*HIDAYAH NOOR*
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@Arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya**(4)*
Kiran asuban fari Hidaya ta tashi daga bacci, wanda in haka kawai ne babu zumuɗin kayan makarantar da aka siya mata babu yacca za'ai ta tashi a wannan lokacin. Babu jiran Inna ta ɗora mata ruwan wanka ita tayi komai, ta saka kaya da takalmi har safa jaka kawai ya rage mata, burinta gari ya waye ta tafi makaranta. Daga jikin gadon ƙarfen nasu ta jingina take kuwa bacci ya ɗauketa dama bai isheta ba.Inna ma yau a makare ta farka, tana fitowa tsakargida ta fara salati ganin yacca rana ta ƙwale tarr. Kiran sunan Hidaya ta shiga yi amma bata tashi ba, ajiye butar hannunt tayi ta koma ɗaki ta shiga tashin Hidaya, ita kuma bacci yayi daɗi tayi juyi zata koma Inna ta ɗane ta da duka.
A firgice ta farka tana turo baki.
"Yatsina fuskar me kike, fita ki duba yanda rana ta fito kina nan kina faman bacci kaman muzuru, sai an zo an zaneki Yayunki su zo suna banbami saboda an taɓa ƴar gwal"."Kai Inna yanzu daga kwanciyar tawa har anyi safiya".
"Um um har yanzu dare ne ke dai ake jira sai garin ya waye. Dalla tashi ki kama gabanki nima ba son da duke kin nake ba".
Karayar da kai tayi kaman za tai kuka tace da Inna,"ban fa ci abinci ba ai".
"To me kika ajiye a gidan da za ki ci? Yau dai kam sai dai ki bari idan kin dawo kya ci dan wallahi nagaji da tashin Halima da ake da sanyin safiya girkin abincin makaranta kawai saboda ke. Yanzu ai ke ba yarinya ba ce ya kamata ki girma da kanki tunda su Yayyun naki ba zasu gane ba".
"To fa in ba aci abincin ba Yunwa bata barin mutum ya gane karatun".
Inna taja dogon tsaki tana barin wajen tana cewa. "Ke ki haƙura makarantar ba dole bace ai, dama zuwan naki ai asarar kuɗin tara ake yi, kuma da ba zasu shigo rayuwar mu ba ai karatun ba samunsa zaki yi ba shashashar banza da wofi ki ta zaman gida, ni bazan kai kaina inda Allah bai kai ni ba".
Tana turo baki gaba da shirin fashewa da kuka ta miƙe tana saka goya jaka. Kafin Inna ta fita a ɗakin tayi saurin shan gabanta tana cewa,"To ai baki mani adu'a ba".
Inna ta galla mata harara da cewa,"Kanki kike zumɓurawa baki ba ni ba". Dariya Hidaya tayi tana kama hannun Inna ta ɗora a saman kanta. Nan Inna ta fara yi mata adu'a,"أعوذ بكلمة الله التما،من كل شيطان وھما،ومن كل عين لماه".
"Allah kiyaye ya tsare ki a duk inda kika shiga, idan kika kula da kanki sai Allah ya kula da ke, ki mayar da hankali don Allah kinji, anjima zan kawo maki abincin idan an gama".
Hidaya ta ƙara yin siriritar dariya tana faɗin,"Inna kene ma za ki kawon abincin, to su waye za su barki? Ni dai na tafi ki gaishe min da Hamma da Adda".
"Zan faɗa masu Allah ga bada sa'a".
Tana buɗe ƙofar gida sai ga Ammar wanda ke niyyar kai hannu ya ƙwanƙwasa ƙofa.
Fuskarsa ta wanzu d murmushi ya tsaya kallon tsab wa ƙanwar tasa. "A'a Doctor to be har an shirya, shine za'a tafi ko ma a jira ni na zo muyi sallama, to koma ki fara cin abinci sai muje na kai ki".
Tana murmushi ta kai bakinta saitin kunnensa tana raɗa masa cewa,"Dama fa Hamma can gidan ku ɗin zanje, kar na faɗawa Inna tace kar na kuskura naje na tashe ku".
Sautin murmushinsa ya fito, hannunta ya riƙe suka koma cikin gidan. Inna na ganinsu bata ce komai ba don tasan duk abinda zata faɗa in dai akan Hidaya ta fita bata ci komai ba ne to Ammar ba zai ji ba don haka kawai t bisu da ido.
Koko da ƙosai ne yau aka yi lafiyayye, sai faten wake da Adda tayi mata mai zafi har da kifi na makaranta, farin ciki a wurin Hidaya kamar ta ɗauki kanta ta dire a makaranta.
![](https://img.wattpad.com/cover/188462047-288-k516781.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
HIDAYAH NOOR completed.
Fiksi SejarahHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.