🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By MiSs Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*NIDAI TYPING ƊIN YAU NAYI NE DAI KAWAI SABODA ƘARANCIN TIME DAN HAKA IN KUNCI KARO DA BA DAIDAI BA KUYI HAƘURI,AMMA BA LAIFINA BANE NA MASU KIRAN WAYANE INDA HUKUNCI KUYI AKANSU*...
*73*
Sosai hawayen dake cike da nadama ke sauka daga fuskar Mansur.
Gaba ɗaya yama manta da a inda yake sai da Mu'azzam ya dafasa tukunna ya ɗago ya dubesa da idonsa da sunkai jawur.
"Sir a filin makaranta kake kuma ga student natai kai komo ya kamata ka miƙe kar raini ya shiga tsakani"
Goge hawayen yay yace mashi ya gode.
Mu'azzam zai miƙe yace dashi, "kaman tare na ganku da ita ko, ka santa ne?"
"ehhh nasanta abokiyata ce"
"dan Allah aina zan iya samunta?"
"ehhh to a hostel take zama amma gaskiya idan har samunta zakai ayanzu inaga zaifi kyau ka haƙura domin tana da miskilanci ga kuma tsinan taurin kai"
"to shikenan babu damuwa,ka dai tabbata da a hostel take ko?"
"ƙwarai kuwa tana room 1 sunanta...."
Hannu Mansur ya ɗaga masa, "basai ka ƙarasa ba na san sauran bayanan"
Motarsa ya nufa ya shiga ya tada ta shi kuma Mu'azzam ya kaɗa kai ya wuce gaba.****
Hidaya ko tinda ta koma hostel kuka kawai take,inama da ace ta mutu ta huta,sai yaushe zataji dadi ne ita kam.
A duk faɗin duniya babu mahaluƙin data tsana sama da Mansur saboda ya ruguza mata rayuwarta,duk farincikin datake ciki idan ta tinasa ƙunci ke ziyartarta.
Mai yasa sai ayanzu data fara jin daɗin rayuwarta kuma zai dawo cikinta,har abada bazata taɓa yafe masa ba.
Shigowar Maryam ɗakin zaune ta sameta kan gadon kanta cikin cinyoyinta.
"Hidaya wai meke faruwa ne dan Allah ki daina kukan kimin bayani"
Kumburarun idanunta ta ɗago ta dubi Maryam, "babu mahimmancin kisan komi bana son takurawa" daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin.
Fuskarta ta tsaya ta ɗauraye a famfo tare da ɗora alwala sannan ta zira hijab ɗin dake hannunta ta wuce masallaci.
Tana shiga ta wuce drower ta ɗauko ƙur'ani ta zauna ta shiga karatu.
Tinda ta fita Maryam ta zauna tai shiru tana tinani to mai hakan ke nufi maine tsakaninsu.
Allah ya kyauta tace ta miƙe zata fita kiran Mu'azzam ya shigo wayarta.
"hellow Maryam"
"na'am Mua'azzam ya akai"
"ya kukai da hidaya?"
"ummm na tambayeta batace mani komi ba illa cewa datai na ƙyaleta babu ruwana""kai Hidaya badai taurin kai ba,shikennan Allah ya kyauta sai anjima"
"uhmm sai anjima"
Bayan katse wayan ta fito ta ɗora alwalan magriba dan anyi kiran sallah.koda ta idar ta ɗauko littafi tana karatu sai taga bai dace ace ta bar Hidaya ahaka ba cikin damuwa dole duk masifar da zatai ta bita taji koma mine.

VOCÊ ESTÁ LENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficção HistóricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.