Page 77.

1.3K 97 10
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


         *Story~Written~Edited*
           *_By Miss Xerks_*🌺




       *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*




بسم الله الرحمن الرحيم...


*77*

Duk wani nau'ika na kulawa da ja ajiki Mansur yayi wa Hidaya amma ina abinma kaman yana tirata ne kan taƙi sa.

Iyaka damuwa ya shiga damuwa dan in zai kwana yana mata magana bazata taɓa basa amsa ba talkless of kallonsa.

Kallo ko in ya haɗasu kallon walaƙanci ne,gashi duk abinda take masa point na sonta bai ragu acikin zuciyarsa ba sai ƙaruwa da yake.

Duk abinda take yana jurewa ya haƙura amma banda wurin cin abinci,idan ya dafa ya kawo in ya fita yanda ya tafi ya barsa hakana zai dawo ya samesa sai ya mata ɗura yanda ya saba tukunna take cin abinci har tsawon wata guda suna ahaka.

Kwance yau ya shigo ya sameta tana barci,gefenta ya zauna yana kallonta yana mai jin daɗi cikin ruhinsa.

Kiss yay mata a goshi gami da kamo hanunta ya sanya nasa ciki yana jin ɗumin nata.

Kaman a mafarki taji ana murza mata hannu hakan yasata farkawa, tana buɗa idonta ta gansa zaune yay ƙuri yana kallonta.

Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ɗaure fuska gami da jan tsoki ta ziro ƙafa zata sauko daga gadonta,miƙewarta tsaye yasa shi janyo hannunta ta dawo ta zauna.

"Haba Hidaya,yanzu fisabilillahi abinda kike ya kyautu kenan,nifa mijinki ne,dan Allah ki sauƙaƙa ma zuciyarki karki dinga barima shaiɗan mafakar samun zama acikinta"

Hawaye ne ya cika idanunta fuskarta da alamun zatai kuka.da sauri ya shiga lallashinta yana bata haƙuri ganin bazai samu yanda yake so ba ya tashi ya fitar mata a ɗakin dan ya lura sam bata son ganinsa.

Fitarsa ta share hawayen daya zubo mata,drower taja ta ɗauko wayanta nan ta kunna data ta hau online,tai sa'a Sadiya da Maryam suna online nan suka shiga hira.

Maryam ke tsokanarta, "aa ke madam wai har yau baki harbu bane naji ba wani news,watanki guda fa harda sati"

Tsoki Hidaya taja mata a rubutun tace, "baki da hanƙali"

Dariya Maryam tai kawai nan suka shiga hiran makaranta kuma tana tambayan Hidaya yaushe zata dawo tace sai mijinta ya sake ta,Maryam ta kwashe da dariya tace ashe ma banice mahaukaciyar ba kece nan Hidaya taji haushi ta daina kulata suka koma hira da Sadia tana cewan dan Allah tazo tace zata zo amma sai sun shigo garin.

Tana ta chart ɗinta Mansur yay sallama riƙe da tray na abinci hannunsa nan yaja yable gabanta ya ijje ya juya ya fita.

Da harara tabi abincin jin kiran sallar la'asar ya sata miƙe,kayanta ta cire saboda zafin da ake bugawa ta shiga wanka.

Fitowarta shigowar Mansoor,saurin rufe idonta tayi ,shi daya tsaya yana niyyan ƙarasa shigowa ta dakatar dashi cikin tsawa a hasale tace dashi,

"wannan wanna irin hauka ne zaka shigowa mutane ɗaki babu neman izini,to ka juya tin wuri"

Da ido ya bita bai taɓa jin haushinta ba sai ayau, "hauka" ya maimata cikin ransa.

"Hidaya ni kike nufin ina hauka"?

"to in ba hauka ba mine,ko baka da masaniyar annabi yace kamin ka iski rumfar mutum bayan sallama ka nemi izini tukunna kamin ka tutsa kai ciki"

"ƙwarai kuwa nasan da wannan,amma inace ni ai ɗakin matata ne ko,duk a halin dana shigo na risketa babu laifi aciki"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now