✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨✨بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Page 28
Not edited
"Wallahi duk rana da ka ƙara kawo min magana me kama da haka sai na zubar ma da haƙora ra.
" Murtala ya tashi yana cewa a'a me yai zafi ai bata kai ga haka ba,
daga faɗar abin da naga Ni da ido na,dama nasan ba lallai ka yar da ba amma ko mu juma ko mu daɗe kai ma zaka gani da idon ka, fita daga ɗakin yayi.
"Nuhu ya koma ya zau na cike da jin hau shin Murtala ya cigaba da rubutun shi.
" Can ɓangaren A'ishah, bayan ta koma gida a tsakar gida ta samu yaya mardiya tana tsintar shin kafa.
" Sallama tayi ta shiga, ta zauna kusa da yaya mardiya tana cewa wash na gaji, yah mardiya sannu da gida.
" Yaya mardiya bata amsa mata ba, ta jefo mata tambaya, daga ina kike?
" Ɗan sosa kan ta Aishah tayi ta ce daga gidan su sahura , ba tare da taji shakku ko tsoron ƙaryar da ta yi ba.
" Har cikin zuciyar yaya mardiya ta yadda da Aishah, ta ce oh kin kyauta ziyara akwai daɗi, ya suke fatan suna lafiya.
"A'ishah ta ce wallahi lafiya suke maman su ma tace a gani she ki.
" Yaya mardiya tace aiya aiko ina amsa wa.
" A'ishah tashi tayi ta kai hijabi da nikab ɗin ta ɗaki ta fito ta fara taya yaya mardiya aiki nan da nan suka gama.
" Lion ko bayan ya raka A'ishah gida ya dawo, suka ƙeɓe shida farhan da kisser da wani daga cikin abokan da ake kiran shi da ɗan malam.
" shirya yadda za a ɗaura auren sukai ba tare da sanin kowa ba, akan farhan shine zai zama waliyin A'ishah, kisser waliyin lion , Dan malam shine wanda zai ɗaura aure.
" Kuma hakan zai faru ne nan da kwana ki biyu masu zuwa tun da gobe ne in Allah ya kai mu dadyn lion zasu koma Abuja shi da Hajiya asabe.
" washe garin ranar kuma sai a ɗaura aure, Haka suka cigaba da tsare tsaren su har a ka kira sallar magrib suka je suka .
" Bayan sallah isha'i lion ya ɗau wan ka , ya nufi gurin A'ishah.
Da zuwan shi ƙofar gidan ya ɗauki wayar shi ya kira A'ishah,
A'ishah dama tuni tayi wanka ta shirya zuwan lion kawai take jira, aiko sai ga kiran shi , ta ɗau ka yace ta same shi a waje yana jiran ta,
" Tashi tayi ta ɗau ko hijabin ta da yasha guga ta fe she shi da turare , ta saka ta fito ta cewa yaya mardiya bari ta je Nuhu na kiran ta.
Yaya mardiya ta mata a dawo lafiya, A'ishah ta fita da wata irin ta fiya mai jan hankali, ta ƙarasa gaban lion.
" Cikin siririyar muryar ta , da ta ƙara siran ta-ta, tace Amin cin allah su tabbata a gare ka yayah na Ni ka ɗai .

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...