🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*LAST PAGE NAYI MISTAKE WURIN PAGE NUMBER INSTEAD DANA SAKA 37 NASAKA 36twice so saiku ɗauke shi matsayin 37*
_Page ɗin naki ne Firdausi Muhammad Maman Khalipha,Hibba da Humaira Allah ya raya yara ina godia da nuna kulawarki_.
*38*
"Baka da hankali Mansur,maike damunka kasan mi kake faɗi kuwa"
Hajiya ta faɗi cikin tsananin ɓacin rai."Hajiya kinsan bazan maki ƙarya ba wlh wlh yarinyar nan ciki ne da ita kuma gatanan ki tambayeta kiji"
Nufar Hidaya tai da kanta ke sunkuye ƙasa zuciyarta na raɗaɗi jinta take inama ƙasa ta buɗe ta shiga.
Dafata Hajiya tayi da damuwa fal fuskarta tace ,"karki ɓoye mani ƴata ki faɗan gaskiya kinji duk da nasan abune mai wuya hakan ya zama gaskiya...shin kun taɓa samun saɓani tsakaninki da Mansur?"
Girgiza mata kai tai alamu na a'a.
"ya taɓa ce maki baya sonki?"
"umum" nan ma tafaɗi da girgiza kai.
"to faɗan gaskiyar abinda ke faruwa da gaske maganar daya ke faɗa gaskiya ne da cikin shege tare dake"
Runtse da ido gam hawaye suka shiga sintiri fuskar Hidaya.
_Bani da wata mafuta data wuce na ƙaryata hakan tinda bashi da wani evidence dazai bada dan nasan bazai taɓa cewa nasa bane kuma Hajiya bazata yarda da fasuwar auren nan ba._
Yawun daya taru bakinta ta haɗiye da ƙyar tare da ɗagowa ta dubi ɗimbin jama'ar dake wurin wanda kowa idonsa ke kanta yana sauraronta.
girgizawa Hajiya kai tai ,"a'a ƙarya ne"
A fusace ko Hajiya ta juyo ta bawa Mansur gigitaccen marin dasai daya sashi razana.
"uwarka yarinyar mutane tamaka dazaka nemi ka tozarta ta haka ,in baka sonta kace baka sonta mana basai ka ɓata mata suna a bainar mutane ba"
dafe da kunci ya ɗago ya kalla Hidaya ya watsa mata harara.
Hannu ya zura ga aljihunsa ya ciro wayarsa.
Numban daya nema ya danna ma kira bugu uku aka ɗaga.
"hellow Dctr idan kana kusa ina son ganinka yanzu dan Allah"Huci da kumburi Mansur kawai keyi yana watsawa Hidaya dake tsaye idonta kansa mugun kallo.
Kusan mintina goma da gama wayar tasa Likitan daya kira ya ƙaraso cikin hall ɗin nan idon jama'a ya koma kansa.
"Hajiya gashi nan kinfi sanin wane shi ki tambayesa kiji"
Maida dubanta Hajiya tayi ga likitan dake tsaye.
"shekaru sama da 25 Dr Lamir muna tare dakai nasan baza a haɗa baki dakai ba dan aci mani mutunci ba ,ka faɗi tsakaninka da Allah shin kasan wannan yarinyar"
Hidaya da duk ta ruɗe jikinta na rawa ta ɗago suka haɗa ido da Dctr.
"ehh Hajiya nasanta farin sani ma kuwa don kwanakin baya ma tazo kan azubar da cikin data ke ɗauke dashi nina bata shawara ta haƙura domin akwai risk atare da hakan"

YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.