Page 76.

919 68 3
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


         *Story~Written~Edited*
            *_By Miss Xerks_*🌺

         *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...



*76*

Nufarsa kitchen ya buɗa babban kwalin indomie ya ɗauko ya fasa kwai ya soya masu ita da haɗin pepe da taji.

Ruwan tea daya sha kayan ƙamshi ya juye a flask ya soya bread shima da kwai.

Akan tray ya jera ya fito parlo ya aje anan dining,harya nufa ɗakinta sai ya tina ba lalle ta fito taci ba nan ya juyo ya ɗauka ya wuce dasu zuwa ɗakin nata.

Tana yanda ya barta bata tashi ba barcin take a nutse kai da gani kasan yana mata daɗi.

Kan madai2cin table dake aje gefe yaja ya aje tray ɗin sannan ya nufeta tare da shafo fuskarta yana sakin murmushi.

Agogon dake manne jikin bangon ɗakin ya kalla 10:30 hakan yasa ya zage coten hasken rana ya shigo ya haske fuskan Hidaya aifa nan ta fara matse ido tana karewa da hannunta.

Bai saki ba har saida ta miƙe zaune tana yamutsa fuska.

Ganin yanda dakin  ya ɗanyi duhu daga hasken daya ke ta ɗan buɗa idanunta suka sauka akansa dake tsaye yana kallonta da murmushin jin daɗi kwance a fuskarsa.

Ɓata rai tayi gami da saurin jan blanket ta rufe jikinta.

Kusa da ita ya zauna saman gado yace,

"Amarya barka da safiya"

Bata tankasa ba sai juyar da fuskanta ɗayan gefen tai.

Numfashi ya sauke yace da ita, "ki tashi haka ki break fast kinga rana tayi kuma daren jiya baki sa komi acikinki ba"

Sama da sau goma yana magana amma ko iskar data ɗaukosa ta kawosa bata kalla ba ta maidasa tamkar mahaukaci sai magana shi ɗaya yake yana bama kansa amsa.

Ganin bata da niyan amsa masa ya miƙe yace ta tashi tai wanka ga abinci nan ya aje mata sannan ya fita zuwa ɗakinsa shima dan yasan idan har yana nan toko zasu kwana haka bazata motsa ba.

Da banzar harara tabisa gami da doka uban tsoki tukunna ta sakko tana ƙunƙuni cikin ranta ta faɗa toilet.

Zafin datake ji ne kawai zai sata yin wanka bawai dan bin umarninasa ba kaman yanda yace.

Bata jima ba ta fito ko shafa mai batai ba sai humra data saka sannan ta buɗa wadrobe ta zaro wata doguwan rigan atamfa ta zira sannan ta ɗaura ɗan kwalinta ɗaurin ƙullin magani.

Tsaye tai tana ƙarema ɗakin kallo kamin daga bisani hawaye ya biyo kuncinta.

Mai yasa su Baffa zasuyi mata haka,mai yasa suka bata wanda bata so bata ƙauna bata jin zata sosa koda watan wataran,wlh dashi da suka bata ƙwamma ace kasuwa yaje yay shelarta,shin har tsawon shekara nawa zata ɗauka kamin taji daɗi a rayuwarta.

Cikinta ne ya murɗa da yin ƙugi hakan ya tabbatar mata da yunwa take ji Ba ƙarama ba kuwa,hamma ta yunwa tai sannan ta nufa kayan abincin dake aje.

Flask ɗin ta buɗa ta yatsina fuska,tsoki taja da cewan Allah ma ya kiyaye taci abincin gidan maƙiyinta,zatama Baffa waya akawo mata kayan abinci.

Sose take jin yunwa acikinta dan tin safiyar jiya rabonta da abinci har ruwa gashi bata iya jure yunwa jiyanma dan taro ne yasa, gefen gadon ta zauna tana tinanin abinyi dan yunwar daɗa ƙwaƙularta take amma da dai taci wannan abincin ƙwamma ta shekara bata sa komi acikinta ba.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now