Page 32

1.1K 86 10
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



         *Story~Writen~Edited*
           *_By Mss Xerks_*🌺



       *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...

'''KUYI HAƘURI DA MISTAKES ƊIN DAZA KU CI KARO DASU DOMIN TYP ƊIN YAU SAURI SAURI NAYI SHI SABODA BANA SON KUYI MISSING.'''

*32*

Cikin kuka Sadia ke bama Umma labarin irin cin mutuncin dasu Inna kewa su Hamma.

"Inna in kika gani sai kinyi masu kuka,wlh rannan danaje gidan wai Adda ce taje wurin Inna nema masu abincin daza suci haka ta korota wai ta fitar masu daga gida...kai anya Umma bada asiri aka masu ba dan wlh Hidaya na ƙaunar Hamma son kuma da bazata iya rabuwa dashi ba komin wahala"

" babu zancen asiri inma shi ɗinne to ya haɗu da hali...ki barsu indai rayuwa ce ta duniya ai ta ishi kowa riga da wando dan na tabbata hakkin ma yarannan bazai barsu ba"

"ni Umma ban taɓama ganin rashin halacci irin wannan ba ,kuma insha'allahu suma zasu ɗaukaka wataran tinda su da Allah suka ɗogara bada abin dake cikin duniya ba"

"Allah dai ya kyauta amma gaskiya abinda sukai sam basu kyauta ba, kuma wannan shine ainin halinsu yanzu ya fito fili ƙarara"

"Umma ni ina ma tausaya ma Hamma da abinda Hidaya take ƙudiri yimasa dan tace sai tozarta shi a idon duniya saboda yanzu ba mutumin data tsana a duniya kamarsa gashi kuma ƴar uwarsa ta kuma ja masa da marinta datayi"

"Babu abinda ta isa ta masa babu abinda zai sameshi domin Allah baya tozarta bayinsa irin waɗannan"

        ****

"wlh Inna ban taɓa tsammanin haka daga gareki ba, yau inace koda wasa kika ga wani zai walaƙanta su Ammar ai sai inda ƙarfinki ya ƙare amma keda kanki kece ke aikata hakan garesu bayin Allah nda suka ɗaukeki tamkar uwar data haifesu suka ɗauki ƴarki kamar wadda suka sakarma nono gaskiya Innan Hidaya baki halacci ba kuma indai da gaske kike to kinyi butulci wlh"

Numfasawa Kawu yayi ya gyara Babbar rigarsa,
"Gaskiya kwatakwata abin bai daɗi ba kam,domin su Ammar ƴaƴa ne na halak ɗawainiyar da sukai daku basu cancanci wannan sakayyarba,koda garin nan kuka mallaka baki ɗaya idan kukai kyautarsa garesu baku faɗi ba ba kuma ku biyasu ba.....ya kamata ku sauya tinani ku tausayawa marayun yarannan....."

Da faɗa Inna ta ɗagawa Kawu Hannu alama na ya dakata.
"kaga ya isheku daga kai har matar taka. Kaga kai ina ganin mutuntakarka bai kamaci ace kana shigowa lamuranmu ba dattijo dakai...wannan ma ai nuna baƙin ciki ne ƙururu saboda kunga ayanxu munfiku shine duk kuke takaici kunfi son kuga rayuwarmu kaman da cike da ƙunci ,kowa sai tsinan munafurci acikinsa"

Ran Malm Shu'aibu ɓace ya miƙe yana bula babbar rigarsa ya dubi Kawu da Ammaa.

"kaga ku tashi mu tafi...taje tayi duk abinda take ganin dai2ne tayi indai duniya ce zatagani ta isa kowa riga da wando harda zanen ɗaurawa.....ke kuma"

Ya nuna Umma Zakiya dake zaune hakince kan kujera,

"keda kika zama ummul aba'isin komi kamin duniya ta tozartasu ke zata fara tozar tawa, munafukar banza da wofi...."

"kaga mai gida ka daina zagina fa ,ni dama ba tinyau kaima na lura dakana baƙincikin tarayyata da Zaliha ba ,ka hanani samun arziƙi ta ɓangaren ƴaƴana shine yanzu dan nasamu ta wani ɓangaren shima sai kayi baƙinciki"

HIDAYAH NOOR completed.Onde histórias criam vida. Descubra agora