🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*16*
Kicikicin ƙwacewa take amma ta kasa saboda damƙar daya mata.
"Hamma dan Allah kasakeni,Adda fa na iya shigowa ko Inna ta fito"
Mayun idonsa yakafeta dasu yanda take faman kumburi tana turo baki sai ya birgesa.
Takawa yay dan matsawa kusa da ita ta ƙara ja da baya,fincikota yay ta faɗo jikinsa.
Diriricewa tai tana Hamma ka bari mana mene hakan kar Inna ta fito bana so.
Jin numfashinta ya sauka ajikinsa ya sauke ajiyar zuciya tare da jin wani irin kasala saboda yanda ta mannu ajikinsa.
Da ƴar ƙwallarta ta fara roƙonsa dan ita tsoro ma ya fara bata kaman wani wanda ya bugu haka ya koma.
"Dan Allah Hamma ka matsa ban so nikam,Adda fa zata iya shigowa ko Inna ta fito ina faɗa ma"
"Kina so na ƙyaleki"?
Ɗaga masa kai tayi alamu na ehh.
"To ɗago ki kalleni kuma cikin idona"
Kasawa tai bata kuma jin zata iya.
hannunsa yasa ya zagaye weast ɗinta dashi.Da ƴar ƙaramar tsiwarta tace,"Hamma fa ba kyau banso ni nace maka"
Ɗil taji abu ya sauka a bayanta,ɗagowa tai tagansa yana hawaye.
Bin idanunsa tai da kallo nan take zuciyarta ta tsinke._wanna irin SO Hamma ke mani haka,shin tin yaushe ya fara sona har yay wann zurfin ._
Hannu tasa zata share masa hawayen ya riƙe ta.
"Ina sonki har abada, har acikin raina da zuciyata Hidaya ke kaɗai kike yawo,ke babbar kyauta ce a rayuwata da Allah ya bani,kece hasken rayuwata,kinjima a cikin zuciyata wanda hakan yasa bazan iyya fiddaki cikinta ba.ki tallafi ruhin Ammar kisoshi Hidaya"
Shiru yay ya kuma fuzgar da iskar bakinsa,murmushi yayi mai sauti tare da sa hannu ya ɗago da fuskarta.
"Ramuwar ta isa Haka kinji.nasan kema hakanne a ƙasan zuciyarki,na tsawon shekara 1½ kin kama kin jingine arayuwarki kinyi shiru da bakinki gashi kuma kin sameni saiki watsi dani bakya gudun ki rasani"
"to meyasa kake sona?"
Da sanyayyen murmushinsa ya juyo da ita baya yasa kansa daga wuyanta ya fara magana ahankali kaman mai raɗa.
"I love you Because i cant stop tinkng about you,kinjima kina zuwa mani a mafarki ,Ki amince mani na ƙara tabbatar dake acikin zuciyata zan adanaki na kuma killaceki inda babu abinda zaki samu zakuma kisha sai tsantsar so da ƙauna daga Ammar"
A kunyace da irin yanayin daya riƙeta yake kuma magana tasa hannu ta turasa baya ,ido cikin ido ta ɗago tana kallonsa ɗauke da murmushin so da ƙauna.
Shima murmushin ya sauke mata mai fitar da sauti,idanunsa da suka ƙanƙance saboda jinyar so su ya ƙara warewa yana kallon bakinta dake motsi dan sonyin magana.

YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.