🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''KUMA GA NAKU RAZ NOVELLA 2,SOSE NAKE JIN DAƊIN COMMENT NAKU ACI GABA DA GASHI UWAR ƊAKIN HIDAYAH NA ƘAUNARKU WALLAH'''
*14*
Wayewar gari bayan da Ammar ya gaida Adda yake ce da ita yanzu gobe mai zasu dafa na sallah.
Ehh to tace dashi "kasan banice da wannan ba sai abinda Inna tace"
To yace ya koma ɗaki ya ɗauko bankinsa tare da wuƙa ya fafe shi.
Kuɗin dake ciki ya ɗebo ya kasa uku,1 yasa a aljihu,ɗaya ya bama Adda yace ta sayowa Hidaya mayafi da takalmi da sarƙa abinda yay ragowa kuma kuɗin mayafinsu ne ita da Inna.
Godia Adda tai masa tana Allah ƙara tabbatar da soyayyarku kaida ƙanwata,ya kuma daɗa buɗamaka a sana'arka.
Ɗayan ragowan dubu ɗaya da ɗari biyar ya nuna mata yace to zai kaima Inna na kuɗin dahuwar salla ne.
To ka gaisheta inkaje tace dashi tana murmushi.
Kasancewar azumin da ake yau ba kayan kari ya tafi,yana tafe yana ambaliyar murmushi burinsa kawai ya shiga gidan yaga Hidaya.
Da shigarsa ko ya tarar da ita ta fito daga wanka jikinta duk ruwa sai ɗaurin ƙirjin dake jikinta tana daɗa ɗauraye fuskarta.
Kasa motsawa tai saboda kunya dan ɗan kwalinta ta ɗaura kuma ko gwiwarta bai rufe ba.
Shiko da sauri ya runtse idonsa ya kauda kai gefe guda,abinda yake gudu kenan azuminsa shiyasa kwatakwata bai son bayyana soyayyarta acikin azumin dan shi yana da matsala abayan ma ya aka cike daurewa kawai yake.
Runtse ido itama tai ta tafi da gudu tayi ɗaki.tsaki Inna tai ta ɗake ta tana faɗan kinsan ai da sanyin saiki ƙi neman babban abu ki rufe jiki ki sai kin fito ki dinga faɗo mani kamar wadda kura ta biyo.
Dariya tayi ta dafa kan Inna tana yi haƙuri hajiya ta mishkila aka samu.
Ko tsanewa bata gama yi ba ta zira kayanta dan Hamma na waje na jiran zai shigo.
Ta window ta leƙa ta hangesa jingine da bango da idonsa a rufe. _Hamma na_ ta faɗa aranta.
Wurin Inna ta dawo ta zauna kusa da ita inda ta kamata ta rungume harda mata sumba tana cizon leɓe.
Kallonta Inna kamayi,"shaƙiyancin yau kuma akaina zai ƙare ya bar Haliman knn"
"UmUm Inna soyayyarki ce take ƙara ƙaruwa cikin raina,naji daɗin haifata da kikai ina sonki Inna ta Allah ya bani ikon faranta maku kaman yanda kukai mani"
Amin Inna tace Allah kuma ya nunan ran auranku gaba ɗayanku ba.
Da murmushi Hidaya tace amin,rope ɗin data lakuto ta ƙarasa shafa ma Inna shi aƙafarta mai ciwo.
Can ganin shiru2 Ammar bai shigo ba tace da Inna," Hamma fa na tsakar gida tin ɗazu dana fito daga wanka"
"Tsakr gida kuma?mai yake to bai shigo ba"
"Nima ban sani ba,yana dai tsaye"
Ammar Inna ta ƙwala masa kira,bai jita ba saidata kuma kiransa ana biyu sannan ya amsa.
VOUS LISEZ
HIDAYAH NOOR completed.
Fiction HistoriqueHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.