🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
The page is dedicated to you bayin Allah masu son novel ɗinnan.
ZARAH DARMA.
MAMAN HAYDAR.
JAMILA GOJE.*65*
Itama da sauyawar fuskar ɓacin ran maganarsa ta dubeshi tace,
"ƙarya kake abinda bazai taɓa yiwu ba ka kira soyayyar da kayi mani a matsayin ta ƙarya ,dan haka ko ko faɗa ko karka faɗa soyayyata nanan acikin zuciyarka bazaka taɓa daina sona ba, dan haka mu bar wannan wasan bana so"
Gemunsa ya shafa ya nunata da hannu sama da ƙasa.
"ke awa na baki zuciyata, ƙarya ne wlh bana sonki bana ƙaunarki na tsaneki na tsani duk wani abu dazai haɗani da ke...wai ko kin manta da cewan so tsuntsune yakan tashi daga wannan bishiyar ya koma wadda yaga dama to kema hakan take kanki tini tsuntsun soyayyata ya tashi daga kanki ya koma kan Sadia macen data zama rayuwata gaba ɗaya"
idonta runtse tana zubda zafafan hawaye zuciyarta na wani irin bugu ta shiga tinanin kalaman da yay mata sak wanda ta watsa masa abawa.
_na tsaneka bana sonka,ko ka manta so tsuntsu ne tini soyayyata ta tashi daga kanka ta koma kan ubaid_.
"Hamma dan Allah karka daina sona ,ka ƙaryata abinda kunnuwana keji daga bakinka bazan iya rayuwa babu kaiba"
Ta furta da murya a raunane jiki sanyi ƙalau dan duk abinda ya faɗa fuskarsa da idanunsa sun tabbatar.
Kallonta yay yana mai tina furucinsa a lokacin da tsanarsa ke yawo a zuciyarta.
_Noor dan Allah karki daina sona ,ki ƙaryata abinda zuciyata ke faɗi game da hakan bazan iya rayuwa babu ke ba._
Dogon tsoki yaja ya bita da idanunsa da suka rine zuwa ja tsabagen ɓacin rai,iskar dake fita daga bakinsa mai zafi ya sauke saman fuskarta datake kallonsa.
"koda mata sun ƙare a duniya bazan taɓa janyoki cikin rayuwata ba,dan baki cancanci macen dazan haɗa inuwa guda da ita ba,ko kin manta bana da arziƙi da lafiyar dazan iya zama dake"
Hannu tasa ta damƙe gaban rigarsa tana kuka mai cin rai haɗe da girgiza masa.
"karka mani haka dan Allah in ba haka ba zuciyata zata iya samun matsala,dan Allah karka ce bazaka aureni ba karka ce ka daina sona....."
Watsar da hannayen nata yay da zafin nama,
"idan na aureki nace na auri me? ragowar wani ko kuma me ,to sam baki dace dana haɗa jiki dake ba"
Da mamakin kalamansa tabi fuskarsa da kallo.
_ragowar wani._"Hamma ragowar wani fa ka kirani"
"ƙwarai kuwa ko kinsha ban san komi ba, dan haka babu abinda zanyi dake can dai kije ki nemi wani daidai dake amma bani ba"
"tsautsayi ne dnt blame me akan abinda baka da tabbacinsa, ƙaddara ce na fika jin zafin hakan, Allah ya shirya mani zan fuskanci hakan arayuwata"
Murmushin takaici yay kamin yace,
"gurguntar data sameni tsautsayi ne bayin kaina bane hakana talaucin da ya same ni Allah ya shirya cewan zan fuskanci hakan a rayuwata"
![](https://img.wattpad.com/cover/188462047-288-k516781.jpg)
VOUS LISEZ
HIDAYAH NOOR completed.
Fiction HistoriqueHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.