Page 31

1.1K 86 4
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


           *Story~Written~Edited*
              *_By Mrs Xerks_*🌺



          *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الحمن الرحيم...


*Masu roƙona akan dan Allah na juya abubuwan dake faruwa zuwa mafarki har mutuwar Surry saboda kar hawan ruwansu yay nasarr tashi...to ina mai baku haƙuri ku ciga ba da binsa ayanda labarin ya tsaru tin farko*

*31*

"Wlh idan da sunan dayafi butulu Hidaya dashi ya dace akiraki,banza wadda bata san halacci ba,wai dama wannan shine irin halaccin da kike ikirarin zakiwa Hamma...banda zamanki dasu kyama kallu a idon duniya ne bare harshi Ubaid ɗin ya kalleki yace yana so ,shashasha mara hanakali da zurfin tinani"

Ɗaga mata hannu Hidaya tai ranta ɓace ta dubi Sadia da tin zuwanta take tsaye ta kasa zaune saboda takaici.

"kinga malama baki isa kice zaki shigo mana har gida kina gayan banzar magana akan wasu ba...dama ba tin yau nagane kina baƙin ciki da duk abinda zan samu ba"

"aikin banza baki da abinda zanwa baƙin ciki ai,mai kike dashi mai kika tara babu wlh idan fanni dukiya ne sanin kanki ai ta mahaifina ta zarta na wannan wanda kike bara ƙarƙashinsa, abu guda kike dashi wanda zan iya baƙin ciki dashi shine iliminki da kika samesa silar matalautan da kike walaƙantawa"

"hmmm kin san mai nake so ki fahimta,ni Hidaya nafi ƙarfin auren talaka wlh domin ba kalarsa bace ni bare kuma auren mai nakasa biyu talauci da gurgunta....ke na ƙwammaci ƙarasa rayuwata babu miji da dai na auri Ammar domin baida arziƙin da zuciyata ke so bare na zauna dashi dan ni ba kalar wahala bace"

"hmmm lalle ne, a dai irin atalaucin nasa kika samu ingantaccen ilimin da kike fariya dashi ayanzu har kike ambaton zaki fita wata ƙasa, a ƙarƙashin talaucin nasa kuka samu rufin asirin da mahaifinku ya nemi ya tona maku, banda su cinku ,sitirarku ke da duk wani jin daɗi naku Kwa samu ai da tini yanzu kunanan kan titi kuna yawon bara kaman timaki baku da wani gata"

"hhhhh naji da wannan kawai za'a iya goronta mani kuma ayanzu kisani ina da mafificin abinda suka mani dan haka idan suna biɗar na biyasu ni mai iya biyace"

"ariziƙi na Allah ne hakana talauci na rabbu ne, duk wani abin duniya mai ƙarewa ne,na tabbata dasune bazasu taɓa gudunku haka ba amma munan dake ki rubuta ki aje wataran sai kunyi nadamar abinda kuka aikata masu domin kuwa haƙƙinsu bazai taɓa barinku ba....da masu wadatar zuciya ake ado "

"duk da wadatar zuciyar tasa mai na taɓa nema na samu alokacin danake biɗa kullum sai dai ace maka sai an samu,babu babu kaman tai fito ajikinmu,ke karki manta fa ma'aiki da kansa yace mu nemi tsari da talauci to akan me kuma hanyar buɗi ta sameni sai na ƙi "

"Allah sarki su Adda,Allah ka dubi bayinka suma ka wadatasu da abinda kake ganin zai zame masu mafi alkhairi...Hidaya ina jiye maki ranar dazaki kukan dazaki ji kaman ranki ya fita dan wlh da auren wani mai kuɗin ƙwamma auren talaka, bana maki fatan rasa Ubaid Allah ya barki dashi"...

"wannan aduar ai ita mahaifiya ta ke mani kullum wadda kinsan karɓaɓɓiya ce dan haka bana buƙatar taki"

Numfashi Sadia ta sauke ta ƙara duban ƙaton ɗakin da Hidaya ke ciki.
Tabbas bata ga laifinsu ba duk wanda ke acikin irin halin dasuke bazaiƙi amsar wannan tayinba.

"ni na tafi bakuma lalle ki ƙara ganina ba domin kuwa ko bikinki bazan zo ba dan hakama kar naga gayyatarki"

"agaida na gaba" tai picking call ɗin Rashida .

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now