🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*SHAFIN NAKU NE HAJARA SHARIF,HUSAINA AND FATIMA ALIYU*
*40*
Door bell ɗin da aka danna ne yasasa buɗe idanuwansa dake rufe kaman mai bacci.
Hannunsa ya miƙa ya danna ƙaramar bell dake kan table nasa wadda ke nuna alama na sada saƙon shigowa.
Ƙarar data maida ne mutumin dake tsaye bakin ƙofar ya buɗa ya shigo.
Da rissinawa ya miƙa file ɗin daya shigo dashi a hannunsa tare da cewan,
"Sir gashi dukkan wani bayani da kake buƙata yana ciki"Amsa yayi ya ɗago ya kallesa ,"oak" ya maida dubansa ga file ɗin.
"amm Sir buh for the....."
Dakatar da maganarsa yay da ɗaga masa hannu yace ,"go i will look for you later"
"oak sir ,thank you"
Da fitarsa ya buɗa file ɗin ya duban da zaiyi ya rufe yasa a drower.
Wristwatch ɗin dake maƙale hannunsa ya kalla 1:05pm, miƙewa yay da hanzari ya shiga toilet ɗin dake ciki yayo alwala tukunna ya fita.
Yana fitowa mai kula da office ɗin nasa ya shiga ya fara gyara abinda zai gyara ya fito tare da ƙullewa.
Fitowar Accountant Farooq Adam Modibbo kowa dake cikin bank ɗin ya dinga rissina masa ana gaida shi.
Da sakakkiyar fuskarsa da bata nuna ɓacin rai ko damuwa ya ɗaga masu hannu da jin daɗin yanda mutane ke sonsa.
Fitarsa ya tadda ma'aikata kowa yay alwala wasu har sun shiga masallaci wasu kuma nakan yi shi kawai ake jira yazo ya ja salla.
Sauri ya ƙarasa ya shiga masallacin nan yaja ma ɗinbin mutanen dake bayansa sallah .
Da iddawarsu bayan yayi adu'oin dazaiyi ya fito tare da nufar haɗɗaɗiyar motarsa mai shegen tsada ƙirar GBox White ,da sauri drivernsa daya hangesa ya taso ya buɗa masa gidan baya ya shiga ya zauna.
Sai daya tabbata daya zauna comfortable tukunna ya rufe ya zago da sauri yama motar key.
Security ɗin dake sanye da kayan sojoji jikinsa a bakin gate ya miƙe tare da ƙarasowa , umarni yabama drivern daya zage masa glass na baya.
Kaman yanda yace yay shi kuma ya nufa ta side ɗin da Farooq yake wanda kuka fi sani da Ammar a baya yace, "sir i think you should follow the gate back becouse there are so many beggers here out side waiting for you to come out"
Agogon hannunsa ya kalla yaga har to 2 dan haka ya bama drivern umarni daya koma ta gate ɗin baya gudun karya fita mutane su ɓata masa time dan a matse yake da yaje gida.
Ba da gudu ba kuma bada sauri ba drivern ke tuƙin kaman yanda mai gidan nasa yafi so har suka iso ga Rosling estate Modibbo Street.
Manyan gidaje 5 ɗin dake jere a layin ya nufa na tsakiya wanda shine tanfatsetsen cikinsu ya dannawa horn da sauri tsohon mai gadi ya taso ya zage dogon gate ɗin,
danna hancin motar zuwa ciki yay, part kusan shida ne ya nufi na tsakiyan dake kewaye da glasss door yay park ya zago ya buɗa ma Farooq ƙofa ya fito sannan ya ɗau sabuwar doguwar tafiya zuwa ciki inda ake aje motocici.

VOCÊ ESTÁ LENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficção HistóricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.