PAGE 7

1.6K 122 8
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
             *HIDAYAH NOOR*
                         🌀🌀🌀🌀🌀

             *Story~Written~Edited*
                  *_Mss Xerks_*🌺



           *Devoted to Ummi Aisha*

*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*_KAI2 WONIWONI ABANI KALA ABANI KALA💃🏽💃🏽,GASKIYA FANS KUNA WANI BALA'IN BURGENI ƊINN INA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU SOSE YANDA BAKWA ZATO,INA GODIA SOSE DA YANDA KUKE BANI KULAWA DASO WALLAH_*😍😘

~NA SADAUKAR DA PAGE ƊINNAN GAREKU XÚMÛNT@ NÔVÊLL@  My heartbeats sai wanda kuka ga daman bawa nakune kaɗai~👌🏼😘😘❤


*7*

Bayan tashinsu a makaranta suna tafe suna hira.

Sadia babu abinda take sai faman koɗa Uncle Deen.

Ita dai Hidaya nata Hmm da Umm ne har suka tari mota suka hau.

Nanma a mota cika ta tai da zancen soyayya,gajiya da jin zancen nata da tayi ta ɗora mata schol bag ɗinta ajikinta.

Ihu Sadia tayi ta ture jakar,"maine hakan ai saiki ɓallan ƙafa,wannan jakar taki gari guda kaman buhun shinkafa"

"haba kece kin isheni da zance mara kan gado"

"tsakani da Allah mutuminn baya burgeki ,ga wanka ga iya tafiya gashi in yana maki kalamann ni har kishi ma nake Yasin,yafa iya soyayya komai nasa abin burgewa wayyo"
Sadia ta rungume hannayenta a ƙirji tana Allah kabani kaman Uncle deen tinda Oo bata sonsa.

Kallonta Hidaya tayi abinma abin takaici,
"toke yake birgewa amma ni ko kaɗan,ke nifa ko bari kiji ma kaf mazan duniya wlh Hamma na kaɗai ke burgeni a komai"

"yo wannan ai dan kinsan yayanki ne,wannan ni a fagen soyayya nake maki magana hajiyata"
"to banzo wannan babinba tukunna sai dai ko nan gaba,banza kema kina son shiga sahun mayaudara irinsu kadija ina Yaya Saifullahi da kika mato akansa"

"Dalla ke kuma yaya Saifu ai na dabanne shine alawar zuciyata"
Da dariya Hidaya tace "ko kuma cingom ba"

Da hirarsu ta samarinsu suka ƙaraso har aka sauke su.
Tinawa Hidaya tayi da karta manta da wajibul manzil ɗin da Mudarrisa Aliyu ya basu.

To tace mata ta faɗa gida dan agajiye take.

Inna ta samu zaune da ƴar radio data saba ji,sannu da gida ta mata ta shiga ɗaki ta cire kayanta.

Wanka tai ta dawo kan cinyar Inna ta kwanta kamin ta huta ta tafi Islamia.

Cema Inna tai idan uku tayi ta tasheta dan zataje wurin Hamma amso aikinta.

Uku saura ko nayi Inna ta tasheta dan tasan shirin Hidaya da wuya.

Sai asannan ma taci abinci tukunna ta saka uniform na islamia ta wuce.

Gidan Adda ta wuce,tana bacci ta sameta .tashinta tayi tana tambayarta ko Hamma ya bar mata saƙo.

"Aa bai bani komai ba ,saƙon maine"?

Ɗan dukan ƙafa tayi aƙasa da shagwaɓa tace,
"Wajibul manzil ɗinfa islamia ne tin shekaran jiya na bashi danma kar ya manta,kuma yau malamin duka zaiyi yace"

Murmushi Adda tayi tana kallonta,Hidaya ƴar shagwaɓa ce ga saurin kuka.

"Aa ni bance ki kuka ba, shiga yana ɗakinsa ki sameshi."

HIDAYAH NOOR completed.Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt