page 30

249 14 5
                                    

✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨✨

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"


Page 30

Not edited

"Yau ne ta kama ranar da su dady da Hajiya asabe zasu koma Abuja da zama gaba ɗaya.

    Lion ne da dadyn shi a taye a jikin mota, dady yana cewa son ka tabbatar kana kula min da kan ka please,

Sannan dan Allah kar ka bari inji an kawo min ƙara ka, na roƙe ka , ka kama kan ka, kafa girma yanzu,

Lion yace karka damu dad , ba abin da zai faru, dady cewa yayi ko kai fa , sannan nasa amsa maka 30 million a account ɗin ka zaka gani, hope zasu ishe ka kafin lokacin wuce War ka yayi.

Lion yace thanks dad zasu isa inshallah, dad yace duk abin da kake nema please you should call me ok,

Lion yace ok dad safe trip, ya buɗe mai ƙofa dady ya shiga, direba ya tada mota, suka wuce.

Suna wuce wa lion yayi wani ihu ya daka tsalle na jin daɗi, wayar shi lion ya ciro cikin forket ɗin shi,

A'ishah ya kira Bugu biyu ta ɗauka yace hello bugun zuciya daga can bangaren A'ishah tace na am yaya Aliyu na ,

  Lion murmushi yayi yace kina wani abu ne yanzu, A'ishah tace a'a mai ya faru,

Lion yace dama wani guri nake so ki raka Ni, Aishah tace ok bari in tashi in shirya,

lion ya ƙara da cewa in kin gama nan da minti talatin ki same Ni a bakin titin kings road , 

kafin sukai sallama lion ta kashe, suna gama wayar part ɗin shi ya koma yayi wanka ya fito yana zuba uban ƙamshi ( uhmmm nace waya ga sabon ango )

Key ɗin motar shi ya ɗauka , ya fito ya shiga cikin motar, a bakin titin ya tadda Aishah na tsaye tana jiran shi,

Fakin yayi, A'ishah na ganin motar shi ta ƙaraso, tana sanye da pink ɗin hijabi da ta ɗinka cikin kuɗin da lion ke bata,

Ta rufe rabin fuskar ta da bakin face mask tare da sanya farin gilashi ma dai-dai ci, buɗe ƙofar tayi ta shiga da Salma,

Lion ya amsa yana sakin mata murmushi ɗuƙar da kan ta ƙasa A'ishah tayi alamar jin kunya, sannan ta buɗe bakin ta tace ina kwana, duk da yau sunyi waya yafi a ir ga,

Lion ya amsa sannan ya tada motar suka bar gurin , suna cikin ta fiya lion ya juya ya kalli A'ishah ya ce kin san inda zamu je,

A'ishah ta ce a'a, lion yace to ya in nace zan kai ki inda za a fille miki kaine fa bakya jin tsoro,

Murmushi Aishah tayi ta ce ya Aliyu kenan na yar da dakai , nasan baza kaso wani abu ya cutar da ni ba balan tana kai kayi yin ƙurin haka,

Imma zaka Kai Ni inda za a cire min kai ne nasan kai ma har da naka za a cire,

yah Aliyu ka sani zan kassan ce mai taka duk inda ka taka, sannan mai zuwa duk in da kaje,

koda ana ƴan kar naman jiki nane a gurin kuwa, abar ma zan cen ina za muje, sauke nunfashi lion yayi yace, zamu je mu siyo kayan da zamu shirya gidan mune ,.

suna maga sai gasu sun ƙara so wani Company da suke sai da kay furniture da sauran kayan amfani na cikin gida,

Faka motar shi yayi a in da aka yi shi musamman Im costomer sun zo da mota su faka a gurin,

Yana faka ya fito ya sagayo ya buɗe wa A'ishah ƙofa ita ma ta fito ya riƙe hannun ta
Suka shiga cikin gurin ,

Nun nuna musu kayayyakin a ka shiga yi, sun zaɓa gado da kujeru masu ɗan karen kyau da tsada , ƙana suka ƙara da wasu kayayyakin kitchen.

Biyan kudin lion yayi cikin kuɗin da dady ya bashi sun siya kayan da ya haura wa miliyan shida,

Address ɗin gidan lion ya basu kafin suka wuce akan in sun koma gida za a kawo kayan,

Daga gurin ba gida suka wuce ba wani ƙaton mall suka wuce, na ma Atam fufi da leshika lion ya siyar wa A'ishah,

kafin suka koma gurin kayan bacci lion ya zage yana zaɓa dan yaga A'ishah na jin kunya, kaf cikin kayan ba na kir ki,

A cikin mall ɗin suka yi siyayyar kayan abin ci, aka je gurin biyan nan ma an kashe fiye da million,

A'ishah tsora ta , ta fara yi da lamarin, a cikin mota aka sa musu , kafin suka nufi hanyar gida.

