🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''kyauta ne gareku Dr. Meenart and sumayyaadam99...'''
*24*
Wayarsa ya fidda daga aljihu yay dialling numban Yahya.
Bugu biyu ya ɗaga tare da sallama.
"ya kaganni fa ƙofar gidanka nazo maka ba sanarwa""ahh haba dai, to bari na fito ganinan"
Ba jimawa Yahya ya fito,hannu ya miƙawa abokin nasa suka tafa.
"kai mutumina kana jin daɗinka fa,wata uku har kai wannan ƙibar haka"
"hhh to mai zai hana kaiko ana bani kulawa yanda ya kamata...yanzu dai bismilla mu shiga daga ciki"
Gaba Yay Ammar yabi bayansa har cikin gidan.
Masha'allahu gidan gwanin ban sha'awa ya haɗu sosai.
Sallama sukai tare da shiga parlon mai ɗan girma dashi yasha kaya.
Kujera Ammar ya nema ya zauna yana ƙara kallon gidan shi kuma Yahya ya fita kiran Yusra data kawo masu ruwa.
Tare suka dawo shida ita hannunta riƙe da ƙaton tray ta sako ruwa d juice aciki.
Ɗauke da fara'a ta aje plate ɗin kan center table tana ma Ammar tsiyar sai yau zai waiwaye su sunan babban amini.Ƴar daria Ammar yay kansa ƙasa bai ɗago ya kalleta ba saboda ba hijab jikinta yace,"ai mani uzuri abubuwa ne sun sha kai da yawa..kuma shima kinga ai bai gari "
"hmmm haka dai kace..ina yini"
"lapia lau.ya kuke kuma"
"muna lapia wlh..yasu Inna dasu ƙawar tawa"
"wlh duk sunnn lapia suna agaidaku"Sai asann Yahya yace,"Ai bai kamata ki kulasa ba tinda har yanzu bai kawo mana Hidaya ba ga biki har ya kusa"
"Hmmm ai inaga dai saita fara yawon amarci tukunna zan sa ran ganinta""ah haba zata zo maku ne sunanan suna rabon IV zasu biyo tanan"
"tom Allah ya kawota dan niko ina son ƙara ganinta tin bikinmu rabonmu da haɗuwa""karki damu zatazo gobe in Allah ya kaimu"
"to Allah ya kaimu..ka gaida su Inna dan Allah in ka koma"Tashi Yusrah tayi ta barsu su biyu.
"Ammar bismilla kasha lemun mana"
"zansha Yahya..." Ammar ya faɗa da alamun damuwa tare dashi.Zama Yahya ya ɗan gyara yace da Ammar "Allah sarki sai kuma naji abu ba daɗi bayan dawowata"
"nami fa"?
"mutuwar yarinyar nan Surayya"Gaban Ammar ne ya buga dan ko kaɗan shiko bayasan ana tina masa da rasuwarta.
"kaidai bari Surayya Allah ya amshi kayarsa"
"Allah sarki Allah ya jiƙanta wlh mutuwarta ta dakeni..ashe ta jima kwance tana jinya""umm ta jima kwance wlh kasan ko bayan rabuwarmu tasha mani kira da text nazo dubata bata da lapia sose ni kuma Allah bai nufa naje ba wlh sai ranar dazata rasu"
"wato kasan babu abinda ya faɗo mani da aka ce ta rasu sai lokacin da Daddynta ya kiraka yake cewa mine aibun ɗiyarsa da bata cancanci asota ba..ka daure ka aureta zai baka duk wani abu da kace kana so matuƙar baifi ƙarfinsa ba"
VOCÊ ESTÁ LENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficção HistóricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.