page 75

384 7 5
                                        

Page 75

" An sallami lion ɗaga asibiti saboda ba wani rauni bane mai tsanani a jikin shi, kawai ƴar gajiya ce da rashin ishesh-shen abin ci da ruwa, hurumin kawai yake da buƙata bayan ƴan kwanaki kaɗan zai dawo.

Tun da A'ishah ta bar asibitin bata sake bari ta hadu da lion ko Ahmed ba , saboda tsabagin kunya,

Bayan lion ya dawo ba yanda yaya Sa'a da nafisa basu yi ba dumin A'ishah taje ta duba lion Amma taƙi zuwa,

Da yamma washe garin ranar da aka sallami lion , nafisa ce ta shigo cikin sashin da aka sauke su ita da su ayaan da ayana,

Suka iske A'ishah zaune tana kallo a falo, ita da aunty sa'a, zama tayi , tace kinanan kina kallon asarar wata kilaki nacan na tarai rayar mijin ki,

A dai cigaba da zaman kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, A'ishah a firgice ta miƙe tana dafe ƙirjin ta , har da salati ,tace wa nafisa me kika ce,

Nafisa ta bata amsa da abin da kika ji, ruky nacan a mazaunin ki na jinyar mijin ki ke kina nan shiriri ta,.

A'ishah bata tsaya gama saura ran nafi ba taja Maya fin dake saman kan nafi ta yafa a saman doguwar rigar da ke jikin ta, sannan,

ta fita da sauri daga cikin part din har tana tun taɓe , amma bata tsaya duba wa ba,

Aunty sa'a ce ta tafa hannu ta tana cewa oh Allah, ke nafisa ai sai kisa zuciyar ta buga, nafi tace kyale shasha sha ina sane na gayar mata haka, yarinya sai bala'in taurin kai , da rashin ya fiya,

In ba a yafiya mu muka yafe mata, amma tana nema , tayi wasa da damar ta , Ni a ce ina da mijin mana a ga yadda zan tarai raya ɗan abin na,

Ga shegen feelings da ke nema ya kashe Mutun , daga sama nafisa taji ance , ai shiyisa nace zan bawa malam ɗari biyu kawai ya ɗaura mana aure muna mu shiga daga ciki,

Tun da nafisa ta fara zuba bi ashe Ahmed ya shigo ya tsaya duk yana sauraren surutun da take zuba wa,

Nafisa ɗago wa tayi ta zabga mai wata uwar harara sannan tace tabɗi jam sai kace wata wadda ta raƙo mata to akai kasu sannan tayi sauri ta tashi ta shiga cikin ɗaki,

A zahiri kuwa baƙaramin kunya ɓace ta Kama ta , a bai yana kuma tace ai da da gaske kake ko gobe ma baza a kai ba sai an ɗauka , rufe baƙin tayi da tafin hannun ta kada wani yaji ta,

A'ishah ko, tan fita ta samu wani guide ya raka ta ɓangaren lion, da sauri ta buɗe kofar shiga ta shiga ciki,

Dai dai ruky na ƙoƙarin kai wa lion kofin lemo bakin shi dumin yasha , da gudun tsiya A'ishah ta ƙara sa gaban su taja birƙi, sannan ta kai hannun ta , ta han kaɗan kofin ,

Tuni ya faɗi a ƙasa ya tarwatse, a furgice ruky ta miƙe dan bata san da shigo War A'ishah ba, ganin wanda ya hana kaɗe kufin , yasa tace kan uban can ,

Shaƙo wuyan rigar A'ishah ta yi , A'ishah ta fiske ta ture ta , tana cewa dalla can sake ni Malama, ruky sake tun karo A'ishah tayi tana cewa Wallahi yau sai naga uban da ya tsaya miki a cikin gidan na,

Lion shiga tsakaninsu yayi yana cewa wai ku kuwa me yake damun kune, A'ishah ce cikin tsiwa ka tan baya dai kila akwai abin da ke damun tane,

Ruky tace honey ka matsa kawai dan wallahi yau sai na koya yariyar nan hankali,

Kwalbar campaign A'ishah ta ɗauka ta fasa sannan ta nuna wa ruky tace wallahi in baki bar gurin nan ba yau sai na nuna miki kaɗan daga cikin rashin hankali ba,

Lion ce yayi cikin ɓacin rai A'ishah meye kike yi haka baki da hankali li ne, bani kwalbar nan, A'ishah tace eh bani da hankalin,

Lion ya saƙe cewa ki bani kwalbar nan nace miki, A'ishah ta ce ka fara cewa wannan abun ta fita sannan ta sake tunkaro ruky da kwalbar ruky ta ja da baya tana zazzare ido

Ashe tace wa ruky fita , ki fita daga gurin na gaya miki ai da sauri ruky taja jakar ta , ta antaya na kare , sai a sannan A'ishah ta sauke nunfashi sannan ta sauƙin kwalbar ta faɗi ƙasa,

Lion yace a faɗa ce baki da hankali ne ko kin ɗauka duk wan Nan abin wasa ne so kike ki cutar ita kenan,