A'ishah bata shiga cikin gidan su lion ba gidan su ta wuce, akan bari taje ta dawo kafin a jera kayan, shi kuma lion ya shiga gida ya kira Company furnitures ɗin suka ce gasu nan zuwa,

Ba a fi min ti talatin ba suka iso , suka fara aiki, tsofaffin kayan aka fara fitar wa ,

kafin aka shirya sababbi, lokaci ƙalilan guri ta ɗauki kyau sai dai Masha Allah, kamar gidan wata sabuwar amarya ( kash na manta ashe fa na sabuwar amarya ce ).

Ita ko Aishah tana ƙara sawa gida kamar ko da yaushe a ƙofar gida ta gamu da malam yana karatu, tsugunna wa tayi ta gaishe da malam ya amsa,

Malam ya ce kin ji labarin kun kusa koma wa makaranta ko ɗasu na kunna rediyo ina saura ran labarai naji ana sanar wa, wai yajin aiki ya ƙare,

A'ishah ta ce eh baba, ance nan da sati Daya zamu koma, malam yace masha Allah ku dage kun ji karatun shine kawai gatan ku shi kaɗai ne abin da zan baku ya zauna tare da ku har mutuwar ku Allah ya bada Sa'a ya kare min ,ku

A'ishah ta amsa da Amin kafin ta tashi ta shiga cikin, takai kusan awa ɗaya a gida dan har girki tayi wa mama kafin ta mata sallama ta wuce.

Gidan su lion ta koma, tana shiga falon taja ta tsaya ba ƙaramin kyau ya mata ba falon, taga anjera komai da suka siya ɗazu gurin ya dawo aljannar duniya

Tana tsaye tana ƙare wa falon kallo kawai taji a rungume ta, ta baya ƙamshin turaren lion da taji ne yasa tayi murmushi.

Juyu da ita lion yayi suna kallon juna ya cire mata face mask da eye glass din dake fuskantar ya jefa su saman kujera,

Sake runguma ta jikin shi, A'ishah jin wani abu kamar maciji tayi yana mata yawo cikin jikin ta,

Sumbatar kumatun ta yayi yace cikin sexy voice ɗin shi, ya ki ka ga gidan  namu, da fatan yayi miki kyau,

A'ishah ta ce sosai ma, murmushi lion yayi yace ummm kaji ta wai sosai ma , ya kwaikwayi yacce tayi magana.

Murmushi Aishah tayi ta ce yah Aliyu, sumbatar laɓɓan ta yayi ya sake kwaikwayon yacce tayi magana yace what my love.

Dukan ƙafaɗar shi tayi cikin wasa tace baza ka bari ba ko, chakwulkuli ya fara mata ta fara sheƙa uwar ɗaria har tana kai wa ƙasa,

Filo ta ɗau ko ta fara jefa mai shima ya ɗauko yana jefa mata haka duk suka ɓata falon, sai da suka gaji kafin suka kwanta a ƙasa suna dariya suna sauke nunfashi,

Sai da suka huta kafin lion ya tashi ya ɗaga A'ishah ita ma yana cewa tashi muje ki ga ɗakin mu ɗakin da zamu ɗin ga raya sunna,

A'ishah cewa tayi kai yah Aliyu, lion yace ahh da me kike nufi sai in tsaya kallon ki kawai, kema kin san Ni ba rago bane amma inshallah a gobe zan tabbatar da kai na,

Share shi A'ishah tayi dan ɓaƙaramin kunya yake sa taji ba, shiga cikin ɗakin tayi tana dudduba ba wa, komai yayi kyau , sunsan aikin su gaskiya,

Sai da ta gama duba ko ina, taje ta wanke bayin da duk abin da ya dace , da ta gama dama lion na jiran ta zasu je su kai ɗin ki

Hijab ɗin ta ta mai da , da face mask, fita sukai , sai da suka kai ɗin ki lion ya bada kuɗin ɗinkin duka, tela ya musu alkawarin suzo su ansa nan da one week, gidan ya mardiya lion ya maida ta akan zasu a haɗu gobe da safe

Tofa

Daga gobe ne

Gobe ne A'ishah zata aure lion ba tare da sanin iyayen ta ba

Gobe naje ganin littafin ƙaddarar Aishah zai buga buɗe.

**"******

Abin da zai sa kawai gobe nayi update shine naga ruwan comments

Ba likes ba comment ba new page gobe , sanin kan kune Kun san cewa gobe zai yi daɗi

Sai naji ku bye

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now