page 35

241 9 3
                                    

Page 35

Not edited

"Taji kamar za'a shigo cikin ɗakin , da sauri haɗe da gudu ta haye kan gado ta ƙudun ɗune, kamar wata mai bacci.

"Nafisa ce ta shigo cikin ɗakin, sheƙe wa tayi da dariya, ganin yadda Aishah ta ƙudun ɗune kamar wata mai bacci da gaske.

Cikin dariya nafisa tace gwamma ma ki tashi yarinya dan nasan ba bacci kike ba,

"Buɗe idon ta ɗaya Aishah tayi, nafisa ta cigaba da cewa, wato ku yan soyayya ko, dama abin da kuke kenan,

"Zuruf Aishah tayi ta miƙe tana haɗa hannun ta guda biyu, alamar roƙo, tana cewa dan Allah kishi shiru kada ya mardiya ta ji,

Dariya nafi ta sheƙe da ita ta zauna a gefen gaɗon tana cewa, san da kuke tsotse bakin juna da shan muyun juna ai baki ji tsoron wani ya gan ku ba,

A'ishah ta ce wallahi kuskure ne , bazan sake ba, dan Allah kada ki gaya wa kowa, tana cewa haka tana yin narai-narai da ido kamar zatai kuka.

Nafisa tace kwantar da hankalin ki ba me ji, sai dai ki kula ya tsaya iya kiss ɗin kar da ku wuce gona da iri, dai , kuma ki kiyaye in da ba Ni na Gan ku ba fa, me zaki ce wa su malam,

"A'ishah cikin zuciyar ta, tace wai ya tsaya iya kiss ai aikin gama ya riga da ya gama, a fili kuma tayi yaƙe tace inshallah Allah hakan baza ta sake faru ba,

Nafisa tace amma dama rayuwa sai da ɗan romancing kin gane ai , Ni ba wannan ba yanzu dai wani school ki ka zaɓa zaki je tp ,

A'ishah bata amsa da , taahaah academy, nafisa ta ce wato saboda ku rinƙa haɗuwa da lion ko oh oh kaji ƴan soyayya.

A'ishah tayi murmushi tace ashe kin gane , ke fa wani school zaki je, nafisa tace nan school ɗin dake nan unguwar, saboda in rinƙa haɗuwa da my love, Yaya Sa'a na hanani fita taɗi , wai bazan ja mata magana gurin malam ba,

Shiyisa na dawo nan, wai duk saboda zaɓin da malam ya mana, da Ni kadai naƙi amma yanzu gashi kema kin dawo kan hanya.

*********

Washe gari haka lion yazo ya ɗauke su ya kai su makaranta, haka kowan ne daga cikin dalibi ya zaɓi makarantar da yake son zuwa, a cikin satin aka gama komai da komai,

Ranar Monday kowa yaje makarantar da ya zaɓa ya fara zuwa,

Lion da kan shi ya kai Aishah makarantar, kai tsaye office ɗin principal suka wuce , da shigar su office ɗin principal ya tashi jikin shi har yana rawa, yana gai she da lion kamar zai duƙa,

Ya nuna musu gurin zama suka zauna, lion ya gaya mai abin da ya kawo su , tare da kafa mai kashe ɗin,

Principal cikin tsatstsamar Hausar sa, insha allah baje shami masala bahh,

Sai da aka nuna wa Aishah ajin da zata ɗauka primary five b, ta gabatar da kan ta kafin suka wuce,

Gidan su lion suka koma, suka shiga raƙa shewa abin su,

*******

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gurin Aishah da lion, yanzu kusan wata biyu da rabi kenan da fara teaching practice ɗin su saura two weeks su gama

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now