page 60

239 18 3
                                    

Page 60

Not editing.

*******
" Malam yun ƙurin zama yayi a ƙasa, daddy yace haba malam ya zaka zauna a ƙasa ai Ni na gai ya ce ka, ko bani na gaiyace ka ba kai ka kawo kan ka ai duk ɗaya muke gurin Allah ba wanda yafi wani,

Malam cewa yayi haka ne kafin ya zauna saman kujera suka gai sa dukan su,

Kafin Daddy ya fara magana kamar haka, wato ainihi malam abin da yasa na nemi da muyi magana cikin sirri shine

Haƙori muka zo baƙa da neman ya fiya akan lefin da muka aika tawa iyalan ka ashekarun da suka wuce,

Tiryan-tiryan daddy ya gaya wa malam duk abin da ya faru zuwa ga abin da ya faru da shi kan shi lion ɗin , da dalilan su na zuwa,

Hawaye ne ya fara zuba a idon malam tono da tsohon gyan bom da aka fama mai a yanzu,

Kafin malam ya fara magana, ɗan nan in nace ka kyauta min a cikin rayuwa ta nawa kaina ƙar ya,

Ta dalilin faruwar wannan lamarin ba irin abun ɓaƙin ciki da be faru da mu ba,

Na farko mutum cina da ƙima ta a idon duniya ya ɓace ko yaro ƙarami ba mai gani na da daraja, hatta sallah an dena bina ,

ɗalibai na sun tar watse , ba mai zuwa dumin ya nemi fatawa ko ilimi a gurina tun bayan faruwar wannan lamarin,

Ba ma shi ƙaɗai ba yara na biyu da ke da aure maza Jen su , sun sake su sun dawo gida dalilin me dalilin ka, na gidan ma sun rasa mijin aure,

Babban abu ɗaya na rasa ƴata mafi soyuwa a gare Ni , A'ishah mamana,

Lion kuka ya fashe da shi jin furu cin malam, daddare Kuma yayi salati ya sanar wa Ubangiji,

Sannan ya ce me ya faru da ita malam cikin tsoron abin da baya so ace malam ɗin ya furta,

Malam sauke ajiyar zuciya yayi, sannan ya ce bayan gano A'ishah tana ɗauke da juna biyu zuciya ta buga ban san halin da nake ciki ba,

Tsoron da firgicin abin da yake faruwa yasa A'ishah ta gudu ya bar gida tun ranar har zuwa yau bamu sake jin labarin taba , kullum tsomaye muke da daƙon jiran ganin ko zata dawo,

Duk da kun sanar dani ka aure ta, koda cikin da ke jikin ta ba dan halar bane zamu amshe shi mu bashi kulawar da ta da ce,

Amma naji daɗi da yarinya da auren ta ba shege bane a cikin ta fata na duk in da take Allah yasa tana hannu na gari,

sannan Allah ya dawo da tunanin ta zuwa gida , ko na samu na ƙara ga nin ta kafin na shaƙi nun fashi na , na ƙar she

Zuwa wannan lokacin lion ya zube a gaban malam yana kuka yana roƙan malam da ya yafe mai kuskuren shi, sannan yace ya mai alƙawarin nemo A'ishah a duk in da take a cikin faɗin duniyar nan,

Shi kan shi Daddy duk juriyar shi hawaye ne kawai ke zuba cikin idon shi,

Malam cewa yayi ba komai yaro , ko ba komai ka yi nadamar duk abin da ka aika ta , kuma ka goge min ko wani shakku da abin da nake jin tsoro cikin zuciya ta

Kaje na yafe ma Allah ya yafe mana gaba ɗaya sannan Allah ya baka nasara gurin ganin ka nemo ta,

Lion sa kan shi yayi a kan ƙafar malam yana kuka tare da yi mai godiya,

Shima daddy godiya yawa malam tare da sake neman yafiyar shi tare da sake yi mai alƙawarin neman A'ishah kamar yadda ya nemo ɗan shi cikin ƙasashen duniya,

Sannan ya ruƙe shi da su tashi daga wan can gidan su dawo wannan, sai da aka kai ruwa rana kafin malam ya yar da,

Ya kuma gida ya samu mama sasu Aunty sa'a ya faɗa musu duk abin da ke faruwa da yadda suka yi da shugaban kasa, wani sabon kuka ne ya tashi a gidan, jin wannan maganar, barin ma nafisa da tafi kowa saba wa da A'ishah,

Bayan an gama cin kuka kafin suka fara haɗa kayan su dumin koma wa sabon gidan su ,

Cikin gidan aka basu tan ƙameman part guda , yara sai murna suke,

Daddy yasa aka kawo musu kayan abinci da kuɗaɗen da ƙarin tufafi,.

Hatta ƴan unguwar sai da aka bi da kyaututtuka suma su sheɗa shugaban kasa guda yazo unguwar su,

Kafin Daddy da lion suka koma Abuja, ko da suka koma basu huta ba,

Suka fara shirin neman A'ishah duk da dai a ransu sun san baza ta wuce Nigeria ba, haka ko cikin garuruwan Nigeria aka fara neman ta birni da ƙauye,

Lion gaba ɗaya baya zama ya huta neman A'ishah kawai yake , barin ma ji yayi da cewa akwai jinin shi a tare da ita , burin shi kawai ace yau ya gan ta , ba zai ko sake bari tayi nesa da shi ba,

Ko asibiti baya zuwa yayi focusing akan abu guda ɗaya, daddy ma burin shi da addu'ar shi kawai Allah yasa a gan su ko ya samu rabon gana wa na jikan sa ku jikar sa

Haka dai suka ci-gaba da binciken dai,

*********

India,

Zaune take cikin ofishin ta da take ƙulla duk wata kitumurmura mugun ta, wani mutumi ya shigo cikin, bata ɗago da kan ta daga laptop ɗin dake gaban ta ba, tace yi magana ina jin ka ,

Magana ya fara kamar haka, ran ki shi daɗe, bin ciken da kika samu muyi a Nigeria akan lion, mun samu nasarar gano wa a yanzu haka yana can har ya fara aiki a wani asibiti da aka gina mishi,

Wani murmushin mugun ta latifa tayi sannan ta ce good, aiki mai kyau, abin da nake so yanzu ku cigaba da san ya mai ido, a bar shi yasha iska na wani lokaci ku dai ku tabbatar komai yake idon ku na kai,

Na ba da jimawa ba zan shigo Nigerian ,

Daga haka mutumin ya fice, wata muguwar dariya latifa tayi sannan ta ce very soon my rattee zaka dawo ƙangin ɓauta ta, a yanzu ka mure iskar duniya sake fashe tayi da wata muguwar dariyar,

Abin da zai hana ta tafiya Nigeria yanzu shine , nan da kwanaki order ta daga gurin king luxury zai iso tana iso wa zata raba wa dilolin da ta samu,

San nan sai ta sauka a Nigeria, da ma suna da mitin ɗin shekara na ƙungiyar su to zuwa Nigeria dole ne,

Ta shirya da ta gama zata ɗauke lion su koma wata ƙasar daban,

Wannan kenan...

••••••

Shin kuna ganin cewa lion zai samu nasarar gano inda A'ishah take?

Ko kuma kuna ganin cewa a karo na biyu latifa zata sake samun nasarar dauƙe lion ?

Ku dai ku biyu ni dan jin yadda zata kasance, tare da yi min vote ,comments and follow ɗin a.

A biya Ni gobe nayi update lol

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now