PAGE 9

1.5K 134 2
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


             *Story~Written~Edited*
                  *_By Mss Xerks_*🌺


         *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...






*9*

Tom kawai Sadia ta iya cemata dan tasan abinda ta faɗa ba mai yiwuwa bane.

Tasha cewan zata bata labarinsu sai kuma taƙi.

Abinda yasa ma take son sanin da gaske ko su Adda ba uwa uba guda suke ba ,watarana suna hirar ita tace tana tsoron Yaya Saifullahi ya auri matar dazata so tana ɓata masa rai,dama a tambayeta ace wazata aura qlh datace ita .

Shine itama Hidaya take cewa nima kullum saina ma Hamma na adua'r nan,amma idan tina wani abu sai naji in lokacin yazo ni zan aureshi dan bazan taɓa ɓata masa ba.

Dariya Sadia tayi take ceda ita ke Hamman nai zaki aura waya gaya maki akwai aure tsakaninku, shine take cemata ai ba uwa uba guda suke ba.

Tin daga nan Sadia ke son jin labarinta amma har yau taƙi faɗa mata,dan ƙarya ne ace a yanzu awannan zamanin asami wanda zaiyi irin wannan ɗawainiyar dayake mata kuma babu dangin iya bare na baba.

Tafiyar suka cigaba dayi suna hira Sadiya na ita harta ƙagu ma akoma schl tasha labari.
Amebo Hidaya tace da ita tana dariya.
Har gidansu ta rakata nan ma suka ɓarke da sabuwar hirar Yaya Saifullahi.

Gab da kirayen Magriba tayo gida har tana haɗawa da gudu dan tabbas yanzu Hamma na hanyar dawowa.

Aiko tai sa'a dataje bai dawowa ba sai dai tasha faɗan Inna.

Ɗan faɗan data mata yasa ta komawa gefe tai zamanta Inna na magana tai mata shiru.

Sai data ɗau carbi ta zabga mata sannan tai saita hankalinta.

Kan cinyar Inna ta dawo ta kwanta tana mata tambayoyi.

Shiru Inna taimata tana mai kukan zuciya.bata fasa tambayarta bama sai ƙara jefo mata wata tayi na cewan"to wai Inna shi Baffa na tsanarki tsanarki da yay  yasa ya gudu ya barki, gashinan yaja sai ƙaryar cewa ya mutu nake,shi kuma Yaya Yusuf ko sai yaushe zai dawo oho"?

Aiko nan take sai kukan Inna ya zama na fili,hawaye sose take nan hankalin Hidaya ya tashi.

Lallashinta ta shigayi har Ammar ya shigo.

Sallamarsa ce ta yanke jin Hidaya na ceda Inna dan Allah kiyi shiru ki daina kuka bafa kyau babba yana hawaye,kinga ke babata ce.

Bai san lokacin daya yar da ledojin hannunsa ba ya ƙaraso da ɗan gudunsa.

Gwalo ido yayi aruɗe ya shiga tambayar lapia mai ya sami Inna.

Ganinsa Inna tai saurin goge hawayenta tana murmushin dole.
Dafa shi tayi tana tambayarsa ka dawo.

Shima cikin hawayen yace da ita"Inna waya taɓa mani ke"

"ba kowa Ammar"
"to mai ya saki kuka"
"bafa komai nace maka,ya wurin aikin naka"

bai amsata ba ya maida kallonsa ga Hidaya datayi shiru tsiru da ita .
"me kikai mata"?
Ya faɗa cikin tsawatarwa.

aruɗe tace dashi "ba abinda na mata Hamma".

"Ƙarya ne,in bake ba to waya shigo ya taɓa mana ita"?

"kaga bafa wani abu bane,tambayata take Yusuf da kuma Babanta"

HIDAYAH NOOR completed.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora