PAGE 2

3K 153 0
                                    

*HIDAYAH NOOR*
'''Reposting'''

*©️Halima.hz*
*halimahz@Arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*2*
Gari na wayewa Ammar ya hau gyaran gidan, dama ko Adda Halima na nan ba ya fita sai ya share mata tsakargida zuwa soro ya wanke mata banɗaki. Yanzu kuwa har wanke wanke yayi ya ɗebo ruwa a can wata rijiya ya cika duk botikai, ko'ina ya share ya gyara yay tsab tsab ka rantse ba gyaran namiji ba. Harta turare ɗan tsinke sai da ya kunna ƙamshi kuwa har soro. Sai da ya kammala komai tukunna yaje yayi wanka.

Wani koɗaɗɗan yadinsa da ya gaji da jemewa ya saka, kayansa kala huɗu ne rak a duniya, duk da yadin ya sha jiki amma hakan bai hanasa yin ƙyalli ba saboda yacca ya sha guga. Turarensa da bai wuce ɗari biyu ba ya fesa, yay kyau sosai a cikin sassauƙar shigar tasa. Biredin da ya siyo daren jiya ya ɗakko kana ya fito yana rufe ƙofar ɗakin nasa.

A bakin ƙofar ɗakin nasa ya tsaya yana ƙirga sauran kuɗin jiya da ya samu jiya naira dubu biyu da ɗari takwas, dama dubu huɗu ne gaba ɗaya, ya siyo kayan shayi da maganin sauro, ɗazu da ya fita ɗebo ruwa ya kaiwa Tabawa mai ƙosai kuɗin ƙosanta da aka karɓawa Hidaya da zata makaranta.

Haka yake jin daɗi na ratsa shi, rabon da ya riƙe kuɗi kaman haka har ya mance. Allah na taimakarsa indai ya samu ɗan sahu ya fita to yakan huce takaice amma kafin ya samu ɗin ne aiki babba.

Jemammiyar wayarsa mai ɗauke da ɗaurin kyauro ya fito da ita yana kallon lokaci. Ƙarfe 9:30, da sauri ya fita dan yanzu su Inna na can na jiran abin kari.
Bai fara wucewa gidan ba sai da ya tsaya ya saya masu ruwan shayi yau kam har da madara.

Da sallama ya shiga cikin gidan, duk suna ɗaki, yau kafin ya zo har Adda ta share tsakargidan da banɗaki, gidan yay tsab kasancewar safiya ce sai ɗaukan ido yake. Ciki ya wuce don tunda Inna ta jiyo sallamar tasa take aikin ƙaraso mana.

"Salamu Alaikum".

Daga ɗaki suka amsa masa da "wa'alaika salam".

Sai da Inna tayi masa izinin shiga ɗakin tukunna yasa kai.

Zama yay daga nan bakin ƙofa.
"Ina kwana Inna"
"Ina kwana Ammar, mun tashi lafiya, ya kwanan kaɗaici".

Ya shafo kansa da cewa,"Ai kuwa dai yau na ɗan kwana ni ɗaya".

Adda ya kalla wacca ke ninke kaya itama ya gaida ita,"Adda ina kwana".
"Lapia lau ya muka kwana".

"Ƙalau, sai dai na kwana da kewarki".
"Allah sarki inan wurin Innata na mance da kai, nayi zaton ma da ka shigo ka ganni kaima zaka kwana nan ɗin"

Bai ce komai ba ya miƙawa Inna kayan shayin da ya shigo da su. Ta karɓa tana saka masa albarka, sai da ta buɗe fuskarta ta washe da annuri tana cewa,"Iyee ka ce yau daɗi zamu ci, Yarona na son mu da yawa, Allah yayi maka albarka ya buɗa maka hanyar samu".

Ya amsa da amin yana miƙewa ya fice ya ɗauki tsintsiya don share ƙofar gida da kuma ɗebo ruwa.

Sai bayan ya gama ya dawo ya zauna yana bawa Inna labarin aikinsa na jiya. "Ai Innaa jiya naji daɗin aikin nan, ba ki ga ba har dubu huɗu na samu fa".

Da mamaki suka kalle shi kowacce na riƙe haɓa,"Dubu huɗu Ammar?".

"Wallahi fa, dama aka ce rabonka idan naka ne sai ya sameka. Inna lokacin fa da na bar nan da rana ina wucewa can wajen mu nan inda nake sayar da kalanzir, to akwai wani da ke zaman tireda a wajen shine jiyan bai da lafiya sai yace na ɗau babur ɗin kawai naje nayi aikin, wallahi cikin ikon Allah da na fita ban ma bar cikin unguwar nan ba na dawo na ba shi kuɗin haya, sai yace na riƙe gaba ɗaya ko ƙwandala ba zai karɓa ba kuma naje har sai lokacin da na tashi".

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now