Page 64.

1K 87 18
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                      🌀🌀🌀🌀🌀







           *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks_*🌺






          *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...


'''SHAFIN NA KUNE MY AUNTYS,WLH KUNFI ƘARFIN PAGE WURINA, FAƊIN YANDA NIKE JINKU CIKIN RAINA BAZAI MUSALTU BA:'''

MAMAN SAYYEED & NOOR.
MAMAN KHADY AND KHALEEPA.
UMMU IMRAN.
UMMU SUDAIS.
UMMU ABDALLAH.
MAMAN MAYEESHA.
NUSAIBA Y GIƊAƊO.
MAMAN BINTU.

Kuji daɗinku😘😍,Allah ya raya maku zuri'a a tafarkin tsira ya barku da mazajenku har gaban abadan da zaman lafiya cike da zunzurutun ƙaunarku a ruhikansu....


*_SIS UMMI AISHA INA MAI TAYAKI MURNAR KAMMALA ƘAYATACCEN NOVEL ƊINKI MAI CIKE DA ƊIMBIN DARASI WATO ƊAN ASALI,LITTAFIN DAYA ƘAYATAR DAMU YA NISHAƊANTAR DAMU ,LITTAFIN DA KAKEJIN TAMKAR KARKA DAINA KARANTAWA DAN DAƊI...INA MAI ROƘON ALLAH DAYA BAKI LADAN FAƊAKARWAR DA KIKAI GAMI DA YAFE MAKI KUSKUREN DAKE CIKI,MU KUMA YA BAMU IKON AMFANA DA FAƊAKARWAR DA MUKA SAMU.....SAI MUN SAKE JINKI A SABON NOVEL NAKI IDAN ALLAH YA BADA IKO_*.

*64*
             ****

"Hidaya ki shirya muje mu dubo Sadia ance bata da lafiya tana jin jiki sose"

"tabb Inna kije dai ke ɗayan amma ni ba inda zani"

"iyyee mikike to da bazaki ba, Sadia ce fa matar da mijinta ke taimakonmu"

"to Inna koma wace ni bazani ba , tinda dai idan naje ba sauƙin zan bata ba"

"amma kodai bata cancanci ki mata haka ba, tinda har kikaji Gwaggo Amina tana faɗin ciwon kinsan ba ƙarami bane, ki tashi muje ba jimawa zamuyi ba kuma da ita ce ma ai da tini tazo maki"

"nidai dan Allah Inna kawai kije dan bazani ba, nima ai danai nawa ciwon ko saƙon sannu bata aikon ba bare tazo dubani"

"hmmm ba lalle ta sani ba data sani ni na tabbata babu abinda zai hanata zuwa"

"to kingani sai ai 1,1 dan danaje dubata ƙwamma nai kwanan tsaye...Inna ki tafi karki jima Baffa yazo yana faɗa"

"dazaki sauƙewa kanki wannan ɗan banzan kishin da bahaka ba, dan idan kika tafi ahaka akwai matsala, dan haka ki tashi kije ki shirya dan Baffanki ce yay mu tafi tare"

Sam ƙin miƙewa tayi ta shirya sai ƙunƙuni take har Inna ta gama shirinta ta fito saiga Baffa ya shigo gidan.

Da mamaki yake dubansu da cewan, "auu har yanzu baku tafi ba, la'asar fa tayi kunsan bani son fitar yamma"

"ummm kaganmu dai yanzu muke niyya dake kasan munkai Mukhtar wurin mai bada maganin Yaye shiyasa,yanzu ma bamu jima da dawowa ba"

"yanzu sai dai da kuka yaye yaron nan, ɗan dako shekara biyu bai ƙarasa ba inace sai sunma wuce biyu ake yaye su ko,mtsswww Zaliha kema kina da matsala wajen biye ta yarinyar nan"

"To Baffan Yusufa ai in ka duba lokaci yayi daza'a yaye shi ɗin tinda makaranta zata koma"

"um to sai dai saboda hakan amma dai da kun ƙyalesa gab dazata tafin an yaye shi"

"wai ai dan ya saba kasan yaran da rigima in akai yayen bare shi dama ba'ai ba ya aka cika bare yanzu da akai ,tin fa da muka dawo yake tsala ihu sai da yay bacci muka sami sukuni"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now