•𝐏𝐚𝐠𝐞{39}•
🅝︎🅞︎🅣︎ 🅔︎🅓︎🅘︎🅒︎🅣︎🅔︎🅓︎
*B͎i͎s͎m͎i͎l͎l͎a͎h͎*
"Kwanaki da satitti ka ne suka ringa tsere suna wuce juna, har ta kama yanzu kusan wata biyu da faruwar wannan al'amarin.
Tsan gwamar yan unguwa ta ragu, sai dai har yanzu ba wanda ya cigaba da halartar masallacin na malam, ko yi mai magana
Yanzu haka jari ya samu yana bin kasuwan nin gwauye yana sai da kayan hatsi , yana samun ɗan abin da zai rufa wa kan shi asiri shida iyalan shi,
Ta ɓangaren yaya naja tsakanin ta da mijinta ba abin da ya canza, bayan ƴan kwanaki ma tana zaune ya shigo gida ya miƙa mata takar da,
Bata amsa ta tambaye shi takar dar Meye kenan, cikin ko in kula yace takar dar sakin kice, miƙe wa naja tayi ta dafa ƙir jin ta tana furta innalillahi wa'in na ilaihir'raju'un,
me na maka haka Haruna zaka yi min irin wannan mummunan hukuncin saki Ni, sa hannun shi a kwankwason shi yayi yace , ai kin cancanci fiye da haka ma, ke da ahalin ki wuta ya kamata a saka ku,
Naja cewa tayi daka ta malam, zan iya daukar ko wani cin mutuncin ka amma kar ka sake ka sa iyaye na a cikin, ba dai gidan ka bane zan bari amma ka sani ƙafa ta ƙafar yara na,
Haka naja ta dawo gida tare da yaran ta guda uku tana zaman id'da,
Nauyin ya sake hawa kan malam, Aishah ko aiki ne ya ƙara yi mata yawa in kaga hutun ta kowa a gidan yayi bacci, nafisa ce kawai ke jin tausayin ta ,
Ayau safiyar ranar talata har waye War gari Aishah bata fito ba, kowa ya fito manya da yaran,
Aishah ke shirya yara su tafi makaranta amma yau har misalin ƙarfe bakwai na safe bata fito ba, ita da take tashi tun kiran sallan farko,
Ba wanda ya ƙarya dan duk aikin Aishah, mama ce taji shirun yayi yawa, ta yiwa nafisa maga da ke daka tsami zata tafi makarantar da ta fara teaching,
Nafisa wai yau lafiyar Aishah ƙalau kuwa naga har yanzu bata fito ba, nafisa ta bawa mama amsa, da ta kwana bata jin daɗi ne,
Mama tace assha amma dai kin bata magani ko, nafisa tace eh tasha paracetamol, sai dai in ta tashi ta ƙara sha,
Naja da mardiya ne suka yi aikin yau, sai wajen ƙarfe goman safe A'ishah ta tashi, mama ta bata abin ci, ɗakyar taci ƙaɗan tana jin amai na taso mata,
Mama ta ɓallo paracetamol ta bata, Aishah ta amsa tasa a bakin ta, zata haɗiye kenan amai ya taho mata, da gudu ta tashi ta yaje ta tsugunna a gurin da suke zubar da ruwa,
Ta rinƙa kwara amai, yaya naja ce ta kawo mata ruwa ta kuskure bakin ta, tare da wanke fuska, kawo i yanzu sun dena jin haushin ta sai ma tausayin ta da suke ji ,
Kama ta tayi ta zaunar da ita kan tabarma Aishah ta jin gina da jikin bango tana sauƙe nunfashi
Ɗakyar ta sake shan maganin ta koma ta kwanta,
Haka Aishah ta cigaba da fama da zazzabin daga yamma zuwa safiya,
Da kyar mama ta ruƙi baba ya yar da akai ta asibiti , yaya naja ce ta shirya zata kai ta,
Primary health dake muchiya suka je, suna zuwa clinic ɗin suka sai kati,
Bayan anyi gwaje-gwaje likita ya kira su cikin office ɗin shi,
Da suka shiga suka gai she ya nuna musu gurin zama suka zauna,
Kallo ya ƙare musu ya ce ina mijin ta yake, yaya naja tace likita bata yi aure ba bata da miji ai,
Likitan yace ok, rubuce rubuce yayi a cikin ta kar da ya miƙa musu tare da cewa, sakamakon gwaje-gwajen da muka yi ya nuna cewa tana ɗauke da cikin wata uku da sati biyu,
Murmushi naja tayi tace haba likita yanzu na gama cewa bata da aure , taya zata samu ciki kuma , a'a a dai sake duba wa,
Likitan cewa madam mu dai ga iya abin da gwajin mu ya bamu kenan in kun ga baƙu gamsu ba zaku iya zuwa wani asibitin , ina mai tabbatar muku amsar da za'a baku kenan, zaku iya tafiya
A fusace yaya naja ta tashi ta a cikin office ɗin, A'ishah ko tun da likita ya furta cewa tana ɗauke da juna biyu, ta ɗauke wuta na wasu mintoci,
Da kyar ta tashi ta bi bayan naja dan ta riga ta mata nisa,
Cikin tsoro ta shiga gidan, taja ta tsaya, yaya naja ce a zaune mama tana tambayar me ke damun Aishah,
Naja cewa tayi ga tanan ta shigo tambaye ta gaya miki, mama kamo Aishah ta ce zo ki gaya min make damun ki,
A'ishah tayi shiru bata ce komai ba, naja tayi tsaki tace ta gaya miki bayan yanzu gani take kan ku ɗaya abin da kika sani ta sani,
Mama cewa tayi wannan wace irin magana ce haka naja wato yau rashin kunyar taki takai na ta biyu ko, to wallahi ki kiyaye,
Maza ki gaya min ko na saɓa miki, tura bakin ta tayi naja tana ƙunƙunai tace , wake taje ta ciwo
Mama ta cire takalmin ta ta jefo naja da shi, naja tace haba mama yarinyar nan wata magana zata sake ɗauko mana fa cikin ne da ita,
Mama cewa tayi ciki, naja tace ciki kuwa, mama ta fashe da kuka ,
Malam shima ya shigo cikin gidan kenan ya dawo daga kasuwa yaji abin da naja ke faɗa,
Zuciyar zafi ta fara mai ya dafe ta, a gurin ya faɗi,
Ƙara fadu war da suka ji yasa suka tashi da sauri gani malam a kwance baya motsi, da sauri suka tashi suka zagaye shi ,
Mama na mai fifi ta naja taje ta kawo ruwa aka yayya fa mai amma bai farfaɗo ba,
Keke nafe naja taje ta samo aka sa malam a ciki aka wuce da shi asibiti,
Da sauri aka amshe shi ganin irin halin da yake cikin, likitoci suka shiga bashi tai makon gaggawa,
Bayan awa biyu suka fito likitan ya kalli Norse ɗin da ke biye da shi a bayan da rike da takardu a hannu yace ta zo mai da ahalin mara lafiyan.
............
See ya
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...