Page 80 LAST PAGE.

2.2K 88 20
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


          *Story~Written~Edited*
               *_By Miss Xerks_*🌺


         *Devoted to Ummi Aisha*

*_2018/2019_*

بسم الله الرحمن الرحيم...


*LAST PAGE*

*80*
Tun daga wannan rana duk wani tattali da kulawa Mansur ya ɗauko ya ɗora akan Hidaya,baya barinta tayi komi data yunƙura da niyyar yi zaice ta barsa zaiyi hakana duk wani motsi nata saiya tambayeta yane? mai take so? ya maida ita tamkar wata ɗanyan ƙwai lallaɓata yake kaman wata jaririya ita kuma sai wani ƙara shagwaɓe masa take.

Sai dai itama bata bar basa kulawa da nuna soyayya ba,makaranta ma tin lokacin yace tayi deferng saita haihu da dariya tace,

"haba honey tin yanzu gaba ɗaya cikin watansa uku fa kaga da sauran lokaci ka barni dai nasan ma acikin hutu zan haihu"

Ba hakan yaso ba danshi fa ko takawa baison takeyi wani lokacin ma saita roƙesa yake barinta ta ɗanyi tafiya amma data miƙe zai sunkuceta ya kaita inda take son zuwa.

Haka  ɓangaren Hajia ma kullum waya takewa Hidaya jin lafiyarta,Inna ko daɗi duk ya hanata sakat jinta take tamkar tayi tsuntsuwa tazo ta ganta sai dai kunya bazata barta ba.

Haka cikinta har ya shiga watanni huɗu ya fara tulu, kallo ɗaya zakayi mata ka gane tana da ciki,cikin ya wani ƙara mata kyau tai wani fresh abinta sai ƙyalli take ba ƙaramin kyau yay mata ba.

Duk sanda ta zauna idan ta kalla kanta ayanzu ta duba irin kula da nuna soyayya da Mansur ke mata saita tina rayuwanta na baya lokacin cikin Mukhtar,ba ƙaramar wuya tasha ba duk tabi ta koɗe ta koma tamkar jaka,lalle gata ma wani abune babbar ni'ima ne.a Allah sarki yanzu motsi motsi kaɗan tayi na ciwo hankalin Mansur zaibi ya tashi ada kama data cika cewa ga wani wuri na mata ciwo Inna zata fara mata faɗan tafiya ragwanta.

Kwance take yau saman cinyarsa a parlo suna kallo tace dashi, "honey mi kake so na haifa maka"?

"namiji"

Saurin tashi tai ta dubesa, "namiji fa kace,banda Irfan ɗin dana maka"

Murmushi yayi gami da janyota jikinsa yace, "to dear banda abinki abinda kike so aishi nike so,ke mi kike son haifa"

Sai data ɗan langwaɓar masa dakai tace,
"mace mana,nima in sami abokiyar pira"

"to yayi Allah dai ya raba lafiya ya bamu kuma mai albarka"
"ameen honey nah" tace dashi tana maida kanta saman cinyarsa.

Sunata hira har 12 tayi lokacin ɗakko Irfan a makaranta yayi,bai barta ita ɗaya ba ta shirya suka fita tare.

       ****

Riƙe da tray ɗin data fito dashi daga kitchen ta nufa dining area ta aje.zama tayi tare da kiran sunan masoyin nata.

"Mahbub"

Yana can yanama Affan wasa baiji ta ba saida ta tashi taje tasami hancinsa ta matse.

"ouchhh yi haƙuri karki ɓallan hancin"

"to bakai ne inata magana ba ka mani shiru"
"sorry Hayatee nah kinsan idan ina tare da my own summun bukmun nike zama"

"umm mai ɗa,to ai saika ijjesa kazo muje kaci abinci ko"
"tom shikenan ranki ya daɗe mar'atussaliha,sannunki kedai Allah yayi maki albarka"

"amin Mahbub ɗina" kama hannunsa tayi shi kuma ya riƙa na Affan dake tafiya yanzu suka ƙarasa ga dining dan cin abinci.

Da kammalawarsu ya wuce zuwa masallaci bayan yajasu sallah ya dawo,tare suka shigo da Aimal data dawo daga schl ana primary 5 an zama ƴan mata.

HIDAYAH NOOR completed.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon