🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Strory~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*DIS IS 4U GUYZ*
Sadeeyer aliyu
A.B.U🌹
Saratu sifawa
Hajara kabir
Ummie💋
Ummu ihsan
Adam madina
Ummu Imran
Marie ousmaneTanx fr ur support..
*10*
Lokaci na tafiya rayuwa na daɗa gaba.
Inna da iyalanta kullum cikin sake son juna suke da nunawa kowannensu ƙauna.
Ɓangaren Hidaya kowacce daƙiƙa ta lokaci Son Ammar ƙaruwa yake a zuciyarta wanda ta kasa gane me hakan ke nufi.
Damuwarta rashin ganinsa,tashin hankalinta ɓacin ransa.
A babu yanda ta iya haka take ɗan sakewa dashi sbd mungun kunyarsa data keji shi kuma baya son haka..Ganin alamarin na neman talwatsa zuciyarta ƙaguwa tai a koma makaranta dan Sadia ta fayyace mata halin data tsinci kanta ciki.
Ranar Monday da aka koma makaranta Sadia bataje ba,hakan yasa Hidaya satar hanya ta fece gidansu kamin a tashi.
Da shigarta ta watsa mata harara ,itako Sadia dariya tayi tana cewa Umum ta Hamma yau kece agidanmu.
A ƙagauce Hidaya ta figi Sadia suka shiga ɗaki.
Zama sukai ko ruwan data kawo mata ma bata sha ba.
Cikin raunin zuciya da sarƙewar murya Hidaya tace da ita,
"Dan Allah ƙawa ya ake gane So? kuma taya yake kama mutum?sannan taya zaka faɗawa wanda ka faɗa akansa?""Hmm mai yasa kikai min wannan tambayar to,keda ba ƴar soyayya ba"
"dan Allah ki faɗan ni dai"
Nan ta kwashe duk irin abinda takeji game da Hamma ta sanarwa da Sadia.Dariya tayi sose harda dukan cinya tace,"So da Ƙauna sun kama wata beb sai dai kuma tai rashin sa'a ta kamu da wanda bazata sameshi ba"
a gigice Hidaya ta ɗago tana kallonta ,cikin shashsheƙar kuka tace"maiyasa?dan Allah bazan samu soyayyar Hamma ba?da gaske kike?akan mene to?"
"ehh mana ,kinsan da cewan babu aure tsakaninku to akan me zaki bari har hakan ta faru dake salon ki wahalar da kanki"
"ke nafaɗa maki fa ba uwa uba guda muke dasu ba hasalima maƙotaka ce kawai ta haɗamu"
Zaro ido Sadia tayi tana kallonta,"wannan kuma ƙaryane yarinya,wlh kun haɗa alaƙa dasu ta musamman imma daga ɓangaren Inna ko Babanku"
Zama Hidaya ta gyara ta ƙara fuskantarta,to tsaya kiji tsakaninmu dasu.
*TUSHEN LABARIN*
_Malm Adam Modibbo zaune yake da Matarsa Halima a ƙauyensu na Gurore dake adamawa,fulani ne ruƙaƙƙu gaba da baya._
_Shi ɗayane wurin mahaifiyarsa tin yana saurayi iyayensa suka rasu,yana da ƴan uwa amma bazaka taɓa cewa yana dasu ba saboda tin mahaifinsu na da rai basa jituwa,ƴan uba kenan._
_Bayan da suka amshi rabon gadonsu kowa ya kama gabansa,ba wanda yake neman wani dan zumunci._
_Da abinda ya samu yaja jari har ya auri Halima marainiyar Allah wanda take wurin wan mahaifinta cikin zaman tsangwama._

DU LIEST GERADE
HIDAYAH NOOR completed.
Historische RomaneHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.