🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Writen~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*_DEDICATED THIS PAGE TO YOU AMINATU NASIR MAMAN HUFAID Da HAFID kiyi yanda kike so dashi sai wanda kika ga daman bari ya karanta,tanz alot for your support and care..._*
*34*
Yau ya kasance laraba inda aka kawo lefen Hidaya akwati 6 banda bagco guda 2.
Kaya ne na alfarma aka zuba ciki dan ko wacce akwati taf take da kaya masu kyau da kuma tsada.
Dubu 100 Ubaid ya bama Hidaya dan ta gyara jikinta kawai banda dubu hamsin daban dayace tai lalle da kitso.
Zaune suke ita da Khadija da wata sabuwar ƙawarta Jauharatu sunata shiri akan yanda shagalin bikin zai wakana.
Jugum Noor tai kaman mara lafiya ko wadda aka ma wani abu da dai ka dubi fuskarta kasan da damuwa.
Jauharatu ce ta taɓota tare da ɗaga mata kai, "madam lapia dai tinanin me kike? bafa a son amarya da damuwa"
"wlh ban jin zan iya samun wata walwala a bikinn in babu Sadia..tin ranar friday nike kiran wayanta taƙi picking nai mata text sama da sau goma babu rply,online ma tayi block nawa gashi duk sanda naje Umma sai tace wai tayi tafiya kuma wlh tanan ban san mai yasa take fushi dani ba"
Da tsaki Khadija mai ɗauke da tiltsetsen ciki kwance kan gadon ta gyara zama tana hararta,
"Mtswww to uwarki ce ko ƙanwar uwarki da zaki bi ki damu kanki dan babu ita a bikinki..ko da ita ko ba ita biki sai munyi shi wlh"
Kallonta Hidaya tayi itama ta hareta da nuna ɓacin rai.
"ina jin Sadia ajikina sose tamkar ciki guda muka hito,wlh duk frnds ɗina nahi sonta kema Khadija kin sani kawai akansu wancan banzan Ammar ɗin muka sami matsala da ita haka kawai ya shiga tsakani na da Ƴar'uwata shege matsiyaci"
Ta ƙarasa faɗi da muryan kuka tare da miƙewa ta fita.
Ummm Khadija da Jauharatu sukace inda ko waccensu ta maida hankalinta ga kan wayarta.
Ɗakin Inna ta wuce inda ta sameta kwance tana barci,
Zama tai daga gefen gadon ta ƙara danna numban Sadia ta kira,har sau biyu tana ringing daga ƙarshe taji ma anyi swtchoff.
_da gaske dama Sadia zaki iya fushi dani haka har kiƙi zuwa bikina duk irin amintar dake tsakaninmu da burin da mukaci akan auran ko waccenmu._
Ƴar ƙwallar data taru a idonta ta maida.
_mun taso tin muna yara tare muke komi dake,mun ɗauki juna kaman ciki guda muka fito,bana da ƴar'uwa ke na maida sakuwata why zaki fishi dani sister akan wasu da baki sansu ba bare asalinsu._
Jin shashsheƙar kuka yasa Inna farkawa daga baccin data ke.
"ke lafiyarki mai ya faru?"
"ba komi Inna" ta faɗi tana goge hawayenta.
"amma kika zauna kina kuka kamar wadda akacewa uwarta ta mutu"
"dama tina maki zanyi ki ƙara kiran Anty Rashida ni na kirata bata ɗaga ba har yanzu"
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.