Faɗa lion ya din ga mata , ita ko A'ishah kallon ƙasa tayi ta na zubar da hawaye, sai daga baya lion ya saurara , ya dage kan shi,

Ya jan yo Aisha ya rungume ta yana bubuga bayan ta, luf A'ishah tayi a saman ƙirjin shi, tana sauke nunfashi a hankali,

Lion ya fara magana kamar haka , na gaya miki ba wani abu dake tsakani na , da ruky bana son ta. Ke kadai zuciya ta take so,

Da gaske ne ruky tana so na amma Ni a matsayin ƙanwa na ɗauke ta , bayan haka ba komai, koma ba ta yacce za ai ruky tazo guri na in kure ta saboda alaƙar da ke tsakanin mahaifina da kuma mahaifin ta,

In na wulaƙan ta ta dady bazai ji dady ba, ki bari in bita a hankali har ta fahimci ba son ta cikin zuciya ta,, ba a saka so da ƙiyayya, kiyi hakuri ki rinka barin ta tana cin darajar so,

A'ishah tashi tayi tana share hawayen ta , tace cikin sanyi murya kayi hakori nima ban san mai yisa na aika ta haka ba, lion ɗan murmushi yayi sannan yaja kuma tun ta yace my cutie pie,

Zan yafe miki amma in nima Zaki yafe min , A'ishah haɗe fuska tayi ta ture hannun shi ta miƙe, da sauri ta koma ta zauna jin zafin da tayi a ƙafar ta,

Sai a sannan ta ankare da ciwon da taji a ƙafar ta har jini yayi , lion kamo ƙafar ta yayi ya daura saman cin yoyin shi dan taga mai ke faruwa,

Ganin ciwon da taji yasa, ya tashi yake ya ɗauko first aid kit Dan ya mata dressing ciwon,

Sake kamo ƙafar yayi ya w
Fara wanke ciwon yana cewa garin kishi har ciwo kika je kika jiwa kanki, ita dai A'ishah shiru tayi bata tan ka mai ba, har ya gama sa mata bandaji a ciwon,

Ya kwantar da ita saman ƙirjin shi ya kunna musu kallo, duka hankalin su ba akan kallon yake ba tunanin abubuwan daban daban suke,

A'ishah sai saƙe saƙe take cikin zuciyar ta, shin da gaske ne lion yayi la damar abin da ya aika ta mata , ko dai yana duk abubuwan nan ne ya sake yiwa zuciyar ta rauni,

Tsoro take kada ta yafe mai , ya sake kujar ta , shi kuma lion tunani yake na , dama su ɗore a haka, su dauwa a cikin yanayin da suke ciki a yan zu,

Har magriba tayi , suyi salla a tare, ƴan aiki ne suka kawo musu abinci suka ci,

Suna cikin cine ayaan da ayana suka shigo falon, A'ishah ta ce musu ba mace ku dena zuwa ko ina ba tare wani ba tare da ku, ayana ce ta ce a'a umma aunty nafisa ce ta kawo mu, da muka she mu muna so mu ji wajen Abban mu,

A'ishah ta ce Togo yayi, zama sukai suna cin abinci a tare, ya zamana A'ishah na bawa ayaan a baki , lion kuma na bawa ayana,

Bayan sallar isha i, A'ishah tace musu to su taso su wuce , ayaan ya haɗe rai yace , a'a ayaannn a gurin Abba zai kwana , A'ishah bata ja ba tace wa ayana to su su wuce ,

Ayaan ya kwalla wata uwar ƙara kamar wanda za a yanka shi, yace sai dai ita ma A'ishah da ayana su kwana a gurin Abba shi,

To fa daga nan , anan su A'ishah suka kwana dukan su saman royal bed ɗin lion , just like a happy family,

******

Ruky a fusace taja Motar ta , Allah ne kawai ya Kaita gida lafiya , tana ƙara sa wa ko fakin ɗin motar bata yiba dai dai, ta fito , ta shiga cikin part ɗin Mommy ta, tana shiga ta same ta a zaune,

Faɗa wa tayi jikin ta, ta fashe da kuka, momyn ruky ( na mance dasu sunan mamar ruky kuyi min tuni ) ruɗe wa tayi , tana tambayar me ya faru , amma ruky kuka kawai take ,

Momyn tace haba wa baby na , ke da kika fita gidan nan cikin farin ciki , yi shiru ki gaya min me ya ɓata ran ki har hawaye ke fito wa cikin wa'in nan kyawawan ida nuwan naki,

Ruky cikin shagwaɓa ta gaya wa Mommy ta duk abin da ya faru , ta ƙara da cewa Ni momy kawai kiwa Abba magana , azo ayi manar auren mu tare Aliyu,

Kuma in ma da auren shi akan waccen kuchakar ya rabu da ita, Mommy ruky tace yi shiru abin ki baby na duk yadda kike so haka za ayi bari alajin ya dawo , ruky ta rungume Mommy ta , tace yauwa Mommy shiyisa nake sonki da yawa

......

See you maybe Wednesday or Thursday...

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now