🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
_INA MAI BAKU HAƘURI NA RASHIN JINA YANDA YA KAMATA, RASHIN POST D WURI DA KUMA TYPING KAƊAN,KUYI HAƘURI ISHA'ALLAHU A HANƘALI KOMI ZAI DAIDAITA MASOYANA_.
*56*
Ware da ido Jamil ya tsaya yana kallonta,zaiyi magana ta dakatar dashi.
"kaga ban kuma son jin wani zance naka,dama ashe badan tausayin halin da nike ciki kake tare dani ba duk wani taimako da kake mani dan na soka ne toko kayi kuskure wlh indai soyayyata ne bazaka taɓa samu ba"
"Haba Hidaya wannan wanna irin zance kike haka ,ya kamata ki tsaya ki saurareni kamin ki zartar da hukunci, wlh babu wasa a maganar danayi maki,ki fara bani dama mu fahimci juna tukunna"
Dogon tsoki taja ta ɓalla masa harar takaici.
"Jamil ina ganin mutuncinka karka bari ya watse daga idanuwana,kana sona ni kuma bana sonka na faɗa maka kaji da kyau, aure ne kake nemana dashi to banyi kaje can ka nemi wata ai bani ɗayace mace ba,bana son takurawa"
"to yanzu mi yayi zafi duk aciki kika tada jijiya kina haƙilo Hidaya,ki fara bani dama mu fahimci juna inaga zaifi ba ki kalla abin ta bai2 ba,mufa ba yara bane daga ni harke, wlh karki tinanin yaudararki zanyi...karki ce dan mijinki ya rasu bazaki kuma wani auren ba niyaar hakan ma babu kyau,nasan kina tinanin ɗanki to wlh na maki alƙawarin zan riƙe makishi tamkar ɗan dana haifa,amma maganar gaskiya bazan iya rabuwa dake ba wlh ina sonki kuma so na gaskiya nike maki ki taimaka ki bani gurbi a zuciyarki domin na shimfiɗa maki salon tawa soyayyar,zan kawar maki da duk wata damuwa taki"
Yana kai ayar zancensa ta wurga matsa ledarsa.
"Jamil bana sonka bana sonka ba kuma zan taɓa sonka ba ka fita a rayuwata ka fita a lamurana idan ba haka ba komi na maka kai kaja, waima ana so dole nene, to bari kaji ni da kake ganina ba aure zanyi ba karatu zanyi dan haka karka zama silar ruguza mani tanadi na,kaja da baya domin bazaka samu abinda kake so daga gareni ba sannan karkai tinanin kuɗin da kake tinƙaho dashi zaisa na soka ko kuma ka iya sayen mahaifana dasu to bazasu sayu ba nima kuma bazan sayu ba, kasan inda dare yay maka tin wuri kar kaja nayi maka abinda harka koma ga mahallicinka bazaka manta shi ba Mtswwww"
daga haka bata jira cewarsa ba ta shige gida da banko gate.
Sam abin bai masa daɗi ba dan harga Allah shi sonta yake da gaskiya kuma son da yake tinanin bazai iya rabuwa da ita ba.
Jimmm ya ɗanyi na tsawon wani lokaci kamin daga bisani ya sunkuya ya ɗau ledarsa ya koma motarsa yaja.
Inna na daga parlo ta shiga ta wani wulli da Mukhtar tana tsaki, Inna na mata magana tai ɗaki da gudu batama tsaya sauraronta ba.
Da kuka ta faɗa kan gado tana jin kaman ta tsaga ƙirjinta ta cire zuciyarta gaba ɗaya ta yar kota sami sukuni.
Ta daɗe haka tana kuka harta gama Inna dake kusa da ita ta tasheta da bata baki har ta ɗanji relif kamin ta ware ta fito su cigaba da aikinsu.
Suna aiki da hirarau suke sauraron radio.
Kaman daga sama Hidaya taji an ambaci sunan Ubaid Nuhu,katse Inna tayi daga maganar datake."yi shiru Inna", radio ɗin ta ɗauka ta ƙaro volume.
ESTÁS LEYENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficción históricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.