part 14

241 10 0
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 66-70

Lion Yana bin ta a baya, yana murmushi ko na meye oho , itama A'ishah haka murmushi take ta cikin nikaf,

sun kusa ka wowa gurin gidan su lion Aishah ta jiyo tace to ka dena bina a baya in na wuce sai ka tawo, ƙaya taccen murmushi lion ya sakar mata,

Kana yaja ya tsaya, har sai da A'ishah ta ɓace wa ganin sa, tana ta fiya kanta na kallon ƙasa,

Ihu abokanan lion suka sa suna cewa dan kwali yaja hula, tsaki lion yaja ya shiga cikin gida dan baya so su ɓata mai good mood ɗin da yake ciki,

Zama yayi a ƙan kujerar dake cikin falon shi yana murmushi shi kadai, yana tono fuskar A'ishah daga haka bacci ya kwashe shi a gurin,

★★★★★
A'ishah

Tun daga zauren gidan su ta cire nigaf ɗin ta, ta shiga cikin gidan fuskar ta cike da murmushi, bakin ta dauke da sallama,

Kallon mama tayi da take zaune a tsakar gidan ita da nafi suna fira tace mama sannu da gida,

Mama cike da mamakin sauya War A'ishahn na lokaci daya tayi , ta amsa da yauwa,

Ɗakin su A'ishah ta nufa nafi ta tashi ta bi bayan ta, mama cewa tayi Allah shi kyauta duk ma abin da kuke ɓoye wa zai fito fili,

tashi itama tayi ta shiga cikin ɗakin ta sanadiyyar ranar da ta Kunno Kai ta mamaye ko wacce ino wa ta gidan,

A'ishah bayan ta shiga cikin ɗaki cire hijabin ta tayi tana ninke wa, nafi tayi sallama ta shigo cikin ɗakin,

Kallon A'ishah tayi tace da alama yau wata samo maganin ciwon ta,

Aje hijab ɗin ta A'ishah tayi ta zauna a gefen katifar su, nafi itama zama tayi kusa da ita , tana cewa to bani labari nasha,

A'ishah kwashe komai duk abin da ya faru tayi ta bawa nafi labari.

Nafi cewa tayi ko kefa yanzu kika dawo kan daidai, A'ishah cewa tayi yanzu nafi Aliyu me yake nufi da yake kira na da my love kenan sona yake,

Nafi tsaki taja tace kema dai wallahi to in ba sonki yake ba ƙin ki yake, wa zai maka duk wannan,

A'ishah cewa tayi na shiga uku!!
Nafi tace kin shiga uku name?
A'ishah tace gaba nake ji kina ganin baba zai yarda da tarayyar mu da Aliyu ne,

Nafi cewa tayi wannan kuma sai dai in ke zaki bari ayi miki auren dole, ai yanzu an dena yayin auren haɗi ko na dole,

Baba ya kamata yanzu ya gane da, "da" da yanzu ba ɗaya bane,

Na godewa Allah yanzu mun dawo mu biyu daga cikin wa'in da basa son wanna haɗin , kin ga yanzu dole baba ya janye ƙudirin sa,

Jajir cewa zamu yi muga ya aura mana wanda zuciyar mu ke so, da haka suka cigaba da fita a tsakanin su,

******
Lion

Kiraye-kirayen sallar la'asar ne ya tada shi daga bacci daya kwashe shi a gurin kusan a wanni uku kenan,

Shi kanshi yayi mamakin kanshi irin awannin da ya kwashe yana sharar bacci, ganin cewa ya kwana biyu be samu bacci cikakken na minti talatin ba,

Kode ba abin mamaki bane ganin yau ya samu damar ganin abin da ya hana shi rintsa wa na kusan sati,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now