wallahi daddy nima ina son ta fiye da komai , in ban same taba , zuciya ta tana gaf da tar watse wa na mutu , dan in na rayu, rayuwa ta zata zama mara amfani,
Daddy nunfashi ya sauƙe sannan ya furta innalillahi wa'in na ilaihir rahu'un,
Lallai ba laifin ka bane kai ka ɗai har da nawa, kuma na ɗauki alƙawarin gyara lefin da Ni da kai da muƙa yi wa rayuwar ka,
Yanzu ka tashi kaje ka kwanta ka huta inshallah Allah koɓe zamu ɗauki hanyar Zariya, tashi lion yayi yawa daddy godiya da sai da safe kafin ya wuce shashin shi,
Ko da yayi shirin bacci, bacci bai zo mai ba sai tunani yake yadda za ta kasance goben, daga baya dai dakyar bacci ɓarawo ya sace shi cike da mafarkai,
Washe gari , daddy sawa yayi aka shirya musu tafiya zuwa Zariya a mota, da misalin ƙarfe goma na safiyar ranar, gwanan motocin da ke tsare lafiyar shugaban kasa, suka ɗau han ya dumin yiwa , daddy da lion rakiya zuwa Zariya..
Tafiya awanni uku ciff ya kawo su, kasan cewa ko ina suka zo wuce wa matsa wa ake basu guri su wuce,
Har suka kawo unguwar, motocin suka yi fakin a ƙoƙarin gidan malam Mani da gidan ya tsufa har wani sashi na jikin gidan ya zuba,
Unguwar gaba ɗaya ta ɗau ka , shugaban ƙasa guda ya zo, mutane sun taro ana ta leƙe mata da maza da yara
Malam Mani ne ya fito daga cikin gidan jin anyi sallama, alamun tsufa gaba ɗaya sun nuna a tattare da shi,
Mamaki ne ya cika shi ganin irin manya man yan motocin da ke tsaye a fake a ƙofar gidan shi ga mutane sun cika ƙofar gidan
Wani mutumi ne cikin shiga ta kaki , yaba shi hannu suka gai sa , kafin yace dan Allah ina neman malam Mani,
Malam yace to yaro ai nine ince dai lafiya, mutumin cewa yayi lafiya dama me girma shugaban ƙasa ke su kuyi magana in baza ka damu ba,
Malam gaban shi ne ya faɗi yace subhanallah ba dai wani lefi nayi ba dai ko, mutumin cewa yayi inshallah Allah ba laifin da kayi kai dai shiga Mota muje in da ya fi kamata ace kun yi magana,
Malam yace to bisimillah yaro , ɗaya daga cikin motocin aka buɗe wa malam ya shiga, kafin motocin suka sake ja zuwa , tsohon gidan su lion dake unguwar, in da ko bayan barin su gidan ba a fasa gyara shi ba,
Ƙaton falo aka shigar da malam in da lion da daddy suke sau ne cikin shiga ta alfarma,
*******
Please comment and vote

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romantik* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...