🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*_BANI DA BAKI BANI DA WATA KALMA DA ZANYI GODIA GAREKU SAI DAI NA BIKU DA ADU'A MASOYANA MASOYA WANNAN LITTAFI,HAƘIƘA KUNA NUNAN ZALLAR SOYAYYA DA IRIN ADU'OINKU DA YABAWARKU GARENI, INA GANI INA KUMA JIN DAƊI BA KAƊAN BA, BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI ADU'AR FATAN ALKHAIRI GA RAYUWARKU,ALLAH UBANGIJI(S.W.A) YA BIYA MANA BUƘATUNMU NA ALKHAIRI YA KIYAYE MU DAGA DUKKANIN SHARRIN ABINƘI DAN ALFARMAR SAYYIDIL WUJUDI ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)_*....
'''INA KIKE ƘANWAR KIRKI KUMA ƘAWAR ALKHAIRI UMMU HANASH THIS PAGE IS YOURS DOMIN FARINCIKIN KI,TANKS SO MUCH DA SOYAYYRKI GARENI ALLAH BARMU TARE...'''
*48*
Su Inna gida yay daɗi rayuwa ta sauya masu.
Ɓarin Baba daban sai Inna da Hidaya wuri ɗaya amma ɗakunansu daban.
Babu abinda Ammar bai aje masu ba na jin daɗin rayuwa a gidan,In babu nepa suna da solar in babu solar ga Gen ɗinsu nan kuma da gas suke anfani.
Kayansu Sadia kap ta ɗinka masu suka bada wancan tsummokaran.
Zaune yau suke a parlo suna kallon Saudia suna hirara suna roƙon Allah ya kaisu wannan gari mai albarka.
Da bayan la'asar inpcter Farooq ya dira a ƙofar gidansu Hidaya.
Da zuwansa ya ƙwanƙwasa gate Hidaya dake daga tsakargida tana wanke kayan Mukhtar cikin washing machine taso tana waye.
Jin muryar namiji ta dawo daga ciki tare da faɗiwa Baffa.
Tashi Baffa yay ya fita ,ba kaɗan ɗin tsorata yay ba ganin police a gidansa.
Lura da yanayin tsoro tare da Baffa inspctr Faruq ya ɗan murmusa tare da miƙama Baffa hannu suka gaisa.
"to yallaɓai kana tambaya ne ?"
"a'a ba tambaya neka ba nan ɗin dai nazo"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ,to lafiya yace ko dan ganinku ba alkhairi bane"
"ehhh to lafiya ba lafiya ba,muna son ganawa da ɗiyarka ne"
Hankalin Baffa tashe yaja da baya yana girgiza masa kai,
"a'a yallaɓai kunyi ɓatan kai ba dai nan gidan kuka zo ba dan ƴata bazata aikata abinda zai kai ga hukuma ta kamata ba wlh bata taɓa sata ba"
"Na sani Baba, karka damu ba wata matsala bace babba yanzu dai kai mana magana da ita"
"ka tabbata ?"
"na tabbata maka Baba, ahanzarta dan muna kan bakin aiki ne"
daga ciki Baffa ya koma ya shiga ƙwalama Hidaya kira.
Da hanzari ta taso daga parlo ta fito tana amsawa.
"Baffa gani"... Turus tayi ganin sauyawr fuskarsa ba kaman yanda ya fita ba.
"Baffa lafiya dai ko ,su wane suka zo"
"shiga ki sako hijab ɗinki kizo"
"Baffan Yusuf lafiya dai ko"

YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.