Page 36

1.3K 78 1
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀




       *Story~Writen~Edited*
            *_By Mss Xerks_*🌺


         *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*

بسم الله الرحمن الرحيم...



*MAMAN SAYYADA TA KAINA,ALLAH YA RAYA MANA SU SAYYADA BISA TAFARKI NA GASKIYA*😍😘

'''ONE LOVE MY SANAZ DEEYAH❤'''


*36*

Tafiya suke suna tangaɗi daka gansu kasan sun galabaita da yawa.

Hidaya da tin tohowarsu take faman nishi ta zube ƙasa dafe da bayanta.

Inna datai gaba ta juyo agajiye ta kalleta.

"Hidaya taso mana kina ga fa yamma na daɗa yi ko so kike yauma mu daɗa fakewa a kango"

"Inna wlh na gaji ne ƙafata da bayana kaman su ɓalle"

Shiru Inna tayi tare da sauke numfashi ta dawo daga baya.

Ƙullin kwancen kayan da suka samu kwana ukun da suke gararamba ta kunce ta shimfiɗa zane a ƙasa.

"to zo ki kwanta anan kamin a kira la'asar mu ƙara tafiya"

Tasowa Hidaya tai a durƙushe ta kwanta kan zanen da Inna ta sa mata tare da ɗora ƙanta kan cinyar Inna ba jimawa bacci ya ɗauketa.

Sai da rana ta ɗan fara sanyi tukunna suka miƙe sukaci gaba da tafiya har suka bar anguwarsu suka shiga anguwar dutti.

"Wash" Inna ta faɗi yayin data tsaya ta kasa ci gaba da tafiyar.

Waigowa itama Hidaya tai ta kalla mahaifiyar tata da tausayawa tace, "kin gaji ne Inna?"

"Nagaji Hidaya kuma ga magriba tayi ina tsoron mu daɗa nausayawa ciki naga kaman maƙabar tace gaba, ƙwamma mu sami zauren wani gidan mu kwana ciki da safe sai muci gaba da tafiya dan bazamu ƙara komawa anguwarmu ba dan cin kashin da suka mana ya ƙona mani rai"

To Hidaya tace ta amsa ƙullin hannun Inna.

Sun ɗan jima nan tsaye kamin su waiga yamma dasu suka hangi wani gida mai ɗan gate suka nufesa.

Sun jima suna ƙwanƙwasawa tukunna wata ƴar budurwa tazo ta buɗe masu.

Gaishe da yarinyar sukai ta amsa masu tare da ce masu bismilla ku shigo.

Shigarsu Yarinyar tace "daga ina?"

Hidaya ce tace da ita "Dan Allah ƴar'uwa ina son zan shiga bayi ne na matsu"

Ɗauke da fara'a a fuskar yarinyar tace "tom bari na zuba maki ruwa"

Toilet ɗin dake tsakar gida ta nufa ta ɗauko buta ta zuba ruwa ciki tazo miƙawa Hidaya matar dake fitowa daga wani ɗaki tace,

"Rabi'a naji buga ƙofa ina sallah kin leƙa ne?"

"ehhh Mama na buɗe baƙin kan hanya ne wai zasu ɗan shiga toilet"

"baƙin hanya kuma ,ke waya faɗa maki yanzu ana wani saukar baƙin hanya kamar baki sauraron radio"

Mama ta faɗi da muryar faɗa ta zura takalmanta.

Tsaye tayi tana ƙare ma Inna kallo kamin ta maida kallon nata ga Hidaya itama ta ƙare mata kallo ta taɓe baki.

"Ina yini Hajiya" Inna da ƴarta suka faɗi tare.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now