Page 49.

809 72 4
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                       🌀🌀🌀🌀🌀



     *Story~Written~Edited*
                *_By Mss Xerks_*🌺




      *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...


*49*

Ƙarfe 9 na safe Hidaya ta dira a ƙofar gidan.

Joseph ne a duty ganinta yaƙi buɗa ƙofa yace ta koma.

Ta jima tana roƙonsa yay banza da ita ƙarshe ma ya rufe gate ɗin.

Har 10 tana zaune wurin tai jugum tana tinani, fatan ta Allah yasa Ammar yace ya janye ƙararta da yayi.

Tana jingine daga bango Gwaggo Amina ta fito.

Ganinta yasata sororo tana kallonta,

"A'a Hidaya lafiya kike tsaye anan"

Ɗan murmusawar ƙarfin hali tayi tace, "Gwaggo Amina ina kwana"

"lapia lau yasu Innar taki"

"suna lafiya kuma kuna lafiya"

"lafiya lau wlh, amma tsayuwar mi kike nan baki shiga ba"

Shiru tai bata bata amsa ba dan haka Gwaggo Amina ta fahimce ta, sarai tasan Joseph ba mutunci tinda ya dawo aiki gaba ɗaya babu mai karɓarsa ya zama ba kowa ma keson zuwa gidan ba.

Gate ɗin ta ƙara knocking buɗewar joseph yace "sannu hajiya" ya faɗi da girmamawa dan yanzu Gwaggo Amina ita ta zama tamkar uwa agidan.

"ka bar wannan yarinyar ta shiga itama ƴar gida ce ƙanwace ga Alhji"

"a'a fa Hajiya wannan yarinya kwanaki data zo ta kusa ja mani na rasa aikina, ina soro na barta ta shiga yanzu na kuma samun matsala"

"kabarta ta shiga babu wata matsala dazaka samu"

Badan yaso ba yana ƙunƙuni ya matsa mata ta shiga yana hararta.

Gabanta na dukan ukuuku tai tsaye nan compound ɗin.

Tinaninta shigarta ciki, ta tabbata Ammar zai yarfa ta kuma hakan bazai dameta ba sai dai ko kaɗan bata son walaƙancinsa gareta agaban Sadia.

Tinani ta tsaya yi shin ta shiga ko kuma ta jira fitowarsa.

Takawa tai zuwa ƙofar tasu ta danna bell da yin ƙararta ko Sadia ta buɗe.

Ɗauke da murushin jin daɗi tace, "Ahhh Hidaya kece bismillah shigo"

Shiga Hidaya tai da sallama suka ƙarasa tare zuwa kan kujera.

"Ina kwana Sadia"

"Ina kwana Hidaya,ykk y gida dasu Inna ina mukhtar"

"wlh kowa lafiya Mukhtar na gaidaki"
"Allah sarki ina amsawa, bari na ɗauko maaki lemu ko"

"a'a da kinma barshi a ƙoshe nike wlh"
"a'a ya kamta dai ki ɗan taɓa wani abun matafiya ai yana buƙatar ko ruwa ne"

Tashi tai ta buɗa madai2cin fridge ɗin dake parlon ta ɗauko drinks ta kawo mata.

A cup ta zuba mata ta miƙa mata wadda ita hankalinta ma bai kanta.

"Hidaya lafiya dai wai na ganki wani iri koda damuwa ne"

"dan Allah Sadia idan Hamma na nan ina son magana dashi"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now