*HIDAYAH NOOR*
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabook*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*Tsohon Labari ne, a yanzu kuma ana gyara shi, Littafin kyauta ne bana kuɗi ba. Littafi na farko da na fara rubutawa sai abinda ku ka gani🤣🤣ko zai muku daɗi oho😂
Da sunan Allah mai Rahma mai jin ƙai.
*(1)*
Da ganin fuskarsa zaka san akwai damuwar da ke ƙunshe a ransa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin gidan na su mai ɗauke da ɗan ƙaramin tsakargida, simintin tsakargidan duk a farfashe yake yayi ramuka, wani wurin an cike da ƙasa wanda hakan yasa wasu wuraren suka yi tudu da kwari. Shi kansa bangwayen duk a farfashe, da yake kusan rabin ginin gidan na jar ƙasa ne. Ba sai an faɗa maka ba, gidan ya isa ya shaida maka cewa mazauna cikinsa talakawa ne sosai wanda ke fama da cin yau da na gobe.Tsakar gidan a share yake tass babu datti ko guda, kana kallo kasan mazauna cikinsa masu tsabta ne, talauci bai sa sun zama ƙazamai ba.
Wurin da ake ajiye jarakunan ruwa ya nufa da butar da ya ɗakko a banɗaki a hannunsa ya zuba ruwa a ciki ya shiga banɗaki, bai jima ba ya fito yana kaɓe jikinsa da sauran damshin ruwan hannunsa.
Botikin ƙarfen da ke dire a tsakiyar tsakar gidan yaje ya ɗauke ya killace shi a muhallinsa, bai nufi ɗaki ba sai da ya gama ƙarewa tsakar gidan kallo ya tabbatar komai a gyare yake tukunna ya wuce ciki.Yagalgalallan labulen ɗakin ya ɗaga ya kutsa kansa ciki yana ƙara yin sallama. Kusa da Inna ya samu ya zauna akan tabarmar da take yana jiran ta idar da sallah.
Inna na sallama tayi aduo'inta tare da gyara zamanta. Juyowa tayi tana kallonsa ɗauke da murmushi a fuskarta."Ammar an dawo?".
"Ehh na dawo Inna, na sameki lafiya?"."Lafiya lau Ammar". Ta faɗa tana yi masa kallon tsab kafin ta sake cewa,"Lafiya dai na ganka wani iri?".
"lafiya lau Inna, gajiya ce kawai".
"Allah sarki to Allah yayi maka albarka, bari na kawo maka abincinka, nasan har da yunwa babu abinda kaci tun safe".Tayi maganar tana yunƙurawa zata miƙe.
Shi kuma yana kallonta da so da ƙauna gami da tausayi yace,"Inna an samu abun dafawa ne?".
"Ehh wallahi an samu, da ke ɗazu Halima ta zo ta kawo min, abunka da wanda ya dogara da Allah ba ya taɓa tozarta. Ku kuwa dama babu abinda zan ce da ku sai Allah ya biyaku da gidan Aljannah ya albarkaci rayuwarku, yanda ku ka ji ƙaina ubangiji yaji ƙan ku ya ba ku masu jin tausayin ku".
"Amin Inna, ke ma Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana".
Abincin ta zubo masa shinkafa da wake ne da mai da yaji. Ya fi dai babu amma ba zaka ce an zuba mai ba, ita kanta shinkafar dan kana hasko ƙyallin kan waken ne da ba zaka ce akwai wake a ciki ba, dudu bai fi loma biyar ba. Ya tashi yaje ya wanko hannunsa tukunna ya zauna ya soma ci. A wannan ɗan guntun abincin da ko cikinsa bai gama tsargawa ba yay gyatsa da hamdala. Inna na kallonsa kawai ta girgiza kai, loma uku kawai yayi ya bar sauran, ta san ba wai ya ƙoshin ba ne kuma ba ƙoshin ne yasa shi yin gyatsar ba, kawai yayi ne don ta ɗauka cewar ya ƙoshi sosai, batun ta ce masa ya cinye sauran ma kuwa bai ta so ba.
"Alhamdulillah. Allah ya ƙaro na kullum kullum".
"Amin ya Allah". Cewar Inna.Kallonsa ya mayar ga Hidaya da ke maƙale a bakin ƙofa tun shigowarsa, taƙi zama kamar wadda ta aikata rashin gaskiya sai faman noƙe noƙe takeyi, ta marairaice fuska tana neman fakar idon su ta fice fit yanda ta saba.
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.