Page 60.

1.3K 83 1
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                          🌀🌀🌀🌀🌀


      *Story~Written~Edited*
          *_By Mss Xerks_*🌺



      *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...


🤣🤣 *GASKIYA KIN BANI DARIYA WATO ALLAH YASA YA KUMA GURGUNCEWA IDAN SADIYA TA MUTU😂😂*, *AMMAKO DA BAKIMA NOOR ADALCI BA GASKIYA*🤣🤣....

'''Masoya Sadia easy dai karku sa cikina ya ƙulle😂😂...'''

*60*
Komowarsu daga lab ya buɗa cooler ya zuba mata shinkafa da miya sai naman kaji samansa da kansa ya haɗa coslow duk ya aje mata.

Gadon ya gyara mata yace ta zauna sannan ya miƙo mata plate ɗin abincin yace gashi taci.

Shiru kaman wanda yay magana da dutse ko inuwarsa bata kalla ba bare ta tankasa.

Kujera yaja ya zauna yana fuskatarta wadda tai tamau da fuska idonta a ƙasa babu alama na zata saurareshi.

"Hidaya kina dai jin mai likita yace ko, ulcer zata iya kamaki idan har baki cin abinci,dan Allah dan Annabi ki daure ko kaɗanne kici badan halina ba ki taimaka kinga Inna da Baffa ma basu jin daɗin ƙin cin abincinki"

Ganin bata da wata niyya ta zataci abincin ya ɗebo da spoon zai kai bakinta azuciye ta tankwaɓar da abincin ya zube jikinsa gaba ɗaya.

"haba dan Allah ka rabu dani ka ƙyaleni ka fita a lamarina ko ana dole ne, nace maka bani son takurawa ka barni mana, rayuwata rayuwata ce bata ka ba dan haka ka safafa mani idan na cutu ai bakai ka cutu ba, abinci ne bazanci ba cikina aiba naka ba mtswww"

Kallonta yayi ya dubi jikinsa data ɓata masa da maiƙon miya.

Baice da ita komi ba ya miƙe ya shiga toilet yasa ruwa ya ɗauraye ya fito.

Farar shadda ce ajikinsa dan haka maiƙon bai ɓoyu ba dan miyan ta soyu.

Harga Allah bataji daɗin abinda ta masa ba sai taji inama ta miƙe taje ta wanke masa sai dai bazata iya ba dan har yau idan ta tina kalmar na tsaneki dayake faɗa mata a baya takanji haushi ba kaɗan kuwa ba.
zasu haɗa ido daga kallon datake masa tai saurin sauke kanta ƙasa.

Yana gama gogewa ya kuma Jan kujerarsa gefe da ita ya zauna tare da ɗauko wayarsa yana dannawa.

Sai daya bari ta sarara daga hucin fushin datake sannan ya kuma miƙewa ya zuba malt a cup ya miƙa mata.

"gashi shanye dan zakisha magani wannan kuma baki isa kice bazaki sha ba"

Neman takurata da yayi nanma da zuciya ta ɓarar masa da ita ajikinsa.

Da mamaki ya ɗago ya kalleta ya kuma kalla kayan, duk da ransa ya ɓaci sai ya kawar bai nuna mata ba kawai ya share.

Aje cup ɗin yayi ya fice,jikinsa ya tsaya kallo sose ta ɓata masa su dole yasan abinyi dan baisan mizai ce da Sadia ba idan ya koma ta gansa haka.

Boutique yaje ya sayo jeans da t-shirt ya dawo nan office ɗin Dr Mujahid ya ɗauraye jikinsa ya sauya kaya sannan yasa wani ma'aikaci a wurin ya wanke masa waɗancen ya goge masa.

Sai dayayi la'asar sannan ya koma room ɗin, tanan kwance an sake sa mata drip saboda amai data sha ɗazu kuma duk a rashin abinci ne.

Sannu ya mata yaja ya zauna bayan drip ya ƙare ya miƙe ya cire mata.yay mata sannu tai masa banza shima baice da ita ƙala ba ya ɗauƙo choculate ɗin daya sayowa Mukhtar ya bashi yana masa wasa shi kuma yaron na wasa da gemunsa kaman yanda Aimal keyi masa.

HIDAYAH NOOR completed.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang