PAGE 21

1.3K 97 1
                                    

🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                         🌀🌀🌀🌀🌀



         *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺



         *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*




بسم الله الرحمن الرحيم...


*21*

"mai yasa ummm,mai yasa haka Ammar....yanzu da kana son Hidayan kaja baki kamani shiru baka faɗan ba...wlh dana san da hakan da tini na jima da aura maka ita, Ammar bakai mani adalci ba na rashin sanar dani dakai da wuri....ashe mafarkin dana jima inayi zaizama dai gaskiya"

Wata bayyananniyar ajiyar zuciya suka sauke dukansu lokaci guda.wani daɗi sukaji ya ratsasu don da duk sun tsorata da yanayin data nuna.

Hawayen kuncin Inna tasa hannu ta goge.

Adda ce ta matso kusa da ita tasa hannu zata share mata ta kauda hannunta gefe,"barsu Halima ƙyalesu su sauka,bana takaici bane na farinciki ne...Na gode Allah na ƙara gode masa ban san ta yanda zan misalta murnata ba akan wannan lamarin ba"

Hannu Inna ta miƙa ma Ammar tare da kamoshi tasa shi jikinta kaman ƙaramin yaro.

"Na gode Ammar na gode maka Allah yay maka albarka ya ƙara ɗaukaka mani kai aduk inda ka shiga ya karen gaba da bayanka..Nasan bazan biyaku da godia ba domin kunfi ƙarfinta,ko Hidaya dazan baka wlh nasan ban biyaku ba...ayanzu ne nake da tabbacin zamanmu zai ƙara ƙaimi da ƙarfi domin nasan babu mai rabani daku,na jima ina tsoron kai aure wata ta rabani dakai..Ammar mai yasa tin farkon danake ɓaɓatun ka fidda mata baka faɗan Hidaya kake so ba kai shiru?"

Kasa magana yay saboda kunyar Inna dayaji ta kamashi.
Shirun nasa ta katse da "wato kayi zaton zance maka ban amince ba ko..hmmm to ai inaga nafika son hakan ta faru,abinn ya jima a zuciyata, bana son na zama na tirsasaka ne akan abnda baka da niyya babu kuma sonsa a zuciyarka shiyasa ban taɓa nuna maka alamar hakan ba dan ban san na zalinceka"

Bin Adda da Ammar tai da ido tana fidda murmushin jin daɗi,ƙwallar data kuma taruwa bisa idonta tai maida tukunna ta maida kallon ga Hidaya dake gefenta.

"ke kuma miye na kukan da"

Baki ta turo ta kalla Inna da sauri ta cusa kanta cikin cinyoyinta saboda kunya,"hankali na ya tashi ne inaji tsoron karki ƙi amincewa da hakan saboda alamunki da suka nuna"

"Hmmm dole raina ya ɓaci ai saboda banji daɗin ɓoye manin da kukai ba. Kuma duk kun mani gurguwar fahimta da kuke tsammani bazan amince maku ba..Hidaya tin kina ƙanƙanuwarki nake da muradin naga na haɗa auranki da Ammar,na jima ina wannan adu'ar wanda tin kamin rasuwar mahaifansu nake hakan saboda Ammar yaro ne mai hankali babu uwar da bazataiwa ɗiyarta sha'awarsa ba..."

Numfasawa Inna tai kamin ta ɗora,"ko kinsan na jima da fahimtar kina son Ammar"

Dukansu suka ɗago suna kallonta.
"ehh mana ai duk abinda nake na takuraki ki nemi mijin aure nai hakanne badan komai sai dan na kawar da Son da kike masa saboda shi ban lura da wanan alamar daga gareshi ba nai tinanin har yanzu soyayyar ƙanwace dai yake maki,hakan yasa nake ta ƙoƙarin yay aure shima da wuri ko kyasawa zuciyarki salama ki haƙura dashi...ashe muradin naku guda ne"

Ƴar dariya Adda tai tace,"ai Inna ni na jima ma banga masoyan dake son junansu haka ba"

"hmm ai ke kin kyauta da abinda kikai mani kinji,har ace yarann suna ƙaunar junansu da saninki shine baki taɓa mani zancen ba koda da wasa..bayan kinajina ina ɓaɓatun maganar aurensa da wata"

HIDAYAH NOOR completed.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang