Page 52.

1K 85 6
                                        

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                         🌀🌀🌀🌀🌀



              *Story~Written~Edited*
                        *_By Mss Xerks_*🌺




              *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...


*MAMAN HAJIYA, UMMU IMRAN ,UMMU AFNAN, SMASHER, NUWAIRA, HAFSAT*
_NO GODE SOSE DA NUNA KULAWARKU GARENI._

*52*

"Kwananmu biyar muna yawo kan hanya babu mafakar zama sai dai in dare yayi mu raɓe ga gidan mutane, ganin babu yanda muka iya nace da Adda kawai mu komo nan wurinku, haka muka juyo tin kan ƙarasa fitowarmu daga cikin mota aka fara mana ihu zagi kai da yana tsiro ai da yayi ajikina, haka aka dinga jifanmu suka kuma hanamu shigowa haka dolenmu muka juya ,to munan tsaye titi ina gogewa Adda ciwon da sukaji mata saiga Sadia ƙawar Hidaya da yayanta ya ɗaukota a makaranta.nan suka taimaka mana zuwa gidansu suka kai Adda asibiti zuwa yamma mukace zamu tafi Ummanta tace a'a babu inda zamu mu zauna tukunna kamin wani lokaci to duk da gardamar dana sa masu kwarjinin mahaifinsu yasa dole muka haƙura muka zauna anan",

"kusan kwananmu biyar anan da raununka Adda suka warke tace tafiya zamuyi nanma tafiya bata yiwu ba, da haka na kira Abdullahi a ɓoye ya sameni dan bana ko son fitowa jama'a su ganni,bada sanin Adda ba nai masa zancen aurensu na idan bai fasa ba to ina ganin zaifi dacewa ace tai aurenta duba da hali na rayuwarmu da muke ciki yanzu, to a sati uku aka ɗaura aurenta ta tare dashi. Daga nan ni kuma na kama gabana zuwa can garinmu dangin mahaifinmu inda nai sa'a na samesu suka kuma yi murna da ganina nan suka bani ragowar gado na mahaifinmu shanu150 da gonaki 4 to dasu na dawo na kawowa Adda , aciki Abdullahi yaja jari indai yay manyan shaguna a kasuwa muka fara zama tare daga baya kuma mahaifin Sadia ya nema mani reslt na IJBM dirct to level 2 acan pataskum inda yake aiki na cigaba da karatuna na ccounting a Bukar Abba University inda na fara karatuna cikin jin daɗi duk da idan na tina abinda ya faru dani a duk sanda nazo hutu nan nakanji ɗaci cikin raina, wani zuwa dana kuma yi hutu rashin sa'a mutan garinn suka ganni suka rufar mani hakan yasa na kwashi su Adda muka koma can pataskum da zamanmu dan bana ko san garin ayanzun... .acan muka haɗu da abokina Hydar wanda mahaifinsa yake manager ne a CBN bayan kammala karatunmu kai tsaye muka fara aiki, to ina a shekarar da zan gama sati biyu ya rage bikin Sadia da Saifullahi wanda zata aura yay accident ya rasu to duba da halin data shiga Adda ta roƙeni akan dana aureta nace sam aini da mace sai a aljanna,babu yanda batai ba naƙi duk da cewar itama yarinyar bawai dan tana sona bane sai dan bin itama umarnin mahaifiyarta akwana a tashi kuma har ta fara sona, ƙarshe tausayin yarinyar da kuma irin karamci nata dana iyayenta garemu daga baya yasa na aminta da auren nata duk da cewar nayi hakanne dan farincikin Adda na, kamin bikin namu kuma ta roƙi mahaifinta aka fita dani zuwa Germany amani aikin ƙafata tinda ance in anyi aiki zai warke ta haka aka mana visa mukaje zuwa Germany aka mani aiki da ƙwarrarun likitoci akan kuɗaɗe masu yawa da dawowarmu bayan wani lokaci kuma akai bikinmu cikin ikon rabbi da ikonsa muka ci gaba da zamanmu acan Pataskum duk da iyayenta sunso mu zauna anan nace a'a bazan iya zaman nan ba ina son sake sabuwar rayuwar jin daɗi, da zuwa bank da muke da Hydar har na sami ƙarin girma acan Bank ɗin danake aiki na zama Manager a hankali Allah na daɗa dafawa nima harna buɗa kuma nawa Bank ɗin na kaina wanda ayanzu yana ɗaya daga cikin wanda ƙasarmu take ji dashi..."

"Gaskiya ne abu yayi kyau amma kuma nai mamakin haɗuwarku dasu Inna duba da yanda mu nan aka dinga nemansu ƴan'uwansu suna ta zuwa"

Murmusawa Ammar yayi ya shafa gemunsa,

"akwai wani guy nan da zata aura daa Mansur to abokin Hydar ne kusan tare suka tasa, to a wayarsa na sami hotonta dana gani nake tambayarsa inda ya santa tinda nima lokacin ina nemanta ido rufe dan ta wankeni daga zargin mutane sai kuma nai sa'a yake shaida mani cewar budurwarsa ce anma kusa bikinsu to aranar auransu wani tsautsayi yasa aka fasa ni kuma tanan na aika driver na ya bibiyesu har ya ɗaukosu ya maido su nan Pataskum inda muke, shi kuma Baban nata dama can sun haɗu da Adda ne ta inda yake neman iyalinsa yanda muka saba dashi halin damuwar da yake ciki na rashinsu nake tausaya masa har nake tambayesa sunansu in yaso sai a tayasa bincikasu a gidan radio ko Allah zaisa suji to da faɗan sunansu da kuma kwatanta mani su yasa na gane su ne...... To kaji ta yanda abubuwa suka tafar mani bayan rabuwarmu"

HIDAYAH NOOR completed.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora